Sashe 39
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Hanif yayi farin ciki matuƙa, domin har ga Allah bai da burin da ya wuce yanzu ya samu Amra a cikin gidan sa, soyayyar da yake mata bana wasa bane, bare yanda ya haɗe da tausayi, yana tausaya mata ko don rashin maganar nan nata, don haka a yanzu ya saka a ransa da zaran sun yi aure zai nema mata magani Insha Allahu, ko Allah zai sa a dace, duk da bai taɓa maganar da ita ba bare ya tuntuɓe ta ko an taɓa nema mata magani ne a baya, yabar dai maganar zuwa bayan bikin su
Amma sai dai kuma matsalar da suka soma fuskanta, iyayen Amra ƴan uwan Mahaifinta sun ƙi amince wa da auren, musamman da Baba Jafaru ya gane Hanif ne zai aure ta, sam ya ƙi amincewa tunda shine babba a cikin su, shine mabi da Mahaifin su Amra, kuma a yanzu tunda ya yanke hukuncin baza a bada auren ba, sai sauran ƴan uwan suka goya mishi baya, yayi ruwa yayi tsaki yace, "in har ba Jabir zata aura ba, wlh baza su taɓa bada auren ta ba."
Abun fa har ya zama fitina, don har maganar takai ga mai anguwan garin su, tunda Dady ya dage baza a tauye wa yarinyar haƙƙinta ba, tunda ya gane halayen Baba Jafaru shiyasa ya dage sai ya amsar musu ƴancin su, musamman da ya zauna da Amra da Mama ya ji ta bakin su, kuma yayi musu alkwarin, "Insha Allahu zai tsaya musu, bazai taɓa bari a cuce su ba."
Dalilin da yasa yakai ƙaran su kenan har hukuma suka sake shiga maganar, sanadin da Mai anguwan garin yace, "shi zai zame mata waliyi in an zo auren, kuma da sa hannunsa a tsayar da baikon su."
Haka kuwa aka saka ranan auren nan da watanni bakwai masu zuwa, wanda yayi dai-dai da kammala karatun Haseena za a yi bakin tarewan su tare
Duk yanda su Baba Jafaru suka so su tayar da ɓalli su nuna su ne dolen su Amra, amma abun ya faskara tunda an shigo da hukuma ciki, amma sun yi rantsuwa, "in har su zasu yi musu aure, to wlh ba da yawun su ba wannan auren, su je suyi duk abun da suke so sun cire hannu a kansu."
Dady kuma yace, "ya dauki maraichin su, shi zai zame musu Uba daga nan har Allah ya ɗauki ransa, Insha Allah baza su taɓa maraichi ba, duk abun da suke so shi zai yi musu."
Ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, domin har gida Mama ta zo ta yi musu godiya har da Momy, tare da su Amran ta zo suka zo suka nuna musu farin cikin su
Ita kanta Momy ta yaba da tarbiyyar Yaran, ba ƙaramin dad'i ta ji ba da ta ga yarinyar da Hanif zai aura, kuma ta yaba da kyawun ta, babu wani abun kushe wa a tare da ita in ba an faɗa maka tana da laluran magana ba, don a lokacin ji take yi tamkar su barta a hannunta ta zauna tunda ta shiga ranta, amma dai haka tabar abun a ranta tayi musu sha tara na arziki, yayinda Hanif ya mayar da su gida,
Ba abun da su Mama zasu yi wa Ahalin Hanif da shi kansa domin nuna musu godiyar su, domin basu da abun da zasu saka musu, haƙiƙa sun taimake su a lokacin da suke neman taimako, Allah maji roƙon bawan sa ne tunda har ya amsa roƙon su ya turo musu bayin Allan nan suka shiga rayuwar su, addu'ar Mama a kullum Amra ta samu inda zata huta da kuma wanda zai tallafi rayuwarta ya riƙe maraichin ta da laluran ta, sai ga shi Allah ya amshi roƙon su, haƙiƙa suna farin ciki a wannan lokacin tunda basu rasa komai ba albarkacin waɗannan bayin Allan da suka shigo cikin rayuwar su, basu da bakin musu godiya su wadatar da su
To tun daga nan haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yayinda a gefe ɗaya Hanif da Amra soyayyar su sai abun da ya ci gaba, suna kaunar junan su sosai, a kullum burinsu su faranta wa junan su rai, duk abun da yasan Amra zata nema a duniya yana iya ƙoƙarinsa na ganin yayi mata shi ko mene ne, koda bata ce ba in har ya ga abun zai dace da ita yana siya ya mallaka mata, kuɗin da yake kashe wa a kan Amra ba ƙaramin girgiza su yake yi ba
Ita kanta Amran tana gaya masa, "ya dena mata irin waÉ—annan É—awainiyar, ya bari idan ya aure ta ko mene ne sai yayi tunda ta zama nashi, amma abun yayi yawa yanzu."
