Sashe 31
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kansa ya gyaɗa mishi ba tare da yayi magana ba, duk da fargaba ce sosai a ransa gudun kar su ƙi amincewa
Shiru Dady yayi shima bai ce komai ba
Ita kanta Momy mamaki ne ya cika ta, tace, "Hanif, yanzu kurman ne zaka aura?
Kallonta yayi cikin sanyin murya yace, "Mom tana da hankali ne shiyasa, yarinya ce mai tarbiyya shine abun da ya ja hankalina gare ta, kuma mun fahimci juna sosai wlh."
Girgiza kanta tayi tace, "Yaro Yaro ne, amma ina gamin ka da Kurma Hanif? Koda kun fahimci juna ai bata dace da kai ba, saboda matsalar a nan gaba ake gudu, taya ya zaka auri wacce ba ta magana?"
Dady yace, "ba batun wannan ba Dija, ai itama Allah yayi ta, baza mu hana sa abun da yake so ba, ta Yiwu shi nashi ƙaddaran kenan auren irin ta, amma before mu yanke hukunci yakamata ka sake nazari da kyau Babana; gudun abun da zai je ya dawo, don ba jima wa za a yi ba, muddin nayi bincike auren kawai za a yi a haɗa dana ɗan uwanka in Matar tashi ta dawo."
Sai yanzu Hanif ya ji sanyi a cikin ransa, nan da nan murmushi ya bayyana a kan face É—in sa yana faÉ—in, "Insha Allahu Dad."
Momy bata yi magana ba tunda ta ji abun da Dady yace, sai tayi shiru kawai duk da har ranta ta damu da jin wacce ɗan nata zai aura, amma kuma kamar yanda Dady yace ne, in ƙaddaransa ne auren ta dole su bar shi yayi, baza su matsa mishi ba
Duk abun nan da ke faruwa SHAREEF na sauraron su daga inda yake amma bai ce komai ba, sai da Dady ya kira sa sannan ya miƙe ya taho wurin
Bayan ya zauna a gefen Sadiq; Dady yace mishi, "to ka ji muna maganar auren ɗan uwanka, in har nayi ƙwaƙkwaran bincike babu matsala za a haɗa auren da naka, yaushe ne ita yarinyar zata kammala karatun nata?"
Shiru SHAREEF yayi na É—an wani lokaci kamar bazai yi magana ba, sai kuma can ya buÉ—e baki yace, "few months ne Dady."
"To Alhamdulillah Allah ya kaimu lokacin, sai ku zaɓi kowanne gida da zaku zauna, but a kusa nake son zaman ku; kunji ko?"
Hanif ya amsa mishi da baki, while SHAREEF kansa kawai ya É—aga
Maryamu tana zaune tana jin duk abun da ke faruwa, amma ta kasa É—ago kai saboda gudun a gane halin da take ciki,
Momy ma sai kallonta take yi tana son ta gane wanne yanayi ne a tare da ita,
Amma ko kusa bata É—ago kai ta kalle su ba, don ba ta bukatar kowa ya gane yanayin ta,
Sai ma tashi tayi ta wuce wurin Dinnig ta zauna tana zuba abincin ta,
Amma yadda zuciyarta take buga wa natsuwarta tana neman ta ƙwace mata, ƙarfin hali kawai take yi da hana bayyanuwar tsantsan tashin hankalin ta, haƙiƙa tana kaunar SHAREEF sosai, amma ya rigada ya yi mata nisa, nisan da baza ta taɓa cin masa ba, tabbas dole ta ba wa kanta haƙuri ta danne komai ya wuce, a yanzu babu abun da take so sama da ta san matsayin ta, baza ta iya jure zama a haka tana kallonsa da wata bayan ita ba, tana da matukar kishi, ta gummaci ta rabu dashi in dai a yanzu ne, rabuwa na har abada kuwa
Suma su Momy abincin suka koma saman Dinnig suna ci,
While SHAREEF yana zaune a kan dogon kujera yayinda ya ƙura wa TV ido, a zahiri tamkar kallon yake yi, sai dai ba haka bane, remote yana hannunsa yana canza channels amma ba ya gane komai,
Jima wa kaɗan kuma ya miƙe yayi musu sallama ya haura sama
Maryamu a sace ta bi sa da kallo har sanda ta ga ya ƙule mata, before ta ɗauke kanta tana jan dogon numfashi mai ƙarfi
Momy ce kadai ta kula da halin da take ciki, girgiza kanta kawai tayi tana kawar da kai daga kallonta, sai yanzu ta ƙara tabbatar wa har yanzu SHAREEF yana a zuciyar Maryamu, amma yadda ta sauya tana danne komai a zuciya; ba ƙaramin burge ta tayi ba, ko banza yanzu ta nuna tana da aji.***
The following day. Maryamu sai kusan ƙarfe goma ta tashi, tun tashin ta da asuba ta koma sai yanzu ta farka,
Tayi wanka ta saka doguwar rigan atamfa mai kalan purple da kwalliyar star mai kalan ruwan madara, doguwar hannu ne da rigan mai bottles a ƙarshen hannun, haka ma gaban rigan an sanya two bottles; yayinda wuyan ke da Coller,
Cif tayi mata rigan daga sama while ƙasa kuma ta buɗe,
Sai da ta É—aura É—ankwalin before ta wuce ta nufi Falo
Babu kowa sai Sadiq a Falon,
Yana kwance a doguwar kujera wayansa a hannun sa yana faman latsa wa
Wurin sa ta nufa da fara'an ta ta kira sunan sa, "Yaya Sadiq good morning?"
