← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 75

Sashe 4

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take a nan jikin Haseena ya saki, nan da nan ta kama kanta sabida wani irin jiri da yake ƙoƙarin ka da ita, sai kawai ta zube a jikin Nanan a sume babu numfashi a tare da ita

Ita kuma sai ta ɗauke ta zuwa cikin gidan ta shige da ita tana rufe ƙofan.
***

          
_____Sai bayan la'asar sannan SHAREEF ya iya tashi; sabida ganin zai iya mutuwa idan har bai nemi abu ya saka a cikin sa ba, jikinsa har rawa yake yi saboda rashin karfin jiki ga tsananin zazzaɓi da ke jikinsa, to ya ɗaura wa kansa jarabar tunani da damuwa zuciyarsa kamar zata fashe don bala'i da ƙunci,
Abinci yayi oda ya zauna ya ci duk da daƙyar yake iya tusa wa a cikin sa, ko rabi bai yi ba haka ya miƙe ya shiga yayi wanka ya canza kayansa; sannan ya ɗauki Jakarsa ya nufi airport,
Koda ya je babu jirgin Nigeria a lokacin, sai ƙarfe goma na dare sannan za a samu,
Dalilin da yasa ya dawo hotel ɗin kenan, ya ci gaba da kwanciya har time yayi, sallah kaɗai ke ɗaga sa, ya so ya koma wurin Haseena ya tuhume ta don zuciyarsa ta kasa natsuwa, amma kuma ya fasa sabida a lokacin wani irin haushin ta yake ji, sam ba ya son sake tozali da ita, a rayuwa shi mutum ne wanda ba ya son a ci amanarsa, musamman a kan abun da yake so, kishin da yake dashi zai iya aikata komai a kanta, yana tsananin ƙaunar Haseena wanda baki ma bazai iya misalta wa ba, shine dalilin da yasa yake tsananin kishin ta kuma zai iya yin komai ko mene ne kuwa,
Amma sai ga shi yau ita ya kama da cin amanarsa, already ta fifita wani a kansa, idan har ta san haka ne meyasa tun farko ta aure shi? Dama ta san ba shi kaɗai zata iya zama dashi ba amma ta ɓata mishi lokaci har haka?
Fushin da yayi da ita ba na wasa bane, duk da ba ya jin zai iya rabuwa da ita amma dole ya ɗanɗana mata kuskuren ta, idan ya je ya huce da ƙafafunta sai ta zo ta ba shi hakuri sannan zai ɗauki mataki a kanta

Yana ganin ƙarfe tara tayi ya nufi airport ya zauna a can, har sai da aka kira su sannan ya shige jirgin

Basu isa Nigeria ba sai a washe gari da tsakar rana, Keke napep ya hau ya isa dashi gida,
Time É—in da ya shiga Falo Momy ne kaÉ—ai zaune

Tayi mamakin ganin sa a haka duk da yau Lahadi zai dawo, amma a yanda ta ganshi tamkar an jeho shi babu natsuwa a tare da shi, abun ya É—aure mata kai, shiyasa bayan ta amsa gaisuwar sa take cewa, "lafiyar ka dai SHAREEF? Wani abin ya faru ne?"

Girgiza mata kai yayi yana ƙoƙarin ɓoye halin da yake ciki, sai yace, "No Momy babu komai."

Shiru ta ɗan yi, duk da bata yarda ba kasancewar ta san waye SHAREEF, kamar ta tambaye shi Haseenan; sai kuma ta fasa tana taɓe baki tare da cewa, "ok, ka shiga in ka kimtsa ga fruit salad nan sai ka sha; before in gama abinci."

Bai ce komai ba ya juya ya wuce steps zuwa dakin su, yana shiga bedroom ya tarar da Hanif yana shirga barci, yayi ɗai-ɗai abun sa daga shi sai gajeren wando a jikinsa, babu riga ya ƙure AC yana shan iska,
Jakarsa ya ajiye yana zama a gefen gadon, tare da tallabo kansa da ke barazanar tarwatse wa sabida mugun tunanin da ya addabe sa, har wani biji-biji yake gani a idanunsa, kasa jurewa yayi shiyasa ya kwanta a saman gadon yana sauke numfashi mai ƙarfin gaske

Sama-sama Hanif yake jin motsi a kusa dashi, har hucin numfashi yake ji shiyasa ya farka a nan take. Mamakin ganin SHAREEF yayi kwance yana sauke numfarfashi kamar wanda bai da lafiya, hakan ya tsorata shi shiyasa yayi saurin tashi yana kai hannunsa jikinsa tare da cewa, "Bro lafiya dai? Yaushe ka dawo?"

BuÉ—e idanu yayi ya sauke masa su a cikin nasa, sun yi ja idanun ko da gani ka san yana cikin tsananin damuwa

Shi kansa Hanif ya san ba lafiya ba a yanda ya gansa a hargitsen nan, ga jikinsa da zafi da ya taɓa har kerma ya ga yana yi, that's why ya ɗan ruɗe da tambayarsa cikin damuwa da son sanin me ke faruwa dashi

But SHAREEF ya kasa magana illa miƙe wa zaune da yayi yana ci gaba da sauke numfashi, tare da ƙoƙarin daure wa ciwon da ke sukan shi

"Please Bro ka sanar min me ke damunka? Ka É—aga min hankali; tell me what's wrong with you?"

