Sashe 52
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gajiya yayi yabar wurin ransa duk a jagule, haka nan ya koma ɗaki amma ya kasa haƙura, ya hau duba keys ko zai samu a dakin nasa, amma babu komai sai na dakin da ke bakin kofa, haushi kamar ya kashe sa, sosai ya ƙwallafa rai a kanta, a ganinsa maganar da suka yi ɗazu zata sassauta mishi ne, yana bukatar ta matuƙa, yana bukatar kasancewar su tare,
Gajiya yayi da binciken ya kwanta da ɓacin ran, don ko wanka ya kasa yi bare ya je ya ci abinci duk da yunwar da yake ji,
Yana kwance abun duniya ya ishe shi, da ya rufe ido Maryamu yake gani ya kasa barci sai juye-juye yake yi,
Ganin yunwa ta addabe shi a yanzu, haka nan ya lallaɓa ya je saman dainng ya zauna, abincin ya buɗe, wanda har lokacin yana tururi tunda a coolern da ta sanya yana riƙe zafi, frd rice ne a ciki, sai yankakken hanta a ciki,
Spoon kawai ya ɗauka ya saka a ciki ya hau ci, daɗin abincin yasa ya ɗan ci da yawa sannan ya rufe ya nufi fridge ya sha ruwa, after ya gama ya koma ɗaki ya sake kwanciya, haka ya dinga juye-juye yana tunanin ko dai ya sake zuwa ya bata haƙuri ne? Duk da bai da tabbacin zata bude mishi ƙofan, tabbas bazai iya zama da ita na tsawon lokaci a haka ba, dole ne yayi wani abun amma bazai hakura da ita ba, wata zuciyar tana faɗa masa, "mai zai hana ya nemo maganin barci yayi mata amfani dashi?" Amma tuna abun da ya faru ranan nan da bata yi barci ba, sai duk ransa ya sake ɓaci,
Yana a wannan yanayin kuma sai ga kiran Haseena, abun ya ba shi mamaki domin rabon shi da ita ya manta, bazai iya tunanin tsawon lokacin da ta É—auka bata amsa call É—in sa ba har ya gaji da kira,
A yanzun ma ya ƙi ɗauka har tayi mishi two missed call, ƙarshe sai ya kashe wayan ma, don a yanzu ba kaɗan ba mugun haushin ta yake ji, ta cutar dashi a rayuwa, ta juya mishi baya a lokacin da yake bukatar ta, ko ya amsa wayan ma babu amfanin da zata yi mishi, har yanzu yana baƙin cikin yanda ta ƙi tausaya wa rayuwar shi, duk da irin ƙaunar da suke yi wa juna, a yanzu kuwa ya soma samun sauƙin raɗaɗin da yake ji a kanta, don haka ba ya bukatar kiran ta a dai-dai wannan lokacin,
Haka yayi barci cikin wani hali cike da mafarkin Maryamu,
Koda ya tashi da asuba sosai cikin sa yake ciwo, ƙarshe a ɗakin yayi Sallah, ya duba maganin sa babu saura,
Haka ya kwanta yana murkususu har garin Allah ya waye, daƙyar ya tashi yayi wanka ya sauya kayan sa ya fice a gidan zuwa asibiti
Wurin ƙarfe tara da rabi sai ga kiran Hanif ya shigo wayansa, lokacin ya fito daga wurin likita, jikin da ɗan sauƙi tunda har sai da ya kwanta ya samu relief a office din,
Sai da ya shiga mota sannan ya amsa kiran
Hanif ya fara sallama, ya amsa mishi,
Sai yace, "ko dai har yanzu kana barcin ne na tashe ka?"
"No, yanzu haka ma ina asibiti fitowana kenan."
"Asibiti kuma? Me ya faru ne?"
Ya tamabaya hankalin sa a É—an tashe, don yayi tunanin wani abu ne
But sai SHAREEF yace mishi, "na je wurin Doctor Abbas ne, magunguna ne suka ƙare na je ya duba Ni."
"Haba! Wai kana nan a haka har yanzu baka yi abun da ya dace ba? Me kake jira to?"
"Mai nake jira kake tambaya?"
"Eh, sabida nayi tunanin an wuce wurin nan Bro, musamman a halin da kake ciki."
Ɗan numfashi ya ja before yace, "Hanif ba yanda kake tunani bane, na kasa samun damar yin komai, ka san abubuwan da suka faru a baya a kan abun da nayi mata, so ta ƙi bani wannan damar."
