Sashe 17
Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
She never thought she would hear these words from him, that's why she was confused at the same time, cike da tsoro da mamakin sa take kallonsa, tana ganin bata kai matsayin da kamar Hanif zai tsaya a gabanta yana furta mata kalman so ba, to mai zata ce mishi? Wannan tambayar shiyasa ta kasa kataɓus kanta a ƙasa jikinta na rawa; matsananciyar kunya ta kama ta
Shi kuma Hanif ya kasa jure shirun ta burin sa kawai ya ji amsar sa a gunta, don haka ya ci gaba da tausasa murya yana gaya mata irin ƙaunar da yake mata, kuma amsar ta kawai yake buƙatar ji a yanzu
A yanda ya nuna damuwarsa da kalallametan da yake yi; ta rasa abun yi a wurin, ga kunya ga mamakin kalaman nasa da bata taɓa tunanin hakan ba, tabbas baza ta ce ba ta son Hanif ba, sai dai a yadda take bata taɓa kawowa a ranta zai iya sonta ba bare har kalaman soyayya ta shiga tsakanin su, tana da wani abu, bata ɗaura wa kanta abun da ta san ya fi ƙarfin ta; duk kuwa da abun da take ji a ranta ba takai kanta inda Allah bai kaita ba,
A ganin ta Hanif ya wuce ya zo wurin ta ya ƙasƙantar da kansa domin neman soyayyarta, amma sai ga shi abun ya zo mata a bazata; a mugun bazata, wanda hakan ya saka ta a wani irin yanayi; sam ta rasa abun da yakamata tayi, ya fi ƙarfin tayi rejecting soyayyarsa, domin shi wani bango ne ko in ce rumfar da yayi musu mafaka a rayuwa, koda ba ta son sa baza ta taɓa ƙin amince masa ba, domin duk abun da ya nema a rayuwarta a shirye take tayi masa shi da iya ƙarfin ta, Hanif ba abun wulaƙanta wa bane a gare ta, bare dama ba ta ƙin sa, abu ɗaya ne ya raunata mata zuciya; sabida kasancewar ta naƙasashshiya mara galihu,
Tuni ƙwallan da suka cika mata idanun sun soma ɗiga a saman kuncin ta, tayi shiru kanta a ƙasa ta kasa kula sa bare ta dakatar dashi daga sambatun da yake yi,
Me zata yi masa ta saka mishi a rayuwa? Ta yarda cewa Hanif yana sonta; ta yarda da iya gaskiyarsa yake faÉ—a mata waÉ—annan kalaman, tabbas abun farin ciki ne a gare ta a ce kamar Hanif yana sonta, amma ba ita ya dace ya nema ba,
Don haka sai ta ɗago kanta da sauri tana kallonsa, bakinta na rawa kamar zata yi magana amma ina ta gaza yi sabida ko tayi yunkurin yi sautin muryanta bazai taɓa fita ba
Hankalin sa ya tashi da ya ga hawaye a saman kuncin ta,
Before yayi magana sai ya ga ta tashi da sauri tana shirin fice wa,
Take shima ya tashi ya mara mata baya yana shan gabanta, tare da kallonta cikin tsananin damuwa da ruÉ—un da ke barazanar tarwatsa mishi zuciya, don yanda ya ga hawaye a idanunta hakan ya saka mishi wasi-wasin rashin amincewar ta dashi,
Shi yasa babu zato babu tsammani ta ga ya duƙa mata a gabanta yana rokon ta da faɗin, "don Allah Amrah ki bani amsar tambayana kar kibar wurin nan batare da kin amince dani ba, yanayin da na ganki ya saka min shakku a zuciyata, ko ba ki yarda da soyayyar da na furta miki bane? Kina ganin kamar ƙarya ne ko?"
Girgiza kanta ta soma yi jikinta na rawa sabida ganin yanda ya duƙa mata, da sauri ta duƙa itama tana ƙoƙarin mishi bayanin, "ya tashi tsaye ba ta son ganin sa a haka."
Hannunsa ya sanya yana ciro wayansa cikin aljihu da sauri, tare da miƙa mata yace, "ki min bayani a nan."
Miƙa hannu tayi ta amshi wayan ta soma yin typing hannunta na rawa, duk alamun ruɗe wa ya bayyana a tare da ita,
Tana gama wa ta miƙa masa wayan
Shi kuma ya karanta ya gani before ya dube ta yace, "no bazan tashi ba har sai kin bani amsar tambayata, ina son in duƙa miki ne sabida ki amince dani, domin a yanzu nayi nisa da dakon soyayyarki ba na jin zan iya jure rashin ki."
Hannu ta sa ta amshi wayan ta sake rubuta mishi, "ta yarda ya tashi zasu yi magana."
Ganin abun da ta rubuta, shiyasa ya miƙe, itama yace, "ta taso su zauna."
