← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 75

Sashe 18

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuma Mama sai ta kasa faÉ—a mata; sai ma tambayarta da ta hau yi, "tare da Hanif suke ne?"

Ta bata tabbacin hakan da sauri tana bin ta da kallo cikin tashin hankali

"Na manta ban sanar miki ba, ina son ganin sa amma na san yanzu ƙila ya tafi."

Hannu ta É—aga tana sake tambayarta abun da ke faruwa tare da faÉ—in, "mai Hanif É—in zai yi mata? Sai ta kira sa a waya."

Dakatar da ita tayi ta hana ta, tace, "ta bari ko zuwa gobe sai a kira shi."
Duk da ta so ɓoye mata abun da ke faruwa; but haka nan ta zayyane mata zuwan Baba Jafaru da rashin mutuncin da yayi, duk da haka ba dukka ta faɗa mata ba tunda sauran ƴan uwan Baban nasu sun zo suma sun ci mata mutuncin ta uwa da Uba, sun yi mata zaga-zaga, sun kuma ce, "sun bata daga yau zuwa gobe ta tattara tabar gidan nan, ta zube yaran zasu iya riƙe su, kuma zancen Amra da Jabir tunda ya nuna yana so ko bata so sai ya aure ta, ƙaryan tsiya take yi bata isa ta hana shi ƴar uwansa ba."
Shi yasa ta ɓoye mata tunda ta san Amra zata ɗaga hankalin ta yanzu ta shiga wani hali

Duk da a yanzun ma kuka ta dinga yi sai da Mama ta tsawatar mata sannan tayi shiru,
Ta faɗa mata, "babu wanda ya isa ya ƙwace mata su ko yayi musu wani abu in har tana nimfashi".
***

_____Lokacin kafin Hanif ya koma gida; Baba Jafaru da Æ´an sanda suka je gidan su suka yi sallama da mai gidan,
Mai gadi ya je ya kira Dady suka fito tare,
A nan ƴan sandan suka yi masa bayanin, "Baba Jafaru ne ya kawo musu ƙara a kan ɗansa da ya rufe mishi ɗa, yanzu haka case ɗin na hannunsu suna son su tafi da Yaron don a je a yi bincike."

Dady yayi mamakin abun da suka faÉ—a, bai san wanne É—ansa suke magana a kai ba shi yasa ya tambaye su ya faÉ—a musu cewan, "Yaran nasa su uku ne, bai san wanne suke magana a kai ba?"

Ɗaya daga cikin ƴan sandan tunda su ne suka je suka kama su Jabir, ya san Hanif sosai; kuma a yanzu Ogansu ne yace, "su zo su taho dashi tunda Baban Yaron ya kawo ƙara, gwara su kira shi a yi zama a ji dalilin abun da suka yi masa."
Shine yayi masa bayanin, "Hanif ne ya saka su suka kama ɗansa, to shi yanzu ya shigar da ƙara ne sai an amsar musu haƙƙin su."

A tunanin Dady ma SHAREEF zasu ce tunda shine ya fi zaton za a iya wannan rigiman dashi, bai taɓa kawo Hanif bane, but jin hakan sai yace musu, "yanzu Hanif ba ya nan yana wurin aiki, amma zasu iya tafiya tare don ya ji ainihin abun da ake tuhumar ɗansa dashi, da kuma dalilin kama wa mutumin ɗansa."
Tunda hankalin sa ya tashi gaskiya shiyasa ya nuna zai bi su kawai, in da hali shi ya kashe case É—in

Baba Jafaru bai so hakan ba, ya so Hanif ɗin za a wuce dashi, baƙin cikin sa ma da ya ga ɗan masu kuɗi ne tunda babu wanda bai san Alh. Ahmad Sama'ila a wannan garin ba, sunan shi yayi fice gaskiya, yana ɗaya daga cikin masu kuɗin Garin Kano, wanda ko baka sanshi ba zaka ji sunan shi a baki in ana faɗan masu hali, ko kuma ka samu taimakon da yake yi wa jama'a ko baka sanshi a fuska ba,
Shiyasa Baba Jafaru bai so ba don ya san za a iya tauye musu haƙƙi tunda da ɗan masu kuɗi zai ja zancen, amma duk da haka bai karaya ba haka suka tafi a ransa yana shirya kitimurmuran da zai yi a station din, dole sai an hukunta su har su Amran, a kan ɗansa ba abun da bazai yi ba