"Nothing, kawai kaina ke min ciwo."
Yayi maganar a hankali cikin sanyin muryansa, yayinda ya kama kan ya kasa saki

Shi kuma Hanif cike da damuwa yace, "I'm sorry, ina zuwa bari in dauko maka magani ka sha."
Ya sauka a kan gadon yana koma wa wurin dressing mirror, since a nan suka fi yawan ajiye magani, ɗauko masa na ciwon kan yayi tare da fita zuwa Falo ya buɗe fridge ɗin, roban ruwa guda ɗaya ya gani a ciki, shi ya ajiye ma ɗazu, shiyasa ya dauka ya kawo masa yana miƙa masa yace, "ya sha."

Babu musu SHAREEF ya amsa ya shanye since yana jin jiki sosai, buƙatar sa kawai ya samu relief

Zama Hanif yayi a gefen sa yana kallonsa, sai ya É—an ja numfashi cike da tausayin sa yace, "tell me what's wrong with you? I know akwai abun da ke damunka ba ciwo kaÉ—ai bane, kana cikin damuwa Bro alamun ka ya nuna min."

Shiru SHAREEF yayi ya kasa yin magana, duk da ya san cewa ba ya iya ɓoyewa Hanif komai, amma yau yana jin kamar bazai iya sanar mishi wannan sirrin ba, tabbas babban sirrin sa ne; taya ya zai iya sanar mishi?
Tunanin da ke ransa kenan

Amma sai Hanif ya dage yana lallaɓa shi domin ya damu da son sanin abun da ke damun ɗan uwan nasa, hankalinsa ya soma tashi a kansa

Hakan ne yasa daƙyar ya iya buɗe baki ya sanar mishi da komai, idanun nan sun sake kaɗa wa sun yi jazur, sai ga ruwan hawaye suna fita, yana kallon Hanif ɗin yake cewa, "ban taɓa tunanin wannan abun zai kasance ba, Haseena fa, wacce nake ƙauna na bata yarda ta gaba ɗaya, amma yau ita ce ta ci amanata, ta wulaƙanta Ni, na kusance ta amma na ji ta a buɗe ba a yanda Mace zata kasance ba, wani ta bama kanta yayi amfani da ita bayan gani tsawon lokaci abun da nake jira ban samu ba."
Sai ya ja numfashi yana kai hannunsa tare da share hawayen da ke gudun tsere a kan face É—in sa

Tausayi da tsananin mamaki gami da tunanin girman son da É—an uwansa yake yi wa Haseena; shine a zuciyar Hanif, tabbas yana jinjina wanne irin soyayya ne SHAREEF yake yi wa yarinyar nan da har yau yake zubar da hawaye a kanta? Shi kansa ya É—an rikice da jin zancen; amma kuma sai ya dafa SHAREEF É—in cike da sanyin murya yace, "Bro, Ni ban gane wanne irin buÉ—e wa kake magana ba? A yanda na san Haseena tana kaunarka, in har bata baka kanta ba bana tunanin zata iya bama wani kanta, a tunanina kun daÉ—e da sanin juna ba wannan karon bane, ashe kallon da nake muku ba haka bane?"

Wani kallo SHAREEF ya watsa mishi, sai dai bai ce komai ba ya É—auke idanunsa tare da sanya hannu ya buga tagumi

"To amma kai taya ya ka san cewa a buÉ—e take bayan baka san wata Mace ba? Ka san buÉ—e wa kuwa?"

"Kana son ka raina min hankali ne? Ina maganar serious issues but kana son ka mayar dani tamkar ban san me nake yi ba? Zuruf abuna ya shige duk girmana, taya ya kake tunanin bazan yi wannan zargin ba?"

Wani irin dariya ne ya so kufce wa Hanif sabida abun da yace; amma kuma tuni ya riƙe dariyan a cikin sa gudun samun matsala; sabida yanda SHAREEF ɗin yake a fusace ya san tsab zai iya ƙara harzuƙa shi yakai mishi bugu, duk da haka sai da ya murmusa yana kawar da kansa gudun ya gansa

But bai san SHAREEF tuni ya gane sa ba, shiyasa ya buge hannunsa da ya É—aura masa a kafaÉ—a yana cewa, "kana min dariya since ka mayar da Ni mahaukaci?"

"No ba haka bane Bro, abu ne dai da ayar tambaya a ciki..."
Kasa ƙarisa maganar yayi ganin kallon da SHAREEF yake masa a yanzu

Dogon tsaki ya ja yana mike wa tare da faÉ—in, "ba na son ma maganar a barta, ka ci gaba da dariyan kai kaÉ—ai tunda ka mayar da Ni sakarai."
Toilet ya nufa ya shige yana bugo ƙofan

Yayinda Hanif ya fashe da dariya yana toshe bakin sa, "Oh! Bro matsala, yau dai abun bai yi dadi ba, yarinyar da ka ƙwallafa rai a kanta an samu akasi ta ci amanarka, dama koda ganin wannan yarinyar tana fiƙi-fiƙi da ido za a rina ai".

_Fan's fatan an yi zaɓe lafiya? Allah ya zaɓa mana shuwagabanni na alkhairi waɗanda zasu sadaukar da lokacin su domin kawo ci gabanmu Amin._

19 March 2023.
[31/03, 4:32 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE3*
_____Biji-biji ta soma gani har sanda ta wartsake ta soma ganin ɗakin, a hankali ta mayar da idanun nata tana lumshe su tare da sake buɗe su, nan take ta sauke su a kan face ɗin Nana da ke zaune saman sofa ta harɗe ƙafafu tana kallonta

Murmushi tayi mata tana tasowa ta zo inda take, tare da kai hannu tana shafa mata face da faÉ—in, "babe, kin tashi?"
Chapter 4 · 0% Book details