But ba ya sauraron ta, bai fasa alherin da yake musu ba, domin yana ji ko nawa ne zai iya kashe wa a kanta, ita kaɗai ce Macen da yake jin ta shiga ransa fiye da ƴan matan da yayi a baya, yana matuƙar tausaya mata, yana tsananin ƙaunarta sosai, a kullum nuna mata yake yi domin ba kaɗan ba Hanif ya iya soyayya, yana faranta mata matuƙa,
Har tana jin cewa babu wata Macen da ta fi ta sa'ar Miji, a yanzu tana jin cewa ita ce ƴar baiwa fiye da kowanne mutum a duniya, haƙiƙa Allah ya ɗaukaka ta babu abun da zata saka mishi dashi sai biyayya gare sa da kuma nuna godiyarta da a kullum cikin ranta ba ta gushe wa da furta alhamdulillah sau babu adadi,
Allah shi ne gatanta kuma ga shi ya bata Mijin da tana jin baza ta taɓa samun wani bayan shi ba, ya ɗauki ɗawainiyar ta kuma ya ɗauki na ƴan uwanta, da mai zata saka mishi? Bata da sauran baƙin ciki a yanzu, shiyasa take mugun sonshi, tana mishi soyayyar da bata taɓa tunanin zata yi wa wani ɗan Adam ba, haƙiƙa dukkan su suna cikin farin ciki duk makusantan su sun san da haka
Musamman ma Hanif, a yanzu shi ya zame hannunsa gaba ɗaya a kan SHAREEF, ba ya kula sa balle ya damu da sha'anin sa, tunda duk wani shawara da zai ba shi ya rigada ya ba shi but ya ƙi aiki dashi, sai dai ya zura wa sarautar Allah ido, ya ƙyale sa yayi duk abun da zai yi, shi dai a yanzu yana farin ciki kuma ba ya son abun da zai daƙile mishi duk wannan farin cikin nasa
Dama ai haka soyayya take, wasu ta sanya su cikin farin ciki da nishaÉ—i, su ji kamar babu wanda ya fi su dace da Abokin rayuwa na gari, wasu kuma akasin haka ne, yayinda Allah zai jarabbe su ta fannoni kala-kala,
Yanzu dai SHAREEF yana cikin wannan jarabawar da bai san ranan fitan sa ba, domin a yanzu bai da wani sauran sukuni, kawai rayuwa yake yi amma babu farin ciki bare nishaɗi a zuciya, sai dai yana iya bakin ƙoƙarin sa wajen ɓoye halin da yake ciki.
***
A can kuwa fannin Maryamu tabbas ta share babin SHAREEF na har abada a cikin rayuwarta, ada tana jin baza ta iya rayuwa babu shi ba, amma a yanzu komai ya sauya, kamar yanda ya nuna mata ɗabi'un sa ya muzguna mata bai tausaya mata ba, tabbas tayi imanin baza ta taɓa farin ciki da samun sa ba, a yanzu babu wani ɓurɓushin soyayyarsa, sai ma zallan ƙiyayyarsa da take jin a koyaushe yana mamaye mata ilahirin zuciya, tsab ta kulle shafin sa karatu kawai ta saka a gaba shine burinta a koyaushe
Suna cikin tsaka da karatun ne aka aiko Bintu ta haihu É—a namiji,
Sai dai babu damar da Maryamu zata je duk da ta ci burin zuwa duk sanda ta haihu, amma kuma sabida karatunta bazai yiwu ta tafi ba,
A lokacin suna tsaka da karatun su ne, babu jima wa suka zana jarabawa suka samu Hutu a time É—in
Sai dai bata samu damar zuwa ba har suka gama hutun suka sake koma wa school, suka ɗaura karatun su, wanda daga wannan hutun ne kuma sun gama da SS 2, in sun dawo zasu shiga ajin ƙarshe, abu kamar wasa, dama komai lokaci ne, duk abun da ake nema wata rana za a cin masa
Ga shi yau da gobe itama Haseena har ta kammala karatun ta ta dawo gida, sai dai fa a inda gizon ke saƙan, kuma rigimar take, yadda ta dage tace ma Mahaifinta, "zata koma can ta ɗaura karatun ta na master's, don baza ta iya zama a nan ba, can take son zuwa ta ci gaba da karatu."
Kuma a wannan lokacin take bukatar komawa, cus tayi musu ƙaryan, "tana business a can ba ƙaramin kuɗi take samu ba."
Su kansu sun san Haseena ta sauya sosai, musamman yanda take jiƙa su da kuɗi tayi ta tura musu kuɗaɗe shiyasa suka amince da cewan sana'a take yi kamar yanda ta ɗaura su a kai, sun hau sun zauna sun amince da ita,
Sai dai Ummansu ne ta ƙi amince wa da komawar ta can abroad ta ci gaba da karatu tunda da auren SHAREEF a kanta, gwara kawai ta tare hakan zai fi, inyaso tayi karatun ta a nan, daga nan har ta ga ƙarshen biro wanann ba damuwarsu bane
Amma sam Haseena ta nuna ba ta so, ita can take son tafiya ko don business ɗin da take yi yanzu, kuma actually sabida Nana zata koma can da zama a nufin zata je ta ci gaba da karatu, dama ko da yardan iyayenta ko babu yardan su baza ta taɓa yin nisa da Nana ba, a yanzu baɗalar da suke yi abun yayi tsamari babu yanda za a yi suyi nisa da juna har wani lokaci, already rayuwar can ya ruɗe ta don ji take yi baza ta iya zaman Nigeria ba, duk wani wayou dole ta yi wa iyayenta ta tafi, SHAREEF kuwa ba a maganar sa don bata da matsala dashi, ko ya yarda shima ko kar ya yarda zata yi tafiyar ta ne, amma bai isa ya ja da zancen ta ba tunda ta san bazai taɓa dena sonta ba