← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 75

Sashe 35

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka Hanif ya zo ya tarar dashi cikin wannan halin yana hawaye kashirɓan, ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba sabida rabon da ya ga ɗan uwansa a wannan mugun yanayin ya jima, musamman yanda yake kwararar da hawaye mai yawa har haka,
Cikin tashin hankali ya matsa kusa dashi yana tambayarsa ba'asin kukan nasa?

Yayinda zuciyar SHAREEF na tafarfasa yake duban Hanif ɗin, idanunsa sun yi ja sun kumbura suntum ga damuwa da ke tattare a kan face ɗin sa, yayinda cikin sanyi da karayar zuciya yake cewa, "ban san me nayi Allah ke jarabta na da soyayyar Haseena ba, na kasa cire ta a raina kamar yanda itama yanzu ta dena so na, Haseena ta sauya min ta dena son farin cikina, ban taɓa tunanin zata juya min baya ba, amma kullum jin sonta nake yi har cikin raina."
Sai ya ja numfashi daƙyar ya ƙara da faɗin, "ina son in manta da ita a raina amma ban san yanda zan yi ba, kamar Ni SHAREEF har na kai lalacewar da wata Mace zata iya wulaƙanta Ni?"

Girgiza kansa Hanif yayi cike da tausayinsa, don ba ƙaramin tausaya mishi yayi ba sabida ya san cewa tabbas yana cikin wani hali da ciwon abun, but sai yace, "Mace ta wuce tunanin ka Bro, duk yanda ka so da nuna mata kai ne a saman ta; gata da nasaba da kyawu gami da tsantsan wayewa; a wurin Mace ba komai bane kai Bro, musamman idan akwai soyayya. Ba tun yau ba na ce maka ka cire yarinyar nan a ranka ka ƙi, already yanzu ba sonka take yi ba, why not baza ka iya ɓanɓare ta a rayuwarka ba? Ba fa ita kaɗai bace Mace a duniya ba, sai lokacin da ta kaika ta baro zaka san cewa kana aikata kuskure.
Duk abubuwan da kake ji haka itama Maryam ta ji sa a baya, amma ka kasa tausaya mata, ka rufe idanuwanka ka wulaƙanta ta batare da tausayi ko rangwanta mata a matsayin ta na yarinya ƙarama ba, ka kasa fahimtar zuciyarta da Allah ya ɗaura mata ciwon son ka, tayi haukan tayi kukan duk don soyayyar da take maka, ta juri kowacce wulaƙanci naka; amma...." Sai yayi shiru yana jan numfashi tare da kallon fuskar SHAREEF ɗin, sai ya kaɗa kansa da cewan, "i know har da alhakin ta Bro, a tunanina Allah ya ɗaura maka don kaima ka ɗanɗana abun da wasu suke ji in aka kasa tausaya musu don sun faɗa irin wannan ƙaddaran; wanda basu suke ɗaurawa kansu ba, don Allah ko ya ya ne ka saka wa kanka tausayin mutane SHAREEF, ka damu da damuwar waɗanda suka damu da kai."

Shiru SHAREEF yayi ya kasa magana, domin ba ƙaramin ɗaure sa da jijiyoyin jikinsa yayi ba, wanda yasa ko idanunsa ya kasa ɗagowa bare ya kalle sa ko ya furta abun da ke ransa

Sai Hanif ɗin ya dafa mishi kafaɗa gami da faɗin, "shawaran da zan baka a matsayina na ɗan uwanka; kuma in CeCe ka a wannan halin da kake ciki; na farko shine addu'a, ka roƙi Allah ya cire maka soyayyar Haseena, domin baza ka taɓa samun wannan farin cikin da kake biɗa a wurin ta ba, sannan..." Sai yayi shiru yana tunanin ta inda zai faɗa mishi abun da ke ransa,
Haka nan ya daure ya ci gaba da maganar, "duk da na san ba ka ƙaunar Maryam, amma har yanzu ita Matarka ce, na san a ranka kana wannan saƙar da baza ka taɓa zuwa wurin ta ka nemi buƙata ba, shiyasa kake zaune cikin wannan halin, Ni zan taimaka maka."
HaÉ—a idanu suka yi da SHAREEF É—in, sai yayi mishi murmushi da É—aga kai tare da sake faÉ—in, "akwai wani shawara, mai zai hana ka neme ta batare da sanin ta ba. I mean koda maganin barci ne ka sanya mata hakan zai taimaka maka ka fita a wannan halin da kake ciki, Ni É—an uwanka ne bazan so abun da zai cutar da kai ba, i will help you a kowanne hali kake ciki. This is the best solution we have".
[13/04, 7:34 PM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE18*
_____Abun mamakin sam SHAREEF bai musa daga shawarar da Hanif ya ba shi ba, domin a ganin sa wannan hanyar ne kaɗai ya rage mishi wajen samun sauƙi daga damuwar da yake ciki, sannan ma da biyu ya amince; ko don ya koya wa Maryamu hankali ya hukunta ta, dama ai ta taɓa mishi sharri makamancin haka, yanzu zai tabbatar mata da gaskiyar al'amarin, lallai bata san waye shi ba

Yayinda Hanif ya ji daɗin yanda SHAREEF ya fahimce sa; domin bai taɓa tunanin hakan ba ko don furucin sa na baya, shi kuma a ganinsa hanya ce mai sauƙi da SHAREEF zai soma son Maryamu tunda har irin wannan abun mai girma zai shiga tsakanin su, tabbas yanzu an samu sauyi tunda har ya amince zai iya kusantan Maryamu, lallai Kura tayi lafiya, to abu mai sauƙi ne ya kamu da soyayyarta, ya ji dad'i sosai,
Shiyasa yace mishi, "zuwa gobe sai su siya maganin barci su saka mata, ya san plan É—in da zai yi har ta sha."