Dariya ya sheƙe dashi, "wai to kai biye mata zaka yi? Haba sai ka ce ƙaramin ƴaro Bro da har zaka bari Maryam tayi maka wayon? Ai ina ga akwai hanyoyi da dama da zaka iya bi da ita, har yanzu Maryam yarinya ce, cikin sauƙi zaka iya sarrafa ta, musamman ma da ta kasance akwai soyayyarka a tare da ita, ba abu ne mai wuya Maryam ta tsane ka ba wlh, kome kayi mata zaka iya sauya ta a cikin ƙanƙanin lokaci, sabida tana sonka, baza ta taɓa ƙin ka ba, soyayyarka ita ce raunin ta, Bro be a man mana, kar ka zauna zaman jira kwaɗo yayi maka ƙafa."
Shiru SHAREEF yayi yana sauraron sa, sai kuma can yace, "yanzu dai kabar wannan maganar ka bani shawara, amma ba yanda kayi zato bane, haƙiƙa a yanzu na soma sanin wace ce ita, kuma har cikin zuciyata ina son kasancewa da ita, ina jin farin ciki da ganin ta cikin gidana, ina jin wani abu a game da ita sosai, sai dai ba kamar Haseena ba, don ba na tunanin soyayya ne."
"Hmm wai kana nufin har yanzu ba ka kaunar Maryam? Har yanzu Haseenan kenan ita ce a cikin ranka?"
"Ban ce maka ba, ina nufin soyayyar da nayi a baya, ba kalan ta nake yi wa Maryam ba, abun da nake ji a game da ita, ba irin wacce na saba ji bane a baya a cikin soyayyata."
Hanif yace, "sabida ita nata soyayyar daban ce, amma baza ka gane hakan ba sai lokacin da ka rasa ta a rayuwa, kana son Maryam Bro, a yanzu soyayyarta na tare da kai, shawara kawai ka bi duk yanda za ka bi domin ku daidaita kanku, babu amfanin ci gaba da zama a haka, ka faɗa mata gaskiyar kana sonta ku zauna ku fahimci juna, ita soyayya tana son fahimtar juna ne, idan masoya suna fuskantar matsala, yana da kyau su zauna su fahimci juna, idan suka tattauna zasu gano matsalar su, tattaunawa tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar masoya, duk abun da ke cikin zuciyarka ka faɗa mata, babu bukatar ɓoye wa, itama a wanann lokacin zata fahimce ka; kuma zata bayyana maka sirrin da ke ranta, duk abun da take ji a ranta zata zayyane maka, daga nan kuma sai kuyi maganin matsalar ku, don Allah Bro ka daure kayi hakan, kar ka tsaya tunanin babu wata soyayyarta a ranka, kawai ka furta mata ko meye."
Ajiyar zuciya SHAREEF ya sauke, cike da sanyin murya yace, "shikenan zan yi hakan, zan yi abun da ka ce min."
Sai ya É—an ja tsaiko before ya sake furta, "Thank you."
Dariya Hanif yayi, sai yace, "muna nan zuwa, zan kawo Amaryata su gaisa da Maryam, amma bazan jima ba don zan wuce mu haÉ—u da wani Likita da muka soma magana a kan matsalar My Amrah, so zan kaita ne kawai in ajiye ta."
"Ok, but bazan koma ba gaskiya, zan je Company don ina buƙatar in je in hadu da Mahmud mun yi waya da shi."
Daga nan suka yi sallama,
Har ya ajiye wayan sai kuma kiran Haseena ta shigo wayansa,
Tsayawa yayi yana kallon Phone din, Sai da ta katse kiran ta sake kira before ya ɗaga, amma ya ƙi yin magana yayi shiru yana sauraron ta
Daga can muryan Haseena ya bayyana, ta kira sunan sa da faɗin, "dear, Wai me ke faruwa nake kiran ka kake ƙin ɗauka? I called you yesterday night but baka yi peaking ba, after all ka san da cewan muryanka nake buƙatar ji, tunda ka ji na kira ka ka san da hakan."
Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarce shi, lallai yarinyar nan ta raina mishi hankali, muryansa a kausashe wanda ya kasa ɓoye ɓacin ransa yake cewa, "oh! Haka ne? You need to hear my voice, that's why you call me ok? I thought you forgot me in this world ban zaci hakan ba, Haseena, nayi mamakin abubuwan da kika aikata min, ina bin ki kamar ƙaramin Yaro, na ƙasƙantar da kaina duk sabida ina sonki, ina azabtuwa da kaunarki, ina buƙatar ki a cikin rayuwata, amma ba ki gane haka ba, lokaci guda kika juya min baya, kika kasa bani farin cikin da nake bukata, Haseena stop pretending that you love me after now I have no use for you."
Mamakin furucin sa ne ya cika ta, domin ta san cewa SHAREEF bai taɓa gaya mata irin waɗannan maganganun ba tun sanda ta samu damar ƙara cusa mishi soyayyarta a zuciya, a kullum in ya kira ta roƙon ta yake yi da magiya yana kuka da idanunsa, amma a yau kuma abun mamakin har ya samu bakin gaya mata magana, don haka tace, "Dear, Ni kake fada wa haka? Ko ka manta wace ce Ni?"