Sashe 68
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dole SHAREEF ya zauna tunda ba shi da yanda zai yi, amma ya san bazai iya cin komai ba
Hanif ne yace, "bari in haÉ—a maka da kaina Bro."
Momy kuma sai ta miƙe, "Ni bari in je wurin ta in zauna da ita, tunda farkawar ta muke so a soma bata magungunan ta."
Daga haka tabar wurin zuwa É—akin da Maryamu ke ciki,
A lokacin da ta shiga ta tarar da ita tana ta kuka tana riƙe da kanta sai nishi take yi,
Da saurinta ta ƙarisa gare ta hankalin ta a tashe tana kiran sunanta, yayinda ta kama hannunta da ke saman kan nata ta sauke tana mai ƙoƙarin tallabo ta tana jero mata tambayoyi
"Kaina Momy, zai cire, ki yi min addu'a zai cire, don Allah ki taimaka min zan mutu."
Haka take faÉ—a tana kuka ta kasa buÉ—e idanunta ma saboda azaba
Momy kamar tayi mata kuka haka take ji, ba ƙaramin tausayi ta bata ba, da sauri ta kama mata kan ta soma koro mata addu'o'i a fili tana tofa mata
A hankali kuma sai ta soma jin azaban yana rage wa, tun tana kukan da iya ƙarfin ta har ta soma ragewa tana ƙara ƙanƙame Momyn
Sosai Momy tayi mata addu'a tana ta tofa mata har sai da ta tambaye ta, "shin ya dena mata ciwon?"
Daƙyar ta gyaɗa kanta a hankali tana buɗe idanun nata, sai dai zugin da ƙafarta ke faman yi yasa tace, "Momy saura ƙafana, tana min ciwo sosai kamar zata cire, shima ki yi min addu'a na kasa ɗaga wa."
"To ki dena kukan haka nan, kinga shi ke ja miki ciwon kan, bari in yi miki insha Allahu za ki ji sauƙi."
Sai ta koma wurin setting ƙafan; tare da ɗago ta zuwa jikinta ta ajiye a hankali gudun kar ta ji zafi, nan ma addu'ar ta soma mata tana ta tofa mata
A haka SHAREEF ya shigo ɗakin ya tarar da su a haka, da sauri ya isa wurin nasu yana mai farin cikin ganin Maryamun ta farka, zama yayi saman bed side drowa yana mai riƙo hannun Maryamu
A nan take ta buÉ—e idanunta, yayinda ta zuba masa su sun cika fam da hawaye sun kaÉ—a sun yi jazur sun kumbure
Da sauri ya washe baki yana mai shafa face É—in ta, while yace, "Maryama, kin farka? Ya jikin naki?"
Shiru tayi don baza ta iya magana ba a halin da take ciki na ciwo, sai dai ta kafa mishi ido tana kallonsa tuni hawayen idanuwanta sun ci gaba da zuba
Momy tace, "SHAREEF, yanzu ɗauko maganin ta a fara bata tunda ta farka, ga su can ka kwaso su sai ka bata, Ni bari in ci gaba da tofa mata addu'ar a ƙafar; tace yana mata zugi."
"To Mom." Ya amsa yana tashi ya nufi inda aka zuba magungunan saman dressing mirror,
Shi ya kwaso da kansa ya soma bata after ya fita ya samo ruwa tunda wani kwaɓa wa za a yi akwai na ƙafa da ake shafa mata
Tare suka dawo da su Dady suma suka shigo cikin É—akin, sun ji daÉ—in yanda Maryamun ta farka, musamman bayan da aka soma bata maganin a hankali ta soma washe wa natsuwarta yana dawowa jikinta,
Ba ƙaramin farin ciki suka yi ba sun zauna gaba ɗaya a tare da ita suna ta mata sannu
After an gama bata maganin, Momy sai ta hana a shafa mata na ƙafan, tace, "SHAREEF ya je ya ɗauko mata kayanta a gida ko kala biyar ne, zata yi mata wanka yanzu inyaso sai a shafa mata maganin."
Don haka suka fita gaba É—aya suka bar Momyn da Maryamu,
While SHAREEF tare da Hanif suka fita a tare zuwa gidansa zai raka sa
Ko kafin su dawo Momy ta taimaka mata tayi wanka har ta shafa mata mai tunda garin akwai hunturu, yanayin sanyi ya fara shiga, da kanta ta amshi kayan ta saka mata sannan ta shafe mata ƙafar da maganin,
Shi kuma SHAREEF ya je ya haÉ—o mata break first Momy ta amsa ta bata da kanta
Haka suka mayar da ita kamar ƙwai a gidan nan, ko jirgawa SHAREEF ba ya yi a kusanta yana manne da ita don a jikinsa ma take kwance, yayi ta rarrashinta yana gaya mata kalamai masu sanyi da daɗi a cikin kunnenta, duk don ya faranta mata
Har Hanif bai bar gidan ba suna tare har dare sannan ya tafi
While SHAREEF kuma a gidan ya sake kwana
Sai dai kuma sabon al'amarin da ya sake kunno wa zuwa safe, kamar wasa jikin Maryamu yayi sauƙi har an fito da ita Falo tunda ba ta iya tafiya, ƙafarta ta kumbura suntum ta ja ruwa sosai,
SHAREEF ke zaune kusa da ita yana bata tea a baki,
Kawai sai ta soma aman jini lokaci guda ta sarƙe da tari numfashinta ya soma sama da ƙasa, nan da nan jini ya jiƙa gaban riganta yana fita ta hanci da baki
Tsananin ruɗe wa da tashin hankali ya riske su, da gudu su Momy suka ƙariso wurin sabida jin kiran da SHAREEF yake musu ya gama ruɗe wa yana kiran sunan Maryamu da ta dena motsi idanunta sun koma fari kamar babu rai a jikinta,
Take ya fashe da kuka yana salati yana cewa, "Momy ta mutu, ta mutu Momy, ku taimaka min don Allah." Ya rungume ta ƙaƙam yana girgiza ta yana kuka.