Da haka suka bar zancen, amma sam SHAREEF ya kasa runtsawa a wannan daren, abu biyu ke damunsa, yanda Haseena ta juya masa baya; da kuma surar Maryamu da ke mishi gizau yana ƙara jin kwaɗayin kasancewa da ita. in takaice muku har mafarkin ta SHAREEF yayi a wannan ranan, sabida ya sa abun a ransa,
Allah -Allah yake yi goben yayi ya gansa tare da ita yana biya wa kansa buƙata ko zai samu sukuni daga gangan jikinsa

A washe gari haka suka wuce Office tare da Hanif, yau ma sai da ya biya ta hospital aka yi mishi ƙarison alluran nasa, tare da Hanif suka je sannan suka wuce wurin aiki

After sun tashi wurin ƙarfe biyar da rabi, don yau sun jima a companin sabida wasu ƴan gyare-gyare da ake yi, ga meeting da suka yi a ƙurarren lokaci, dalilin da yasa suka kai wannan lokacin kenan

A hanya da zasu dawo Hanif ya faÉ—a masa, "zai tsaya su siya yoghurt, sabida a ciki za a sanya mata maganin barcin, shi zai san yanda zai yi ta sha Insha Allahu."

Bayan sun tsaya sun siya, suka ƙarisa wani Pharmacy suka siya maganin sannan suka wuce gida

Har a ran SHAREEF wani dad'i yake bijiro masa ya rasa daga ina yake jin wannan farin cikin, abun da zai iya cewa kawai don yau zai kawar da kwaɗayin sa ne, shiyasa maybe yake jin farin ciki a ƙasan zuciyarsa, tunda sam bai damu da Maryamu ba sannan ba ya jin ta a rai kamar yanda yake kwaɗayin jikinta, gaskiya tana da dirin da babu ƙarya ta saka shi a wani yanayi, bai taɓa tunanin haka yarinyar take da kyakkyawar sura ba, ko kuma don ta ƙara girma ne? Haka yake ta tunani a ransa yana son ya ƙara tozali da ita,
Amma koda suka koma bai same ta a gida ba, sai baza idanu yake yi ko zai ganta, in fact ma a falon ya zauna koda suka dawo yana son ya ga gibtawar ta, amma bai ganta ba, kuma babu damar tambaya

Yayinda Maryamu kuwa yau a gidan su Feena ta wuni, takai mata ziyara, tunda tun dawowarta Hutu bata je ba, su kansu basu san ta dawo nan Hutu ba, sai yau da ta je tayi mata wuni, daga nan suka tafi gidan su Amina a tare

Sai yanzu ne Momy ta aiki Sadiq ya je ya dauko ta, lokacin ya fita kenan su SHAREEF suka dawo gidan

Sai bayan magriba suka shigo shi da Maryamun,
Dayake suna shiga aka kira sallan isha'i that's why Sadiq ya wuce masjid, itama Maryamu ta shiga dakinta ta gabatar da Sallah, bayan ta idar ta shiga tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigan material mai sauƙin nauyi kalan dack brown da design ɗin flowers masu kalan ja, rigan A. Shape ne mai aljihu da dogon hannu an sanya robber a ƙarshen, sai ta saka hula a kanta ta rufe tulin gashinta, takalmi kawai ta zura ta fita Falon suka zauna da Momy suna kallo, while tana bama Momy labarin fitan da tayi tunda ta tambaye ta

Sai da aka idar da Sallah sannan su Dady suka shigo gidan gaba É—aya,
Sai lokacin SHAREEF ya hangi Maryamu idanunsa a kanta ya kasa ɗauke kai yana sake ƙare mata kallo, a ransa har ya hango abun da zai wakana a tsakanin su

Ko kusa bata kalli inda yake ba balle ta nuna Allah yayi ruwan tsakin sa a wurin, harkan gabanta kawai take yi, bata san ma sanda ya bar wurin ya wuce É—aki yin wanka ba,
Suna zaune da su Hanif suna hira sai dariya suke yi,
Sai daga baya ne suka tashi suka ci abinci a saman dining, after sun gama suka dawo Falo suna ɗan taɓa hira,
Tun lokacin Maryamu ta soma jin barci tunda ba ta jimirin jima wa yin hira, in har ka ga ta tsaya hira to ta sha barci da rana ne, wanda kuma hakan ba sabon ta bane zai yi wuya Maryamu tayi barcin rana in har lafiyarta ƙalau,
Suna cikin duba waya ita da Sadiq, yana nuna mata wasu abubuwan da bata gane ba a sabuwar wayanta,
Har ta soma gyangyaÉ—i sai kuma tace mishi, "ya bari zuwa gobe sai su ci gaba."
Bayan ya bata wayan tayi musu sallama ta wuce É—aki

Momy na sake gargaÉ—an ta, "kar ta kwanta bata yi addu'a ba."
Domin koyaushe sai ta tuna mata in har zata tafi daki sai ta sake gargaÉ—in ta

Ta amsa mata da, "to." Tana wucewa
Chapter 35 · 0% Book details