Babu yadda ta iya dole ta koma wurin zaman ta tana duƙar da kanta ta kasa cewa uffan, sabida jiran da yake yi tayi masa magana, wayansa na hannunta yana sauraron abun da zata rubuta mishi,
Sai da ya sake mata magana before ta soma rubutun a tsanake zuciyarta na tsintsinke wa
"Yaya Hanif, ba abun da zan iya saka maka dashi a duniyar nan ko me na baka, ko mai ka nema a gare Ni a shirye nake da in baka shi hannu bibbiyu ina mai farin ciki in bar bai saɓa wa mahaliccin mu ba, sai dai abun da ka nema a wurina a yanzu yayi ƙanƙantar da zan iya baka shi, kasancewata ina da wata tawaya da bazan iya baka farin cikin da kake so ba, ba Ni ya dace ka so ba, amma tunda ka buƙata a gare Ni zan baka ƙanwata Afra, zata fi dace wa da kai fiye da Ni, duk da haka gani nake yi ban kyautata maka ba domin ka wuce haka a gare mu, kayi haƙuri ka amshi Afra ƙanwata domin ita tana yin magana, bata da tawaya kamar Ni, baka dace da Ni ba, baza ka taɓa dacewa da Ni ba har abada, ba na son wata matsala a nan gaba."
Shiru tayi tana kallon rubutun hawayenta na É—iga a saman wayan,
Lumshe idanunta tayi before ta ɗago ta miƙa masa wayan, sai da ya amsa sannan ta saka hannu ta soma share hawayen tana mai duƙar da kanta zuciyarta na mata wani irin ƙuncin da ta kasa gane dalili
Shi kuma da ya gama karanta wa sai ya ɗago yana duban ta, fuskarsa ba walwala yace, "ba ita nake so ba ke nake so Amrah, idan har kin san cewa na wuce neman abu a wurin ki ban samu ba, to ki amince da soyayyata domin shine kaɗai abun da za kiyi ki faranta min, Ni na san ƙaddara kuma na san da cewan ke Kurma ce amma a haka nake sonki, ina sonki Amrah! Ke nake so ba wata ba, do you love me? you can marry me? Amsar ki nake buƙata yanzu."
Ido ta zuba mishi, a wannan lokacin ta kasa ɗauke idanunta daga cikin nasa, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjin ta, wani irin ƙauna da zallan soyayyarsa ne ke mamaye a cikin zuciyarta, baza ta iya ce masa a'a ba, shiyasa a hankali ta gyaɗa mishi kanta alamun amince wa, yayinda tayi ƙoƙarin miƙe wa tabar wurin da sauri,
Sai ta ji saukar muryansa cikin sautin dariyansa da ya bayyana farin cikin sa
"I love You so much! I really love you!
Thank you for trusting me. You are the only one in my heart, I love you My Amrah!"
Kasa haƙura tayi lokacin da ta isa bakin ƙofan ta buɗe, sai da ta waiga ta kalle sa tayi masa murmushi; murmushin da ya sanyaya masa zuciya, before ta fice da sauri; itama tana jin farin ciki a zuciyarta wanda ta rasa daga inda yake fitowa
Secretary da ya É—ago yana duban ta, mamaki yayi sabida ganin yanda ta fito da farin ciki amma kuma face É—in ta É—auke da hawaye, abun ya É—aure masa kai shiyasa ya tambaye ta abun da ke faruwa?
Amma sai Amra ta nuna masa babu komai ta kasa sanar mishi abun da ke faruwa,
Sai ma ƙoƙarin kawar da tambayoyin da yake jero mata tayi, ta ƙi basa fuska ta mayar da hankalin ta kan aikin ta
Dole shima ya hakura da jin ƙwaƙwaf tunda bazai samu abun da yake so ba, amma yana ji a jikinsa akwai abun da ke faruwa, ya daɗe yana mamakin yanda ta fito cikin office ɗin, time to time sai ya ɗago ya kalle ta yana sake mamaki da ganin yanda take murmushi ita kaɗai; kuma babu natsuwa a tare da ita, kamar ma bata a cikin tunanin ta sabida hannunta na kan computer tana latsa wa amma idanunta da hankalin ta ba sa kai.
***
_____Ƙarfe biyar kamar yanda suka saba tashi, yau ma a haka suka tashi,
Motansa Amra ta hau suka wuce, duk da bata so bin sa ba amma bata da yadda zata yi; baza ta iya zille masa ba
A cikin Motan ma wani irin kulawa ya dinga bata yana furta mata irin tarin ƙaunar da yake mata,
Duk kunya ya cika ta ta kasa sakin jikinta, rufe idanunta tayi da Hijabin ta kawai tana sauraron zantukan nasa waÉ—anda suke sanya ta nishaÉ—i da farin ciki
A hankali yake tuƙa motan har suka isa gidan su
Sabida kunya yasa Amra ta kasa tsaya wa, da sauri ta fice har da haÉ—a wa da gudun ta tabi lungun gidan su,
Bata juya ba har ta shige cikin zauren gidan before ta dakata tana sauke numfashi, yayinda ta sanya hannu a kan ƙirjin ta tana jin yanda yake buga wa da ƙarfi,
Yau tana cikin farin ciki, ina zata saka wannan farin cikin? Haƙiƙa yau Allah yayi mata kyautar da babu kamar ta a tarihin rayuwarta, Hanif tamkar haske ne a tare da ita, samun Hanif a matsayin Masoyinta tana ji a jikinta tabbas zata yi farin ciki, yana da kirki matuƙa, ta tabbata bazai taɓa wulaƙanta ta ba,
Sai da ta jima a wajen before ta sanya kai ta shiga gidan,
Sai dai lokaci É—aya farin cikin nata ya gushe da ta tabbatar da abin da ke faruwa a gidan,
Domin a cikin wani hali ta zo ta tarar da Mahaifiyarta duk da su Salma sun tafi Islamiyya,
Damuwar da ta gani a tattare da ita har da hawaye shi ya É—aga mata hankali, nan da nan ta tashi hankalin ta ta soma tambayarta abun da ke faruwa