Sashe 8
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zumbur Haseena ta miƙe tsaye tana kallonta zuciyarta na luguden buga wa, tamkar zata faso ƙirjinta don tsaban tsoro da tashin hankali, gaba ɗaya babu sukuni a tare da ita, hawaye tuni sun wanke mata fuskarta tsaban tashin hankali,
Wannan wacce irin mummunar ƙaddara ce ke shirin son ya tunkaro ta? Ina ta kawo kanta take kokarin kashe kanta?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,
Ta kiɗime ta rasa inda zata saka kanta, hawaye kawai ke ɗiga a kan face ɗinta suna ɓulɓuluwa da sauri - da sauri
Miƙe wa Nana tayi tana kallonta tace, "You better calm down because you don't have any other chance than this, muddin kika ce za ki fita to sai dai ki rasa rayuwarki, ba ki da wani zaɓi Haseena, komai naki a tafin hannuna yake, zan iya sarrafa ki a duk sanda na so."
Sai ta shafa face É—in ta tana sakar mata killer smile, before ta wuce tabar Falon gaba É—aya
Har ta fice kallon hanyar da ta bi take yi, kamar tayi suman wucin gadi bata san me ke wakana ba a lokacin, komai nata ya tsaya cak babu sauran abun da ke motsi a tare da ita, illa hawayen da ke ɗiga har yanzu suna kwaranya a ƙasa,
Sai kuma can ta zame ƙasa ta koma saman kujeran jikinta na kerma, kuka ta fashe dashi cikin tsananin tashin hankali da nadamar kasancewar ta a nan ɗin, "wayyo Allana! Mai na ja ma kaina; me ke shirin faruwa dani ne? Kungiyar asiri? Ni ɗin? Na shiga uku na lalace! Meyasa wannan ƙaddaran zata faɗo rayuwata? Meyasa na yarda da ita after all na san wace ce ita?"
Kuka ta dinga yi tana sambatu gaba É—aya ta firgice ta rasa inda zata tsoma kanta,
Lokaci guda wani tashin hankalin ya riske ta saboda ganin ta da tayi a dokan taji cikin mutanen da ta saba yin mafarki da su, ciki kuwa har da Nana da su Herin ƙawayenta,
Yayinda wani ƙaton Mutum mai dogon gashi yake tsaye a tsakiyar su wanda shi ya fi su munin gani, alamu shi ne babban su kuma Oga a cikin su
Idanunsa jazur yake kallon inda Haseena ta sandare ta fita a hayyacinta, tsawa ya daka mata sai ga ta a gabansa a ɗaure idanunta a kafe a kansa, alamun ma ba ita take sarrafa kanta ba, wani kallo yake watsa mata tare da magana da turanci, "tunda kika kasance a cikin mu dole ki bi ƙa'ida da dokoki, daga yau kin shigo cikin mu kenan da ke zamu riƙa yin komai, ko kina so ko ba kya so, don haka daga yanzu tunanin ki mu zamu riƙa sarrafa shi, ba ke babu musu har abada."
Sai ya ɗaga hannunsa take wata walƙiya ta bayyana da ƙoƙo a hannunsa, tun daga saman kanta ya soma zuba mata jinin da ke cikin ƙoƙon yana zuba jikinta, gaba ɗaya ya jiƙa ta sharkaf da jinin sannan ya ɗaga kansa ya soma sirkulle, bayan ya gama ya buga goshin ta sannan ya kamo yatsunta sai ga wasu zobuna sun bayyana a yatsun nata gaba ɗaya na hannun hagu, dukka iri ɗaya har wanda Nana ta bata su guda biyu da jima wa,
Dariya ya ɓaɓɓake dashi yana kallon jama'ar da ke wurin,
Nan fa suka dinga zagaye su tunda sun san me yake nufi, suna yi suna wasu karatu da babu kan gado, sun jima a haka before su dakata, kowanne cikin su ya zo yana shafa hannunta tare da mata maraba da zuwa cikin su
Haseena dai tana kallonsu da jin su batare da ta gane komai ba, kuma babu damar musu bare daukar mataki, a lokacin ma jin ta take yi wani iri kamar ana sauya ta, ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi bare ta san me ke faruwa da ita, tunda aka ɗaɗɗaka mata wani abu a baki daga nan bata sake sanin inda take ba,
Sai buÉ—e ido tayi ta ganta a saman gadon ta cikin halin ciwo ba ta iya sarrafa komai nata
Nana na gefen ta don ita take kula da ita, ganin ta farfaɗo ba ƙaramin farin ciki tayi ba, kiran sunan ta tayi tana kamo hannunta
While Haseena ta amsa mata tana kallonta cikin wani irin yanayi, baza ta iya cewa ga abun da ke damunta ba amma ji take yi kamar an sauya ta
"Sorry na san kina wani hali a yanzu, but bari ki yi wanka sai ki sha magani za ki wartsake ko?"
Ta ƙare da mata murmushinta wanda ba ya gushe wa a kan face ɗin ta, taimaka mata tayi ta tayar da ita takai ta har cikin toilet,
A takaice ita tayi mata wankan; ta nannaÉ—o ta a cin towel ta dawo da ita ta kwantar da ita,
Sannan ta je ta zuba mata indomie da ta dafa mata ta kawo mata ta bata da kanta, sai da ta gama sannan ta É—auko mata kayanta ta saka,
A hankali ta kama hannunta tana kallonta tace, "na san za ki ji sauyin yanayi a tare da ke, kar ki damu a hankali za ki saba kina jina?"