Sai da ya ɗago ya dube ta before ya miƙe zaune, face ɗin sa da murmushi yace, "Morning My lovely sis, kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah Yaya." Ta amsa mishi tana zama gefen sa
"Sai yanzu kika tashi har Yaya Hanif ya tafi."
"Eyya ban ji daÉ—i ba, na so mu sake yin sallama, but zaka ara mun waya ai na kira shi, Ina Momy?"
"Momy tana sama ita da Dady."
"Yauwa Yaya Sadiq, Please ina son zuwa shopping don Allah ka kaini, There are things I need to buy, and I want you to buy me a phone please, na gaji da zama haka nan nima na ƙosa in riƙe tawa since na zama big girl."
Dariya ta ba Sadiq, sai kuma ya ji daɗi musamman da ya ji tana turanci ba kamar haukan ta a baya ba, yanzu ta ɗan kware ba shirmen da ta saba yi ba, ba ƙaramin burge sa tayi ba, sai yace, "Ni dai bani da kuɗi Maryam, but mu bari Dady ya fito sai ki tambaye shi, inyaso ko zuwa after azuhur ne sai mu je shopping ɗin, ai bazai yiwu a bar big girl babu waya ba."
Dukka suka yi dariya sabida ta gane tsokanarta yake, But sai tace, "thanks sweet Bro, amma yaushe ne zaka tafi karatun ka? Na ji Momy tana maganar da Ammee lokacin kafin su tafi."
Sadiq yace, "ba yanzu ba ai, maybe before ki tafi or after kin tafi, just few weeks."
"Allah ya kaimu lafiya."
"Amin ya Allah".
***
_____Koda Maryamu ta faɗa ma Momy zasu fita shopping da Sadiq, bata hana su ba, ita da kanta ma ta basu kuɗin, Dady ya ƙara musu ya bada kuɗin wayan tare da nasu Aakifah, yace, "a siya har da su."
Maryamu sai murna take yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, shiyasa da suka je supper market din, ita da kanta ta zaɓi wayoyin dukka iri ɗaya, but ta bambanta color din rigan wayan, ita nata sky green ne domin kalan ne ta fi ƙauna, suma sai ta ɗaukar musu nasu favorites ɗin,
Suna cikin siyayyan ne tayi gaba tana neman abun da zata É—auka tana tura basket da take zuba siyayyan nata
Sai ga wani saurayi ya zo ya sha gabanta yana mata magana
Maryamu tunda ta kalle shi sau É—aya ta É—auke idanunta a kansa bata sake kallon sa ba, sai dai sauraron sa da take yi tana duban abun da zata É—auka
Sadiq daga can nesa ya hango su, Saurayin na kokarin jan mata basket É—in wai zai taya ta É—auka, nufo wurin yayi yana duban sa da cewan, "excuse me Oga, ya haka zaka tsaya da Matar aure kana shishshige mata?"
Da mamaki saurayin yake kallonsa, sai yace, "haba, ai na ga ita kaÉ—ai ce kuma bata yi min kala da Matar aure ba."
"To a goshin ta za a rubuta ne?" Sadiq yayi maganar cikin ɗaure fuska, har yana saka hannunsa ɗaya a aljihu tare da goce tsayuwar sa irin na isassun Mazan nan, ya ƙara da faɗin, "don Allah kabar nan wurin in ba so kake in maka duk abun da ka siya da kuɗin ka ba, Matana ce ita, zaka iya tafiya yanzu."
Yanda Sadiq ya tsare sa da ido babu alamun wasa a tare da shi, bare yanda ya ganshi jibgege shiysa bai yi musu ba, a tunaninsa da gasken shine Mijin nata, hakan yasa ya ba shi haƙuri ya wuce a wurin da saurin sa
Mai Maryamu zata yi in ba dariya ba, ta kasa riƙe dariyanta sabida abun da Sadiq yayi
Yayinda shima yake taya ta yana ƙara gyara gaban rigansa sai ƙwambo yake yi, "yo ya kika ga acting ɗin nawa? Wlh ya ɗauka Ni Mijin naki ne fa."
Dariya tayi ta É—aga masa hannu alamun jinjina tana cewa, "Yaya Sadiq wlh ka burge Ni."
"To in ban da abun shi É—an rainin wayon, an gaya masa kowa ake gani a hanya a kula? To an riga sa wannan, ina wuri baza a ci wa auren Yayana mutunci ba."
Jin hakan yasa Maryamun bata sake magana ba, sai ma gusar da dariyan fuskarta tayi tare da canza zancen nata tana yi tana duba abun da zata dauka
A haka suka gama siyayyan su; tunda shima Sadiq ya siya wasu abubuwa nasa da yake bukata in zai wuce England,
After sun biya suka koma Mota, ya ja suka bar wurin, suna ɗan taɓa hira kiran SHAREEF ya shigo wayansa,
Rage gudun motan yayi sannan ya amsa call É—in
Daga can side É—in SHAREEF yake tambayarsa inda yake a yanzu?
Yace, "muna kan hanya ne zamu koma gida."
Umarni ya basa a kan, "ya biyo Company yanzu yana neman sa."
Bai tsaya jin ta bakin sa ba ya katse kiran
Maryamu kuma bata san da waye yake wayan ba, sai da ta ga ya karya kwana ba hanyar da suka biyo ba, ta kalle sa tace, "wai ina zamu je ne Yaya Sadiq?"
"Companin mu zamu je, yanzu da Yaya SHAREEF na gama waya yace in je in same shi."