← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 75

Sashe 70

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE37*
_____Cikin ƙuduran Allah bayan an tashi tsaye wajen duƙufa da karatu da addu'ar karya ƙungiyar; tun a wannan daren mai afkuwa ta soma afkuwa, wanda sanadin haka Allah ya fara tona musu asiri, abun ya faru ne a lokacin da suke tsaka da yin meeting din su, wanda nan take gobara ta tashi ayar Allah ta soma tasiri a kansu, duk yanda suka so suyi wani abu mai kama da sihiri sun kasa,
Lokaci guda sai ga wasu daga cikin jami'an tsaro sun farmaki wurin nasu, dama sun sha kawo farmaki sabida abubuwan da ake faɗa a wurin da jita-jitan da suke samu, ko sun zo basu taɓa ganin kowa a wajen ba sabida an yi amfani da sihiri ba wanda zai ga mai ke faruwa a wurin, babban fili ne wanda aka kewaye wurin da bishiyu, a nan ne ƙungiyar asirin nasu take, majority a baya idan an so ganin bayansu ba a samun damar hakan, wanda ma yasan zancen ƙungiyar nasu rasa ransa yake yi, sai ga shi Allah da ikonsa sanadin ɗauke wani Yaron mai kuɗi da aka yi, sai aka kama mutumin batare da ya ida nufinsa a kan Yaron ba, Mahaifin Yaron kuma sai ya ɗauki mutumin ya danƙa shi a wurin hukuma, da aka matsa shi da duka da bincike, sai ya bayyana komai, kuma suka taso ƙeyanshi don ya kawo su wurin,
A kuma dai-dai nan saboda Allah ya so ya ga bayansu, addu'ar Malaman da suka wuni suna yi Allah ya amsa,
Wannan dalilin ne wajen ya fara kama wa da wuta sabida bom din da jami'an tsaron suka saka, sannan suka shiga suka yi musu rubuti kan mai uwa da wabi suka dinga duka suna kashe wasu, yayinda suka so yin amfani da tsafin su wajen tsira amma abun ya cutura,
Ƙarshe an kama wasu; wasu kuma an kashe su a nan take batare da an tausaya musu ba, aka rusa wurin gaba ɗaya aka yi baja-baja da komai

Kafin ka ce me; ƴan jaridu sun cika wurin ana ta ɗaukar rahoto, tun a daren labari ya soma yaɗuwa a kan wannan mummunar ƙungiyar asirin da yau aka ga bayan su, labarin da ya yaɗa kaf ƙasar Australia da ma kewayen ta, ana ta haska wa a TV da jaridu

A washe garin ranan ne Abba da ya tashi zai yi tafiya, ya je duba Haseena don ya sanar mata tafiyar nasa tunda ya jira - ya jira bata fito ba, amma abun mamakin ko sama ko ƙasa babu ita; daga ita har ƙawarta Nana, an duba gidan ko'ina babu su a ciki, kuma Mai gadi ya tabbatar wa da Abba, "basu fita gidan ba." in fact ma bai buɗe gidan ba sai da asuba lokacin da Abba zai je masallaci, shi kuma yana wurin a nan yayi Sallah tunda haka yake yi sabida gadin gidan,
Abun ya É—aure wa Abba kai, yayi ta kiranta a waya ko zai same ta amma babu labarin ta tunda wayan ba ta shiga,
Abun kamar almara kuma kamar wasa; zance ya zama gaskiya, tunda karshe da ya ji shiru bata dawo ba dole ya É—age tafiyar zuwa gobe,
Amma kuma babu ita babu labarin ta, abun ya soma tsorata shi hankalin sa yayi matukar tashi, sai ya koma bin dangi yana neman inda zai ga Haseena,
In takaice muku zance har gidan su SHAREEF sai da Abba ya je wai neman Haseena

Su kuma ɓatan Haseenan bai basu wani mamaki ba, sabida bayanan da Malam yayi musu a kan ƙungiyar, ya rigada ya bayyana musu cewar, "dole ƙarshen su ya zo, dole sai wata fitina ta afka musu sai sun tarwatse."
Suna ganin cewa hakan yana da nasaba da addu'ar da aka yi musu,
Fatan su dai Allah yasa hakan ne don a yanzu burinsu kawai Maryamu ta samu lafiya,
But har yanzu dai shiru ne babu ci gaba a lamarin ta, tana cikin wani hali gaskiya, wanda idan bawa ya kalle ta sai ya tausaya mata, sai ya zub da mata da hawaye, sai ya koka mata,
A kullum hankalin su a mugun tashe yake, babu wanda ba ya zubar mata da hawaye, abun ya cutura don gani suke yi kamar zata mutu ne, wanda hakan yasa dole Dady ya kira iyayenta ya sanar musu, don kar ya zo ta mutu a hannunsu cikin wannan ciwon batare da sun sani ba, hakan bai yi musu adalci ba, ya faÉ—a musu iya abun da zai iya faÉ—a musu, daga ciwon da take yi na aljanu har izuwa yanzu da ciwon da ya dawo mata gadan-gadan kullum suna kanta aljanun