[11/05, 9:20 AM] Ù†Ùيسة OumÆŠahira: 🌱🌱🌱🌱🌱
    *SHAREEF*
      _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱
_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_
*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*
__________
*BOOK2*
_______________*PAGE36*
_____Bazan iya misalta muku halin da suka shiga ba a sakamakon ganin yanda Maryamu take fitar da irin wannan jinin, babu numfashi a jikinta,
Musamman SHAREEF wanda kuka kashirɓan yake yi yana ta kiran sunan ta kamar wanda ya zauce shima, domin a lokacin ya sadakar ta mutu
Ita kanta Momy hawayen take zubar wa domin ta kasa jure wa
Dady ne mai ƙarfin hali har ya iya ɗaukar Maryamun tunda SHAREEF ya kasa, yace, "su wuce asibiti."
Shi ya saka ta a mota sannan ya kira driver yace, "ya tuƙa su zuwa asibiti."
A halin da suke ciki a rikice suke babu mai iya tuƙa motan
Gaba É—aya suka wuce zuwa asibitin,
Dady sai rarrashin SHAREEF yake yi ganin yanda yake ta kukan ya kasa yin shiru,
Yace, "kuyi haƙuri ku dena wannan kukan, ba shi ne maslaha ba, addu'a zamu yi mata, Allah ya tashi kafaɗunta."
Amma sam SHAREEF ba ya iya jinsa, shi ya riƙe Maryamun a jikinsa sai tattaɓa mata face yake yi, in yayi-yayi kuma sai ya koma ya rungume ta ya sake fashe wa da wani sabon kukan
A haka har suka ƙarisa hospital, yayinda tuni SHAREEF ya fitar da ita ya nufi asibitin da gudun sa,
Su Dady suka bi bayansa zuwa ciki,
Wurin Likitan Dadyn suka nufa tunda asibitin ne aka kawo ta
Dayake sun tarar dashi nan da nan ya sanya aka amshe ta aka shigar da ita emergency, ƙarshe oxygen aka sanya mata sabida ganin bata numfashi, daga nan suka fara bata taimakon gaggawa, Likitoci biyu ne a kanta sai wasu Nurse's su uku
Yayinda su SHAREEF suna haraban wurin hankalin su a mugun tashe, suna ganin yanda ake shige da fice daga cikin É—akin,
SHAREEF ya kasa tsayuwa ma illa zama da yayi a ƙasa a jikin bango ya takure kansa, a lokacin ya dena kukan amma idanunsa sun ƙanƙance sun yi jazur da su, ko gani sosai ba ya yi sabida yanda suka tara ruwan hawaye, zuciyarsa kamar zata fashe don baƙin ciki, ba ya son ya rasa Maryamu a wannan lokacin, domin a yanda yake matuƙar ƙaunarta ji yake yi sai dai ya bi ta can, saboda bazai iya rayuwa babu ita ba, ya saba da ita a ɗan ƙanƙanin lokacin nan, fatansa kawai Allah ya tashi kafaɗunta yasa baza ta mutu ba, sai ga hawaye shaa sun ci gaba da zuban masa, sai yayi saurin ɗaura kansa a ƙafafunsa yana sakin numfashi mai wahala jijiyoyin wuyansa dana kansa duk sun fito masa raɗo-raɗo, fuskar nan ta sake ja tayi kamar ɗanye
Ƙarshe suma su Momy wuri suka samu suka zauna sabida sun kasa tsayuwa,
A inda Momy take ba shi baki cike da tausayinsa, tana gaya masa, "ya riƙa addu'a, yanzu addu'a Maryam take bukata, babu abinda zai same ta insha Allahu."
Itama tana yi tana share hawayen face É—in ta sabida tsananin tausayin Maryamun
Ba a jima ba a lokacin Likitan ya fito hankalin sa a tashe sabida sun kasa shawo kan matsalar, basu gane komai ba, har yanzu ba ta motsi sai dai sun tabbatar akwai rai a jikinta, sun yi iya yin su basu gano komai ba, infarct ma jinin da ke É—iga ta hancinta da bakinta still zuba yake yi, sun rasa yanda zasu yi su tsayar, ya fito a tsorace hankali a tashe ya nufi wurin su
Suma tuni sun miƙe tunda suka hange shi,
Dady yayi saurin tambayarsa shima hankalin nasa a matukar tashe kamar zai yi kuka?
"Be patient, it's too bad, we don't know what's wrong with her, abun tashin hankalin her blood refused to stop, we can't stop it, we don't know what's wrong with her, we need more information to save her life before we lose her Well, I'm not sure she'll be alive for more minutes."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..."
Abinda suke furta wa kenan sun gaza yin magana suna sauraron Likitan da ke ƙara musu bayani
Yayinda SHAREEF ya gaza motsi ma sabida halin da yake ciki, tamkar ƙirjinsa zai fashe don ɗaci da zafin zuciya gami da tashin hankali
Before suyi magana sai wata nurse ta rugo aguje tana kiran sunan Likitan, tana faɗa masa, "yarinyar tana motsi yanzu haka, tana can tana bige-bige sun kasa riƙe ta."
Da jin haka sai likitan ya bi bayanta da saurin sa,
While SHAREEF ma ya take masa baya don bazai iya jira a nan ba, dole ya je ya ga halin da take ciki,
Hakan yasa suma su Dady suka bi bayansa a rikice