Sashe 54
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayinda Maryamu itama ta saki baki ta dinga rattafa mata labarin soyayyarta da SHAREEF, ta faɗa mata yadda ta so shi so ba kaɗan ba, "duk da a wannan lokacin tana jin haushin shi da kuma tsanar sa, amma maganganun da ya fada mata a jiya yasa ta ji sauƙin komai, jiya ta kwana cikin tunanin sa tamkar soyayyarsa ta dawo sabo a tare da ita, tana jin tabbas baza ta iya rabuwa da SHAREEF a rayuwarta ba, domin shi ƙaddaranta ne, sai dai kuma abubuwan da yayi mata ya cutar da ita ba kaɗan ba, ta kasa manta komai har yanzu tana kallon abun da yayi mata a idanunta," sai tayi dariya a karshen maganar nata, ta sake duban Amran tace, "na so in tsane sa ya babu wani tamkar sa, sai dai ashe abun ba mai sauki bane a gare Ni, soyayyarsa ita ce ƙaddarata, a kansa na gane raunina, ada ina kallon kaina tamkar babu wanda yakai Ni Jarumta, kin san me? Hawayena suna wuyan fita a cikin idanuna, ina da taurin rai matuƙa, amma kuma; tun sanda na soma jin labarin sa, mafarin soyayyata a gare sa kenan, batare da na soma tozali da shi ba, tun a lokacin na san cewa Ni maƙurar mai rauni ne, domin na kasa ɓoye soyayyarsa koda na ɗan ƙanƙanin lokaci ne, a lokacin ne hawayena suka samu damar zuba, na zama mahaukaciya a kansa, ina jin a lokacin bazan iya rayuwa babu shi ba, idan har ban same shi ba mutuwa zan yi, na azabtu gaskiya kuma bai tausaya min ba, ina ji a raina a lokacin tabbas ba yin kaina bane, sabida ciwon da ya same Ni a wannan lokacin, na so na koya wa kaina tsanar sa, amma ashe hakan ba zai faru ba. Kin san maiyasa nake baki wannan labarin nawa?"
Ta ƙare maganar fuskarta a washe cike da farin ciki
Yayinda Amra kuma ta cika da tausayinta, tana kallonta ne tamkar ta zubar mata da hawaye, idanunta sun cika da ƙwalla, sai ta girgiza mata kai alamun a'a
Ita kuma sai tace, "sabida ina son ki bani shawara ne, a raina na ji cewar na zayyane miki komai, sabida a dai-dai wannan lokacin ke ce a tare da Ni, duk abubuwan da yayi min, kina ganin ya dace in yafe mishi da gasken yana son zama dani in manta da komai? Ra'ayin ki kawai nake bukata domin ba na son in ci gaba da bin ra'ayin zuciyata."
Shiru Amra tayi tana kallonta, sai kuma tahau mata rubutu tare da bata shawarwari a game da jin ta bakin ta, tabbas ta nuna ta tausaya mata, amma ta nuna mata cewan, "haƙuri shi ne ya fi komai a gare ta, bata da wani zaɓi face hakan, domin duk wanda yayi haƙuri a rayuwarsa wata rana zai yi dariya." Ta sake nuna mata matukar dacewan su da SHAREEF, kuma ta nuna mata, "tayi Sa'a sosai, babu amfanin ci gaba da ƙuntata mishi matuƙar ya nuna nadamar sa a gare ta, don haka kawai tabar komai ya wuce ko don samun farin ciki a tare da ita."
Sosai Maryamu ta ji daÉ—in shwaranta, kuma ta yarda har zuciyarta tabbas ta yafe wa SHAREEF komai, komai ya wuce, baza ta sake tuna abubuwan da yayi mata ba,
Don haka suka ci gaba da hiran su gunun sha'awa
Haƙiƙa Amra ta ji daɗin haɗuwa da Maryamu, ita kanta bata taɓa bama wani dama a rayuwarta kamar yadda ta ba Maryamu ba, ta saki jikinta sosai da sosai da ita
A haka suka jima har magriba sannan Hanif ya dawo É—aukar Amra,
Kuma har wannan lokacin SHAREEF bai dawo ba,
Yana can gidan su yayi zaman sa can tun sanda ya dawo daga Company, yana can yana tunanin yanda zai yi ya shawo kan mutumiyar tasa
Yayinda itama take zaune a gida tana faman jiran sa,
Inda a dai-dai wannan lokacin har wanka tayi ta cakare ta zauna a falo tana faman jiran sa, tana riƙe da wayan ta ta hau kan facebook tana karanta labarai sai dariya take yi tana nishaɗi
A wannan lokacin aka dauke wutan NEPA, ko'ina yayi duhu sabida kusan ƙarfe takwas da rabi saura ne a lokacin,
Wayan hannunta tayi saurin kunna wa tana haska falon, ta ajiye a saman kujera ta ci gaba da kwanciyar ta, tana lissafin yadda zata tarbi SHAREEF ta ba shi mamaki,
Dariya ta kwashe dashi, sai kuma ta ji dariyan nata yana fita bibbiyu tamkar ana kwaikwayon ta, hakan ne yasa ta dakatar da dariyan tana miƙe zaune idanunta a zare a waje cike da mamaki, abun ya matuƙar bata mamaki, amma don ta tabbatar da abun da ta ji maybe kunnenta ne, sai ta sake kece wa da wani dariyan, yayinda ta sake jin dariyan yana fita da karfi kuma bibbiyu, gidan yana amsa wa da ƙara,
