← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 75

Sashe 38

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yanda yabar Maryamu, a haka ta ƙudundune kanta ta dinga sharɓan kuka gunun tausayi, ga raɗaɗin marukan da ya sauke mata har yanzu tana jin ƙaran marin a cikin kunnenta, kuka sosai ta dinga yi ta kasa sararawa kanta sabida tsananin baƙin cikin abun da SHAREEF yayi mata, lokaci ɗaya ta soma jin tsanarsa na huda mata can cikin zuciya baƙin ciki da ƙunci suka tokare mata maƙogwaro,
A haka ta kwana cikin wannan halin ko motsa wa ta kasa yi illa hawaye da take zubar wa cuz sautin muryanta ma ya dena fita, ba ƙaramin jigata tayi ba sabida wani irin ciwon kai da ya cafke ta,
Har aka yi kiran sallan asuba a kunnenta aka yi tana ƙudundune da kanta a saman cinyanta ta cure wuri ɗaya ta kasa motsa wa,
Dalilin da yasa koda ta miƙe zata shiga toilet jikinta yayi tsami wuyanta ya riƙe ƙam daƙyar take iya sarrafa kanta, idanun nan sun kaɗa sun yi jazur haka ma fuskarta tayi suntum, a haka ta lallaɓa tayi sallan a zaune sannan ta kwanta a wurin tana mayar da nimfashi, sai tsiyayar da hawaye take yi waɗanda sun kasa tsaya wa daga cikin idanuwanta, a duk shuɗewar seconni tana jin ƙiyayyar SHAREEF na ƙara huda mata zuciya, haƙiƙa tayi nadamar sanin sa, a yanzu dai baza ta taɓa iya auren mugu azzalumi mara imani irin sa ba, wlh sai dai ta mutu da ta zauna dashi koda soyayyarsa zai kashe ta ne, bare ma a yanzu jin ƙiyayyarsa take yi,
A nan ta kwanta ta kasa motsi har garin Allah ya waye lokaci ya soma ƙurewa amma ta ƙi tashi,
Sai da kusan ƙarfe tara tayi sannan ta miƙe zaune daƙyar, ba ta son Momy ta zo ta tarar da ita a haka shiyasa ta lallaɓa ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta zauna a bakin dressing mirror tana kallon fuskarta, daga ita sai towel da ta ɗaura daga saman ƙirjinta har zuwa cinyoyinta, ido ta tsira wa madubin tana jin wasu zafafan hawaye suna ƙoƙarin fitowa, sabida ganin yadda face ɗin ta tayi mugun kumbura sakamakon marin da ta sha; da kuma kwana da tayi tana kuka ga rashin barci, babu shatin yatsu amma duk kumatun ta sun suntume, manyan idanuwanta sun yo waje sun kumbura ciki sun yi jazur alamun ta sha kuka sosai, har saman laɓɓanta sai da suka tasa,
Wani irin kuka ta fashe dashi tana kai hannunta ɗaya zuwa saman bakin ta, cikin shashsheƙan kuka take faɗin, "Allah ya isa ban yafe ba, Insha Allahu Allah sai ya rama min abun da kayi min, bazan taɓa yafe maka ba."
ÆŠakyar ta iya tsayar da kukan ta tashi ta je ta sanya riga da wando na fakistan, sannan ta yafa mayafi a saman kanta ta fita Falo

Babu kowa sai Momy wacce itama tana shirin kiran Maryamun ne da ta ji ta shiru, amma ganin ta a wannan yanayin fuska ta kumbura, hankalinta a tashe take dubanta da tambayar ta, "me ya same ta?"

Ɗakyar Maryamu ta mayar da ƙwallan da ke shirin zubo mata, tace, "Momy babu komai."

"Ya za a yi ki ce min babu komai; bayan ji be yadda kika fito fuska a kumbure alamun kin sha kuka? Sanar min mai ke damun ki?"

"Momy ciwon kai ne jiya ya dame Ni shine na kasa barci."

"Subhanallah.. amma ai yakamata ki zo ki tashe Ni in ba ki magani Maryam, ba wai ki zauna kina kuka ki bar ciwo a jikinki ba, ko da asuba maimakon ki taso ki zo in ba ki maganin, kar ki ƙara haka kinji ko? Bari in kawo miki maganin, ki je ki zauna ki karya ina zuwa."
Tayi maganar tana tashi ta nufi upstairs da sauri domin É—auko mata maganin

Yayinda Maryamu kuma ta ƙarisa wurin dinning ɗin ta zauna, sai da tayi shiru na tsawon lokaci before ta soma haɗa tea a hankali cikin sanyin jiki da rashin karsashi, har ta gama before Momy ta kawo mata maganin,
Hakan ne yasa ta afa a baki ta sha da tea É—in

Momy kuma ta ƙarisa zuba mata arish da ƙwai a flat, ta ɗaura mata bread a sama before ta tura mata gabanta, tana ce mata, "tayi maza-maza ta ci."
Falo ta koma ta zauna tana duba wayanta tana son tayi kira

A time ɗin SHAREEF shima ya fito, domin shi kansa bai samu yayi ishashshen barci ba sakamakon abun da Hanif ya faɗa masa a jiya, sosai maganar ta tsaya mishi a rai cike da tsananin mamakin wai Maryamu ne ta ba shi ƙodan ta, tsananin takaici da dana-sanin abun da yayi mata ne ya kasa runtsa wa sai gab da asuba barci ɓarawo ya kwashe sa,
Har garin Allah yayi bai tashi ba

Yayinda Hanif yayi shirin zuwa aikin sa ya tsallake sa ya wuce batare da ya tashe shi ba, ya wuce wurin aiki shi kaÉ—ai

Sai yanzu SHAREEF ya farka ya ga ya makara, wanka yayi ya ɗaura alwala yayi Sallah ya shirya sannan ya fito riƙe da Jakarsa,
Tun dosowan sa Falon ya hangi Maryamu zaune a saman dinning, kanta a ƙasa tana kallon cikin cup ɗin da ke gabanta ta kasa shanye wa sabida halin da take ciki na rashin daɗin jiki; da kuma ƙuncin zuciya,
A hankali ya taka ya iso cikin Falon yana ma Momy Barka da safiya

Ta dube sa tace, "sai yanzu? Ai nayi tunanin baza ka je aikin bane ga shi har ƙarfe tara da rabi, Hanif ya daɗe da tafiya."