Gaskiya bazan iya misalta muku halin da iyayenta suka shiga ba, amma a ranan sai ga su sun shigo Kano, sai dai tun a kallon da suka yi mata na farko hankalin su ya ƙara tashi fiye da halin da suke ciki,
Inna kukanta ta kasa riƙe wa tana mamakin wai Maryamu ce ta koma haka? gaba ɗaya ta firirice ta gama fice wa a hayyacinta, idan tana wani abun tamkar mara hankali, har yanzu ƙafanta da ta kumbura har yanzu tana nan a haka sai ma ɗuran ruwa da tayi, abun kamar zai yi sauƙi sai kuma ba haka ba, kuma wai don an dage mata da neman magani ne, iya ƙoƙari ana yi a kanta gaskiya shiyasa ake samun sauƙi, da tuni ba wannan zancen ake yi ba

Baba dai kasa haƙuri yayi yace, "a ba shi ƴarsa ya tafi da ita gida, a can zasu yi mata magani."

Dady ya so ya ba shi haƙuri tunda ga shi ana samun ci gaba fiye da baya, abun ne idan yayi gaba sai kuma yayi baya, ya faɗa masa, "yayi haƙuri tunda a nan sun san mafarin ciwon nata, Malamin da ke duba ta yana iya ƙoƙarinsa ana dace wa."
Tunda aljanun kanta ne suka hana ta sukuni, kullum sai sun tashi mata, shi aljanin yana son wai sai an ba shi Matarsa, sai an sake ta

SHAREEF kuma ya ƙi sakinta duk da ganin halin da take ciki, don shi ya fi ta ma shiga wani hali, bare da ya ji maganar Baba da yake cewa zai tafi da ita, hakan ne yasa yace mishi, "babu inda za a je mishi da Matarsa, a barta a nan tunda shi ne Mijinta, idan ya raina ƙoƙarin su ne ya je ya kawo maganin a yi mata a nan, amma bazai ɗaga mishi Mata ko nan da can bane."

Dady ne ya daka mishi tsawa yana cewa, "baka da hankali ne SHAREEF? Shi da ƴarsa ka ce bazai tafi da ita ba? Ina ka taɓa jin an yi haka?"

Hawaye kwance a idanunsa yake cewa, "Dady ai ko shine Mahaifinta; Ni kuma Mijinta ne, ina ga ya raina ƙoƙarin mu ne shiyasa yake son tafiya da ita..."

"Rufe min baki dalla can, in ƙara jin ka sake magana a nan." Dady ya faɗa a tsawace a kuma fusace yana hararan SHAREEF ɗin

Shi kansa Baba sai yanzu ya ji bai kyauta ba har ransa, sai yace, "kuyi haƙuri don Allah, hankalina ne ya gushe sabida halin da na tsinci ƴata a ciki, na san Mijinta ya fi Ni iko da ita, don haka bazan ɗauke ta ba zan barta a nan ɗin, Allah ya bata lafiya."

"Amin Amin." Suka amsa su dukka,
Yayinda Dady ya sake ba shi haƙuri yana ƙara jaddada mishi, "insha Allahu zasu yi iya yin su, ko ina zasu je domin nema mata lafiya, yayi haƙuri ya barta a nan komai zai wuce da yardan Allah."

To dalilin da yasa aka bar Maryamu a nan kenan ana kula da ita,
Wanda sabida yanayin jikin nata ne yasa su Inna sai da suka yi kusan sati É—aya before suka koma cike da tausayinta da tunanin halin da take ciki

Haka rayuwar ta ci gaba da gudana, a halin yanzu itama Amra rashin lafiyar yasa an mayar da ita gaban mahaifiyar ta, tunda tun cikin da ta samu take faman laulayi mai matuƙar wahala, ga shi har lokacin babu ci gaba a samun lafiyarta, har Hanif ya yanke shwaran fita da ita ƙasar waje, sai kuma ciwon Maryamu ya dakatar dashi, sannan kuma daga baya sai itama ta soma ciwon

Momy tace, "ya É—auke ta ya mayar da ita gidan su sabida zasu fi kula da ita, tunda ciki ne zata fi samun kula wa wurin Mahaifiyarta."

Hakan ne yasa aka mayar da ita gida, yanzu kusan watanni uku kenan tana can har lokacin jikin babu daɗi, sai an dawo da ita kamar ta warke, kasancewar Afra take zaune da ita, sai kuma jikin ya sake rikicewa dole aka sake mayar da ita wurin Mama, ga shi irin cikin nan ne mai shegen tsirfa ga laulayi, ga babu damar tayi wani aiki, to ina ta ga wani lafiyar bare tayi wani aiki? Tunda tuni Likitoci sun hana ta ɗaukan komai koda tsinke ne, a cewar su, "cikin bai da ƙwari zai iya zube wa".
*** *** ***

_____Har wannan lokacin babu labarin Haseena tunda aka neme ta aka rasa, tun su Abba suna saka ran dawowarta har sun fidda rai, kuma ko kusa babu wanda ya ji labarin abun da ke faruwa duk da an haska a yawancin talabijin, dayake labarin ne kawai da inda abun ya faru, babu fuskokin jama'ar da aka kama
Chapter 70 · 0% Book details