Su Momy da suke Falo sun ji shiru bai dawo ba daga yin sallama, ga shi har ƙaran Mota suka ji ya ɗauka ya fita,
Shi yasa hankalin Momy bai kwanta ba since mai gadin tun farko ya faÉ—a musu Æ´an sanda ne,
Waya ta É—auka ta kira Dadyn tana tambayarsa,
Shine ya faÉ—a mata abun da ke faruwa,
Dalilin da yasa gaba É—ayan su hankalin su ya tashi har SHAREEF da ke kwance saman three seater, duk abun nan bai yi motsi ba idanunsa a rufe yana faman tunanin da ya zame mishi jiki,
Kyakkyawar fuskar nan nasa har ta rame ta faɗa kamar ba shi ba, ga ƙasumba da ya ajiye yayi yawa duk ya sauya mishi kamanni sabida rashin gyara, a kwanakin nan sam ba ya jin dad'in jikinsa, ko karsashi ba shi dashi shiyasa yau da ya tashi da ciwon kai ya ƙi zuwa wurin aikin, duk da har ya shirya zai je amma ya haƙura da zuwa,
Daga shi sai short trouser da farin singlet a jikinsa,
Jin abun da ke faruwa shine ya tashi zaune yana tambayar Momy madaidaitan idanunsa duk sun shige sun sake fari fat kamar madara

Tana cikin sanar mishi ne Hanif ya shigo gidan

Shi kansa SHAREEF yayi mamakin cewa da aka yi wai Hanif ne aka zo tafiya dashi,
Yana shigowa kuwa tun kafin kowa yayi magana shi ya fara mishi magana, ba tare da ya bari an amsa mishi sallaman nasa ba, yace, "Hanif wai meke faruwa ne? Mai ka yi wa Æ´an sanda suka zo tafiya da kai?"

"Ƴan sanda kuma?" Hanif yayi maganar cikin mamaki sabida har ga Allah ya manta abun da ya faru da safen

Momy tace, "eh mana, yanzu suka tafi da Dadyn ku a kan sun zo tafiya da kai, shine ya bi su don ya ji ba'asi.."

Shiru yayi da mamaki kwance a kan fuskarsa har yanzu, sai kuma cikin lokaci abun da ya faru ya faÉ—o masa yace, "oh! Na tuna, to ai Ni ne na saka aka kama min wani É—azu da safe..."

Saurin katse sa Momy tayi tace, "a kan me to? Mai yayi maka Hanif; Kai da baka da rigima kuma?"

Zama yayi gefen Sadiq yana ajiye Jakarsa tare da faÉ—in, "Momy wasu ya so cin musu zarafi shine dalilin da yasa na É—auki mataki, domin Yaron irin waÉ—annan Æ´an iskan nan ne Æ´an shaye-shaye, don haka zan wuce can kawai in ji abun da ke faruwa."

Cikin rashin jin dadi Mom ta dube sa da cewa, "to ina ruwanka Hanif? Meyasa zaka shiga abun da bai shafe ka ba?"

"Mom na san baza ki hana Ni aikin alkhairi kamar wannan ba, sannan ma yarinyar na santa tunda a karkashina take aiki, su marayu ne suna bukatar taimako, har cikin gidan su yake shiga yana cin musu zarafi, kuma yana son ya lalata musu yarinya, gaskiya bazan iya bari ba koda ban sansu ba bare akwai alaƙa a tsakanin mu."

Jikin Momy yayi sanyi, sai tace, "haka ne, gaskiya ka kyauta da ka taimaka musu, amma tunda ka fi sanin abun da ke faruwa yakamata ka bi Dadyn ku tunda kai aka zo É—auka, inyaso sai ku san mai ke faruwa."

"Haka ne Mom bari in je."
Yayi maganar yana miƙe wa da sauri

SHAREEF shima miƙewa yayi yace, "jira Ni bari mu wuce tare."
Sai ya juya ya koma upstairs ya je ya saka kaya, riga da wando ne ƙananu, sai ya saka ƙaton cumbas a ƙafafunsa kalan blue t.shirt ɗin da ke jikinsa,
Sauko wa suka yi suka wuce a tare, duk da Sadiq ya so bin su amma Hanif ya hana shi.
[31/03, 4:33 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE10*
_____When Hanif arrived at the police station, they found them in the DPO office,
Lokacin an je fito da su Jabir kamar yanda DPO ya bada umarnin a kawo su don a yi komai a gaban kowa,
Yana cikin tambayar Dady zuwan Hanif É—in,
A lokacin sai ga su sun zo station din, wani Constable ya shigo yana sanar da DPO, shine ya bada umarnin a shigo da su

A tare suka shigo cikin office É—in, Hanif na gaba SHAREEF na biye dashi a baya,
Bayan sun gaisa DPO yace, "su zauna."
Ya nuna musu wurin zama kafin daga bisani yace, "yanzu dai ga kowa ya hallara tunda ga wanda muke nema nan, amma duk da haka sai an kira Mahaifiyar yarinyar da ita kanta yarinyar sun zo nan sannan a tattauna abun da ke faruwa, Alh. Ahmad don da kai a cikin zancen nan shiyasa gwara a nemi maslaha mu ji ta inda matsalar take, hakan zai fi."

Dady yace, "gaskiya ne DPO, to ina ga za a iya kiran su ai babu damuwa."

Kafin DPO yayi magana ma; Hanif yace, "zai je ya taho dasu in babu damuwa."

DPO ya ba shi dama sannan ya tashi ya tafi.
***

_____Almost fifteen minutes sai ga Hanif ya dawo tare da Mama da Amra,
A tare suka shigo suna biye dashi a baya
Chapter 18 · 0% Book details