Shiru yayi bai ce komai ba kuma bai zauna ba

Itama sai ta mayar da hankalin ta a kan wayanta tana cewa, "ka je ka karya."

Juya wa yayi bai ce uffan ba ya nufi wurin dinning ɗin, har ya ƙarisa idanunsa a kan Maryamu da ta ƙi ɗagowa kanta a ƙasa ba ya ganin fuskarta, tsaya wa yayi a wurin ya zuba mata ido yana jin zuciyarsa babu dad'i, musamman lokacin da ta ɗago kanta tana shirin mike wa tabar wurin, hakan ne yasa ya ga fuskarta wacce take a kumbure babu ɓurɓushin fara'a, tana barin wurin sai ya lumshe idanunsa, a karon farko a rayuwarsa, a karon farko ya ji tausayinta da kuma tsananin nadamar abubuwan da yayi mata, idan har zata iya sadaukar da lafiyarta domin ceton shi, meyasa zai ci gaba da tsanarta? Shin mai tayi masa? Meyasa ya kasa fahimtar zuciyarta? Wacce iriyar soyayya take mishi har da zata iya bada ƙodan ta gare shi duk da ƙiyayyar da yake mata? Ya shiga ruɗani da rikicewar zuciya,
Zama yayi sai dai ya kasa cin komai a wurin yana jiyo maganganun Momy da take yi wa Maryamun

Tana tambayarta jikin nata, a cewar ta, "in har bata ji sauƙi ba zata saka SHAREEF yakai ta asibiti yanzu a duba ta."

Amma sai Maryamun tace, "a'a da sauƙi jikinta, maganin yana mata aiki ta soma jin sauƙin kan."

Ya kasa cin komai haka ya tashi jiki a sanyaye ya nufo wurin su yana cewa, "Momy zan wuce."

"Ok to Allah ya tsare ya bada Sa'a."

"Amin Momy na gode." Yayi maganar idanunsa a kan Maryamu da har yanzu ta kasa É—ago kai bare ta kallesa,
Har yabar wurin bai samu sun haÉ—a idanu ba

Yana fita sai Maryamu ta kalli Momy tace mata, "tana son koma wa Abuja a yau, ta gaji da zama nan."

Da mamaki Momy take kallonta, tace, "kamar ya kin gaji da zama a nan Maryam? Ko wani abun ake miki baza ki zauna ki ƙarisa hutun ki ba?"

"A'a Momy Ni dai kawai a mayar dani can, ko kuma in koma Zaria in ƙarisa hutun, ba na son zaman nan."

Shiru Momy tayi tana duban ta, domin tabbas ta fahimci akwai tsantsan damuwa a tattare da ita a yanda take maganar dole akwai wani abun a ranta, dalilin da yasa tace, "ko dai SHAREEF yayi miki wani abun ne kike son tayar da hankalin ki Maryam?"

Kamar zata yi kuka tace, "a'a Momy..."
Sai tayi shiru ta kasa ci gaba da maganar

Itama kuma Momy tayi shiru tana ta kallonta,
Hakan ne yasa Maryamu ta duƙar da kanta saboda ganin yanda ta ƙura mata idanu,
"Shikenan, bari zan sanar da Dadyn ku in ya amince sai driver yakai ki ko zuwa anjima ne, bari Sadiq ya shigo gidan shima ya je wurin Abokansa ne sai ku je ku sake wasu siyayyan ki yi musu tsaraba."

Jin haka har zuciyar Maryamu tayi dama-dama ta soma jin sanyi, domin a yanzu ba ta buƙatar ci gaba da zamanta a gidan nan, koda wasa ba ta son sake tozali da fuskar SHAREEF kuma a wannan lokacin, farin cikin ta kawai ta samu tabar gidan nan batare da sun sake haɗuwa ba, domin a yanda take ji komai zai iya faruwa da ita, ranta a ƙuntace take burin ta kawai tabar gidan.***

Ai kuwa zuwa ƙarfe ɗaya Maryamu ta haɗa kan kayanta kaf, tunda Dady ya amince sabida yanda suka ga ta matsa tana son tafiya, shima tunda ya tambaye ta ta nuna tana son tafiyar ne kawai, hakan ne yasa ya yarda, suka fita da Sadiq suka sake yin siyayya sannan suka dawo gida, bayan ta gama haɗa kayan ta tayi sallan azahar sannan suka durfafi hanya da driver, sai Abuja.

Koda su Hanif suka dawo sai dai suka ji labarin tafiyar ta a bakin Momy.
[17/04, 3:56 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE20*
_____Maryamu ta tafi da kwana huÉ—u; shima Sadiq ya wuce England; tare da Hanif suka tafi,
Dayake shi zai je yayi masa wasu abubuwan na harkan karatun, bai dawo ba sai da ya tabbatar da ya kammala masa komai before ya dawo

A lokacin Dady yake sanar masa, "ya gama binciken neman auren sa, a koyaushe za a iya tura wa, don haka yanzu babu wata matsala sun gama yarje mishi aurenta."
Chapter 38 · 0% Book details