Da sauri ta gimtse bakin ta tana ƙara zare idanu, a wannan lokacin mamaki ne kawai ya cika Maryamu amma babu ko ɗigon tsoro a tare da ita, don ita mace ce da ba komai ne yake saurin tsorata ta ba, koma wa tayi ta kwanta tana cewa, "oh! Illan sabon gida kenan, sai kayi haƙuri." Sai ta ja tsaki tana ɗaukar wayan nata ta ci gaba da latsa wayan,
Wanda yake É—ebe mata kewa na É—an wani lokaci
Can kuma sai ta soma jin iska yana kaÉ—a wa sosai har yana É—aga Curtin É—in Falon, tashi tayi ta nufi wurin windown ta soma rufe wa,
Har ta rufe sauran, ya rage saura guda ɗaya, tana ƙoƙarin rufe wa sai ganin ƙatuwar bak'ar Mage tayi a saman windown, ko kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi Magen nan tayi wani uban sufa ta ɗare mata jiki,
Ƙara ta saka tana wurgi da wayan, ta soma kiciniyar cire Magen a jikinta, amma inaa; ta maƙalƙale ta tana kai mata yakushi mai mugun azaba, wanda tuni ta rikirkitar da Maryamun nan da nan ta fita a hayyacinta ta faɗi ƙasa tana ihu da kururuwa, tsoro da tashin hankali gami da tsananin ruɗin ganin wannan mummunar Magen yayi matuƙar razanar da ita, kuka take yi sosai tana son fincike Magen a jikinta amma inaa ta kasa, kokawa suke yi sosai duk da yadda take yakushin ta tana cizon ta tana son cire ta a jikinta amma ta kasa, ga azaban da ke ratsa ta duk inda ta kafa mata ƙumba, kuka sosai Maryamu take yi duk ta fita a hayyacinta ta haɗa zufa kashirɓan ga hawaye shaɓe-shaɓe,
Daƙyar ta samu nasaran fincike ta a jikinta duk ta gama yaga mata riga ta ji mata ciwuka a wuya, tana yin nasaran wurgi da ita tayi wani irin ƙundunbala tana shirin gudu wa, daƙyar ta iya tashi ko ganin gabanta ba ta yi; ta ranta a guje zata shige dakin ta, sai dai rasa ƙofan da tayi yasa ta buga kanta da bango, wani uban ihu ta fasa idanunta sun rufe tuni ta afka cikin ɗakin ko ganin gabanta ba ta yi,
Da lalube ta ƙarisa bakin gadonta jikinta na rawa kamar mazari ta haye ta ƙudundune tana kuka da salati
Gurnani ta soma ji cikin É—akin alamun Magen ta biyo ta,
Ai kuwa nan ta hange ta sabida tana iya hango idanuwanta masu ban tsoro da jan haske kamar walƙiya
Da sauri ta toshe bakinta hawaye na ziraran mata tsoro da firgici gami da tashin hankali sun cika ta,
Tana ganin ta yo sufa zata faÉ—o kan gadon,
A guje ta miƙe bakin ta na ambaton salatin da bata san mai take furta wa ba, domin a lokacin Maryamu ta sadakar ta mutu bata taɓa ganin irin wannan bala'in ba,
Tana sauka saman gadon ta harÉ—e ta faÉ—i a wurin,
Magen ta kawo mata cafka tayi saurin riƙe mata wuya,
Yanda suka soma kokawa tana ƙoƙarin yakushe ta amma Maryamu ta riƙe mata wuyan gam ta shaƙe ta kamar zata kashe ta, tsoron da take ciki bata san ma mai take aikata wa ba burin ta kawai ta ceci kanta daga mummunar Magen,
Sai kawai ta samu ta dinga buga kanta da ƙasa babu ƙaƙƙauta wa, Magen na kuka kamar kukan Kura amma Maryamu ta ƙi ƙyale ta tunda ta samu wannan damar, kamar mahaukaciya haka ta koma tana dukan Magen ko ta ina,
Hakan bai yi mata ba sai da ta wawura inda zata samu abun bugu, nan hannunta ya taɓo Kujeran dressing mirror, da sauri ta miƙa hannu ta taɓo wurin mirror inda kayan kwalliyar ta yake, kwalban turare ta cafko ta samu ta buga mata
Magen ta tsandara wani uban ihu mai kama dana Mutum,
Lokaci guda Magen ta ɓace ɓat a hannunta
Hakan ba ƙaramin razanar da Maryamu yayi ba, ta sake ɗimauce wa lokaci ɗaya ta rarrafa ta miƙe ta bi hanyar ƙofa, tana zuwa dai-dai bakin ƙofan ta sake buga kanta da bango a kokarinta na neman ƙofan fita, nan ta saka ƙara ta faɗi a sume babu numfashi a jikinta
Wanda a dai-dai wannan lokacin SHAREEF ya dawo gidan, yayi siyayyan kaya maƙil a ledoji, ya kwaso kayan ya fito zuwa cikin gidan, sabida akwai duhu shiyasa yayi amfani da touch light na wayansa ya shigo cikin Falon,
A nan ya hangi hasken wayan Maryamu a yashe wurin window, tsaya wa yayi yana kallon wurin, sai kuma ya nufi cikin falon ya ajiye siyayyan da yayi mata, wayan ya É—auko cike da mamakin ganin ta a wurin a yashe,
Tunaninsa ya ba shi ko dai tsoro ta ji har tayar da wayan nata tunda babu wuta a gidan, don haka ya nufi ɗakin ta kansa tsaye ya burma, ya kusa cin karo da ita a ƙasan sai ya hange ta yashe kanta ya fashe yana zubar da jini,
A kiɗime ya duƙa gabanta yana kallonta cikin tashin hankali da al'ajabin halin da ya tsince ta
Ga ta nan a yashe goshin ta ya fashe, yayinda riganta kuma gaban rigan ya yage gaba É—aya sai bra É—in ta, wuyanta duk yakushi da kuma alamun cizo da yake tsittar da jini