← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 75

Sashe 75

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hakan kuwa aka yi aka mayar da Maryamu gida a cikin wannan halin, ga rashin da suka yi ga kuma fama da ciwon Maryamu

Kasancewar an sanar da Iyayenta abun da ke faruwa, ga kuma rasuwar da aka yi, shiyasa suka taho yin musu ta'aziyya, su bakwai suka taho, da Iya Samira da Inna da Umma Jummai, sai Baba da Yaya Faisal da su Yaya Ashiru, a ranan zasu koma su Yaya Naziru, while su Iya Samira zasu É—an kwana biyu su ga halin da ake ciki

Shima a daren aka sallami Hanif ya dawo gida, sai dai jikin nasa babu dad'i tunda a halin da yake ciki na fama da tunani da rashin da aka yi masa, a koyaushe sai dai ka same shi yana hawaye, ya kasa jure rashin da yayi abun ya taɓa shi ba kaɗan ba, kuka yake yi sosai yana mata addu'a a zuciya, har lokacin ya kasa saka wani abu a bakin sa; duk da rarrashin da Iyayensa suke masa, sai dai ruwa da yake jiƙa maƙoshin sa, ƙarshe a gidan su Momy yake kwana tunda bazai iya kwana a gidan shi ba, hakan na tuna masa da mutuwar Amra.

While an ci gaba da nema wa Maryamu magani, cikin hukuncin Allah wajen wata biyu kenan da faruwar abun, aka samu ta haihu lafiya a gida, wanda hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanya su ba, ta haifi ɗiyarta Mace sak SHAREEF

Sai yaran suka zamo tamkar tagwaye da ɗan wurin Hanif, tunda shima yaron sak mahaifinsa ne, yana gidan su Hanif kasancewar ya ƙi yarda a jirga mishi da ɗan, soyayyar da yake yi wa yaron bazai yarda ya kwana a wani waje batare da shi ba, don haka Momy take kula dashi suma suna matuƙar kaunar Yaron, wanda ya ci sunan Mahaifin Amra, wato Abubakar, suna kiransa da Sadiq

Saboda wannan sunan da aka saka sai da Sadiq ya zauna ya daÉ—e a gida bai koma England ba, tunda tun rasuwar shima ya zo, to sai bai tafi ba tunda ya ji an yi masa takwara sunan su É—aya da Yaron, son duniya sun É—aura wa Yaron abun tausayi

Ga kuma jaririyar Maryamu wacce itama tubarakallah lukuceciya da ita, duk wahalar da ta sha babu abun da ya same ta lafiya lau aka haife ta, sai dai Uwar ce ma da take jinya tunda jikin babu dad'i,
Kowa aka faɗa masa haihuwar yayi murna matuƙa,
Ƴan Zaria duk sun zo suna ranan suna, yarinyar sunan Amra aka mayar, hakan ya faranta ran kowa.
*****

_____  *Bayan wasu lokuta*
Izuwa yanzu Hanif ya fauwala wa Allah lamurran sa, yau da gobe yasa ya ɗauki hakuri da dangana ya saka wa ransa, tun yana jin bazai iya manta wa da Amra ba, ga shi yanzu komai ya soma wuce wa ya zama normal, a sanadin haka har ya amince da wasiyyar da Amra ta bar mishi kuma ya ɗauki alkawarin sai ya cika mata, koda kuwa babu son Afra a ransa ne, bare kuma babu yanda za a yi ya ƙi jinin Amra, soyayyar da yake mata yana yi wa kowa nata irin sa, in har jinin Amra ne bazai taɓa ƙyamatar su ba, kuma bare Afra tana kama da Amran sosai, don haka ya nuna ƙudirinsa ya bayyana wa iyayensa wasiyyar da Amra ta bayar

Babu wanda yakai su farin ciki gaskiya, musamman yanda suka ga Hanif ɗin; shi da kansa ya kawo zancen, alamun dai yana son ya cika mata wasiyyar ta ne, zasu fi so yayi auren gaskiya a halin da yake ciki yanzu, tunda ga shi lokaci ya ja kusan shekara kenan da rasuwar Amra, kuma sun yaba da tarbiyyar gidan su Amra zasu so su ƙara ƙulla alaƙa; duk da yanzu an zama ɗaya

