← Book details Shareef Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 75

Sashe 63

Shareef Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah da ikonsa sai Maryamu ta buÉ—e idanunta ta sauke akan Kunaman nan, ko kafin takai mata saran tuni ta faÉ—o tim a saman gadon,
A haukace ta miƙe zata bar ɗakin batare da ta san inda hankalin ta ke jikinta ba, sai dai kamar ana ingiza ta ne zuwa Kofar fita

Yayinda Kunamar tuni ta bi bayanta ko kafin ta fita ta ɗana mata ƙarin ta a ƙafa

Ihu ta yanka ta faɗi a nan ƙasa tana shure-shure idanunta sun sake fitowa waje kamar an zuba musu barkono,
Haka Kunaman nan ta sake samun dama ta sakar mata wani ƙarin daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba, kamar an yi ruwa an ɗauke numfashin ta ya ɗauke daga gangan jikinta

Ƙara Kunaman ta saka mai kama dana Mutum, daga nan kuma ta ɓace ɓat sai ga ta ta rikiɗe ta koma Haseena tana ɓaɓɓaka dariya sabida farin cikin samun nasaran kashe Maryamu,
Shikenan matsalarta takau

Da sauri Nana ta rungume ta tana tambayarta yanda tayi ta kashe Maryamun?

Cikin farin ciki Haseena ta bata labarin komai tana dariya, sai tace, "yanzu Burina ya kusa cika, na tabbata duk taurin kan SHAREEF sai ya dawo gare Ni, domin a yanzu haka ma aikin mu ya fara tasiri fiye da koyaushe yana nan zuwa nan gidan."

Ko kafin ta dire maganarta sai suka soma jin hayaniya kamar na muryan Abba a waje

Jin abun da yake faɗa shine dalilin da yasa Haseena ta miƙe ta duba window, ta hange sa tsaye tare da SHAREEF yana ci masa mutunci sabida ganin sa a gidan sa; after ya sakar masa ƴarsa,
Da sauri ta fice a É—akin ta fita wajen,
"Abba." Ta kisa sunan sa da sauri tana ƙarisa wa inda suke

While Nana tana tsaye a bakin ƙofan tana kallon abun da ke faruwa

Kai tsaye wurin ta ƙarisa batare da kunyar Abba ba ta rungume shi cikin tsantsan farin ciki

Shi kuma kamar soko haka ya tsaya sai ma farin cikin da ya ji yana ziyartan sa sakamakon tozali da ita da yayi, nan da nan ya sanya hannu ya sake manna ta a jikinsa

Abba da baki a sake ya bi su da kallo kamar ya samu TV, sai kuma yace, "Haseena, mene ne haka kike yi? A gabana kike rungumar wanda ba Mijinki ba?"

ÆŠago kai tayi tana duban Abban, sai tace, "Abba wa yace maka ba Mijina bane shi? I love him so much, ka bari zamu tattauna dashi and I will tell you everything, please give us another chance."

Shiru Abba yayi, but sai da yayi wa SHAREEF wani kallo before yace, "okay, amma ki kula daughter."
Daga haka ya juya yabar wurin ya shige cikin gidan

Ita kuma sai tayi ɗage ta sumbace shi saboda rashin takalma a ƙafanta, daga nan ta ja hannunsa tace, "mu shiga ciki."

Haka ya bi ta kamar jela babu musu a ransa, amma kuma yana tunanin abun da ya aikata anya ya dace kuwa? Mai zai sa ya ji yana sonta a yanzu after sun rabu? Mai ke shirin faruwa dashi ne?

Cikin falon suka shiga suka zauna a saman two sitter, inda ta manne dashi tana ɗaura kanta a kafaɗansa sabida kewarsa da tayi, yayinda take jin soyayyarsa na ƙara tasiri a zuciyarta, tabbas baza ta iya barin ma wata ɗiya Mace shi ba, ya rigada ya koyar da ita Zumar soyayyarsa, SHAREEF ba irin Mazan nan bane da ake samu cikin sauƙi ba, ire-iren su cikin ƙasar nan namu suna da ƙaranci, komai ya haɗa wanda ɗiya Mace mai ji da kanta zata mutu a ƙaunarsa,
Tuni ta É—ago kanta suna kallon juna, sai takai fuskarta zuwa ga nasa tana shirin haÉ—e bakin su wuri É—aya

Tuni ya buɗe nasa bakin ya shigar dashi cikin nata sun soma tsotson juna cike da shauƙin so, wani irin yanayi suka shiga gaba ɗayan su musamman yanda take mishi irin salo tana shashshafa shi kamar zata haɗiye shi, nan da nan ta ci nasaran zautar dashi ya biye mata sun zama kamar chewing gum a wurin

Tsawon lokaci suna a wannan yanayin, before su dakatar da abun da suke yi, yayinda fuskarta ke kusan nasa take shafa kafaÉ—ansa cikin salo tana faÉ—in, "dear, meyasa kayi min haka don Allah? Ka san fa ina son ka da yawa, Please ka dawo da soyayyata a cikin zuciyarka mu dawo mu kasance tare, i love You so much and bazan iya rayuwa babu kai ba, Please."

Gaba ɗaya ta kashe masa jiki musamman yanda take maganar cikin tsantsan shagwaɓa da karya murya, lokaci ɗaya tayi tasiri a kansa sabida har lokacin tamkar bai san mai ke damun sa bane, don haka ba shi da wani zaɓi face ya kyautata wa zuciyarsa sabida muradin ta da take yi, nan ya buɗe baki yana bata haƙuri a kan abun da yayi mata, sannan ya ƙara da faɗin, "i love You too sweetheart, idan kin yarda zan mayar da ke dakina domin mu kasance tare, I will give you everything you want but now I need you in my life."