Kai Haseena ta gyaÉ—a mata ba tare da musu ba, saboda a yanzu jinta take yi komai take so zata iya mata babu wata gardama, jinta take yi tana son wani abu amma ta rasa mene ne
Kamar Nana ta sani sai ta ɗauko mata cup da ke ajiye, wanda akwai jini ne a ciki don shine abun shan su, basu da drinks sai shi, miƙa mata tayi ta karɓa
Sai da ta leƙa cup ɗin; ta ga abun da ke ciki sannan ta kalli Nana tace, "mene ne shi?"
Murmushi tayi mata tace, "ki sha zan faÉ—a miki."
Kanta ta gyaÉ—a mata, sannan ta buÉ—e baki ta kafa kai a ciki; sai da ta shanye before ta cire tana lanÉ—e baki kamar wata mayya
Hannunta ta ɗaura a nata tace, "daga yanzu irin wannan abun shine abun shan ki, ƙarfin ki da kuzarin ki zai ninku fiye da haka, jinin wasu mutane ne da muka sha, in kina buƙata kawai kina ɗaukar cup za ki ganshi a ciki."
Shiru Haseena tayi bata ce komai ba, kuma babu wani tunani a ranta face kallon Nanan da take yi
"I will explain to you everything that is in our group, you will understand everything, even the rules in it".
***
Tun daga lokacin Haseena bata sake tuna SHAREEF a cikin rayuwarta ba, domin a halin da take ciki komai nata ya sauya ta tsinci kanta a cikin wani irin rayuwa da bata taɓa tunanin ganinta a ciki ba, duniya ta soma sauya mata lokaci guda ta soma ganin sauyi a tare da ita,
Kuma a ɗan ƙanƙanin lokaci ta fahimci kungiyar su wanda har itama an bata dama tana gudanar da tsafi, komai ta taɓa in tana buƙatar abu zata iya samu, musamman ma kuɗi lokaci guda ta jiƙe da kuɗi, basu da sana'a sai fita yawo da su Nana suyi abun da suke so,
Ba iya SHAREEF ba har Iyayenta ta soma manta wa da su a rayuwarta; since bata da time É—in su
Kusan satin ta uku cif da kasancewar ta a cikin ƙungiyar, wanda SHAREEF ya gaza jure rashin ta duk da fushin da ya ɗauka da ita, jin shiru bata neme shi ba dole shi ya ɗauki waya ya kira ta,
Sai lokacin ta tuna dashi, kuma ta tuna abun da ya faru a tsakanin su before ya tafi ya barta, har yanzu tana son SHAREEF soyayyarsa bata sauya a tare da ita ba,
Amma kuma babu sha'awarsa a tare da ita don Nana ta ɗauke mata wannan; ita kaɗai take jin sha'awarta, in har ba da ita zata yi harka ba to baza ta taɓa bukatar wani ba,
Lokacin da ta É—auki wayan suna magana bata nuna masa komai ba, illa ma cewa da tayi, "ya manta da ita bai neme ta ba tsawon wannan lokacin, sabida ya dena sonta ko?"
SHAREEF ya rasa ma mai zai ce mata jin abun da tace, sai yayi shiru yana jan numfashi tare da jinjina ƙarfin halin ta
"Wai dear nayi magana kayi min shiru, meyasa ka rabu da Ni ne sai wannan lokacin zaka kira Ni? Nayi fushi da kai since ka dena sona, shikenan."
Sai ta kashe wayan É—ib
Tsantsan mamakin abun da tayi masa ne yasa shi kallon wayan; yayi kasaƙe yana kallon phone ɗin, lokaci ɗaya ya soma jin ransa na ɓaci saboda abun da tayi masa, yanzu ya sake tabbatar wa dole akwai wani a gabanta Haseena ta soma gajiya dashi, dialing numban ta ya soma yi ransa na ƙuna, yana jin ta ɗauka ya soma magana cikin zafi, "Haseena, Ni zan kira ki ki kashe min waya? Bayan duk wannan laifin da kika yi min? but now I called you and you hung up on me? Me ke damun ki?"
"Me ka gani? Ko nace maka wani abun na damuna ne? Kai ka tafi ka bar Ni a kan laifin da ban aikata ba, SHAREEF kai kaɗai ne wanda nake so ban taɓa kusantar wani mahaluki ba sai kai, meyasa ka kasa ganewa ne?"
"Haseena, Ni kike yi wa tsawa haka?" Yayi maganar cikin tsananin mamaki da al'ajabi
Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, yayinda ta zuba wa Nana idanu tana kallonta kamar yanda itama take kallonta tun shigowar ta cikin É—akin
SHAREEF kuma daga can kashe wayan yayi batare da ya furta komai ba saboda yanda ransa yayi matukar ɓaci
Kallon wayan take yi tayi shiru tana tunani a ranta
Nana zama tayi gefenta tana sanya hannu ta soma shafa ta before tace, "babe, me ke faruwa ne? Da ke da Boyfriend naki ne ko?"
Ɗago kai Haseena tayi tana kallonta; but still ta ƙi yin magana
"Wai meyasa baza ki rabu da shi bane? Ni fa ina kishin ki a kan wannan mutumin sabida na ga alamun kina matuƙar ƙaunarsa, har yanzu na kasa cin galaba wajen raba ku, yanzu ba amfanin da zai miki ki rabu dashi Please?"