Suma a fannin su Mama babu wata matsalar gaskiya, don a lokacin Afra ta gama secondary school ɗin ta har tayi apply zata shiga nan BUK, kuma Dady da kansa ya biya mata tunda shi ya ɗauki ragamar karatun su yanzu, tuni ya ƙwace ladan a wurin Hanif, tunda ada shi ya soma biya musu,
Afra abun ya zo mata a baƙon yanayi, wai Mijin ƴar uwanta yanzu shi ne zai zama Mijinta, abun da bata taɓa tunanin sa ba sai ga shi Allah ya sauya komai, gaskiya baza ta ce ba ta sonsa ba bare biyayyan iyaye kawai zata yi, amma har ranta sai ta ji kamar bata kyauta ba, sai dai kuma Hanif ba irin Mazajen da ake sake da damar samun su bane, ko tana sonshi ko ba ta sonshi baza ta taɓa watsa musu ƙasa a ido ba, bare kuma an ce wasiyyar Yayarta ce, tayi kuka sosai a wannan lokacin da aka faɗa mata, daga ranan sai kuma damuwa ya shige ta koyaushe tana kuka da tuna ƴar uwanta, rashin ta ya dawo mata sabo,
Bare da damuwar haÉ—in auren; wanda ba a fi sati Uku ba aka É—aura musu aure ta tare a É—akin auren ta, inda Amra ta zauna

Rayuwa kenan! Juyi -juyi, abun da baka taɓa tunani ba sai ka ga shi ya faru, ga Afra da Hanif a matsayin Miji da Mata komai ya sauya

A fannin Maryamu ma yanzu komai alhamdulillah za a iya cewa, don lafiya ta samu har ta zana jarabawar ta da kanta yanzu haka ta soma zuwa makaranta

Sai ya zamana class É—in su É—aya da Afra, tunda itama ana auren ta soma karatun, duk da ba course É—aya ma suke karanta ba,
Yaron Amra ya dawo hannunta sabida Hanif ya ƙi yarda yayi nesa dashi, yana hannun Afra ita take kula dashi, kuma dashi take zuwa school, shiyasa baza ka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, hakan ne yasa Hanif yake matuƙar ji dasu daga ita har Sadiq ɗin

Ita kuma Maryamu ƴar iya, ta ƙi yarda ta je da goyo school, don ita cewa tayi, "goyo zai hana ta karatu, yadda take matuƙar ƙaunar karatu bazai yiwu ta haɗa raino da karatu ba."

SHAREEF yayi faɗan har ya gaji, haka nan ya ƙyale ta tunda yana son abun da take so, komai take so shi yake mata, don haka shi da kansa yake kula da Yarinyar idan yana gida, idan kuma yana da aiki sai ya kaita school ya wuce da yarinyar wurin Momy, a can zata zauna har sai an tashe su school, sannan zata biya ta can ta ɗauke ta.

*ALHAMDULILLAH.... labarina ya zo ƙarshe daga nan da yardan Allah, abun da na faɗa dai-dai Allah ya bamu lada, kuskuren da nayi Allah ya yafe min, Allah ya bamu ikon amfana da abubuwan da na rubuta Amin.*

Bazan manta ku ba Masoyana Masoyan wannan littafin, jinjina a gare ku;
Nana Aliyu
A'isha Yaguda
A'ishatu Chindo
Zahra
Anisa
Delicious Soph
Fa'iza
Fatima Sabo
Hafsah Abdul
Hafsah Kimba
Hauwa Aliyu
Hauwa Muhammad
Hajiya Maman Khad
Jamila Ibrahim
Maman Areef
Maman Sadik
Hauwa el Khabir
Murja ce Maman
Murja Sani Abu
Nafisa Musa
Queen
Radiya
Rahama Ibrahim
Ruƙayya
Shmciyyer
Ummi
Zainabu
Sister Rukky
Fauziya
Hafsa Ahmad.
Dama wa'danda ban faɗi sunan su ba na fili dana ɓoye, Allah ya bar ƙauna, JIKAR LAWALI na gaishe ku son Fisabilillah 😘 sai mun haɗu a sabon littafina wanda zan sake shi ranan 8/6/2023. *RAYUWAR MADINA!* Ku kasance da Ni don jin dad'i da nishaɗin ku.

Please follow me on wattpad UmmuDahira,
WhatsApp only 07065334256, Nagode.

2023.
Chapter 75 · 0% Book details