DaÉ—i ne kamar ya kashe ta sabida ganin ta ci nasara, "But if you love me, can you give me everything I need?"

"Yes, Whatever you want, I will give it to you, ki faÉ—a whatever you want."

Cikin kissa da karya murya tana ƙara danna mishi ƙirjinta tare da goga mishi cikin salo take cewa, "but ka ce min kana da wata Matar, Ni kuma bazan iya zama da wata ba, idan kana son farin cikina domin mu kasance tare dole Ni kaɗai zaka zauna da Ni, domin Ni kaɗai na cancanta da kai, dani kaɗai ka dace dear, and ina son ka bi Ni Australia mu zauna a can mu ji daɗin rayuwarmu tare, if you do this for me and finish everything for me, I will believe you very much, and I will love you more than anything in the world."

Shiru SHAREEF yayi ya kasa cewa komai sabida jin abun da tace, but ba ya tunanin zai iya yin hakan, don haka ya kasa magana yana tunani a ransa

While ita kuma sai ta tsira mishi ido tana jiran amsar shi, ta san idan ta ci galaba a kansa shikenan ya zama nata na har abada, don haka sai tayi amfani da damarta ta miƙe tace masa, "tana zuwa."
Daga nan ta tashi ta je ta amso drink É—in da suka haÉ—a domin shi, don in ya sha shikenan kuma soyayyarta zai dawo fiye da kowa a duniya, komai tace yayi zai yi mata,
Tana zuwa ta miƙa masa cikin kwarkwasa tace mishi, "ya sha kawai, koyaushe zai iya bata amsa but ba sai yanzu ba, zasu sake magana daga baya."

Haka SHAREEF ya amsa cup É—in, babu musu ya sha kamar yanda tace dashi bayan yayi Bismillah a zuciyarsa

After sun yi sallama ya tafi, yana kan mota ya kira Hanif ya tambaye sa inda zai same sa

Ya faÉ—a masa, "yanzun nan ya shiga Company."

"Ok I'm coming now."
Daga haka ya kashe wayan ya nufi Company, kai tsaye office din Hanif ya wuce ya shiga

Hanif da ya gansa yayi mamakin yanda ya ga ya sauya mishi, dalilin da yasa ya tambaye sa, "ko akwai wani abu ne?"

ÆŠan numfashi SHAREEF ya ja before yace, "Haseena. Haseena ta zo gidana, amma abun da ban faÉ—a maka ba; na sake ta tun tana can..."

Tun kafin ya ƙarisa maganar farin ciki ya nuna a kan fuskar Hanif, cikin zumuɗi yace, "what kind of happiness is this? good news." Sai dai tuni ya sauya fuska sabida jin ƙarisan zancen nasa, "What! Ka mayar da ita ka ce? And you love her now?".

*Happy juma'at Mubarakh fans and enjoy your weekends.😘 Love you.*
[08/05, 6:04 AM] نفيسة OumƊahira: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*Littafina na kuÉ—i ne, ki biya ki karanta, zaku iya samu na a kan wannan numban wayan. 07065334256.*

__________
*BOOK2*
_______________*PAGE33*
_____"And bayan ka sake ta kuma mene ne dalilin zuwan ka gidan su yau?" Yayi maganar da tsananin mamakin jin zantukan SHAREEF

Wanda shi kuma yana dafe da kansa kamar zai yi kuka yake cewa, "i don't know Hanif, and yanzu kuma ina sonta, ina son zama da ita, yanzu ta dawo rayuwata, tunanin ta a kwanakin nan ya hana Ni saƙat that's the reason da na je ganin ta, and I thought ta koma can Austria."

"Hasbinallahu wani'imal wakeel!" Hanif ya furta yana tsare sa da ido ya kasa cewa komai yana faman kallonsa, yayinda yake sauraron zantukan sa da ya dage yana ta mishi bayanin halin da yake ciki da yanda yake ji a zuciya, sai da ya gama tsab before yace, "gaskiya akwai matsala, abun nan da ɗaure kai Bro, mene ne dalilin ci gaba da sonta bayan abubuwan da tayi maka a baya? Gaskiya ban yarda da ita ba, yakamata ka ɗauki mataki tun kafin abun ya zama worst irin na baya, ka dage da addu'a Bro domin samun sauƙi daga wannan bala'in da ke shirin kunno ka, bai kamata ka ci gaba da son wannan yarinyar ba sai dai akwai abun da tayi maka ne, ka san irin su ba abun da baza su iya aikata wa ba. You better ka tashi tsaye cikin addu'a ka dage i know kana da apps cikin wayanka na azkar, ka duba ko na sihiri ne da wasu addu'o'i na miyagu kayi tayi domin tseratar da kanka."
Sai kuma ya girgiza kansa da ci gaba da faɗin, "wai tana son ka bi ta can ko? Kai wannan sheɗaniyar yarinya ce yakamata ka tashi tsaye ina faɗa maka Bro, don idan Iyayenmu suka ji abun bazai yi kyau ba." Ya ƙare maganar cikin baƙin ciki da damuwa

Yayinda har a cikin zuciyar SHAREEF ya yarda da zancen Hanif, sai ya ji dad'i a ransa sabida samun shawaransa, don haka tun a lokacin ya soma ƙoƙarin karanta addu'a; yayinda ya fitar da wayansa yana son duba applications na azkar; ko yana nan bai goge ba
Chapter 63 · 0% Book details