← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 83

Sashe 83

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Shiru ya yi na dan lokaci yana tunani a zuciyarsa
Shirunsa ba a kan komai bane sai a kan tunanin abinda ya dace ya yanke, wanda ba zata ga an tauyeta ba, ba kuma zai tauye kansa ba

Tsakani da Allah har a cikin ransa ya ji dadin da bata bi su ba, kuma dalilin wannan shima ya daga mata kafa a kan abinda ya so yi mata na rashin kyautawarta dangane da yar uwarta, sai ya daga mata kafa dan ko ba komai ta ji naganarsa duda yana hankalce da ita ba ruwanta da harkar sunnan ya'yansa sai a wunin biki kawai ta je ta zauna a gefe tana kallon mutane tana amsa waya da dane danenta
Ama duka wannan ya yi niyar a hankali zai kwatanta hada kansu , zai kwatanta hada zumunci a tsakaninsu, ba zai dira kai tsaye ya yi haka ba dan abin ne tunda farko a rikice yake, dole ya bi a hankali

A nutse ya fuskanceta ya ce" Kina ji? Risala ki yi hakuri kin ji? Idan bakya zaman nan din ne ku je gidan Hajiar baki dayanku, ama bana son maganar zuwa gidanku ki yi har sati guda dan kawai na yi tafia, a nan dinma ai ba ke kadai bace sai idan kin so zama ke kadai din, ga masu aikinki ga komai, kuma kina iya sakawa daga gidan naku kannenki su zo su tayaki zama ko?" Ya fadi nagabar kannenta ne kawai, domin ba zasu taba zaman minti goma basu yi fada ba, sam basa zaunuwa waje daya, akoy lamari na rainin junna a tsakaninsu
Risala ta yi tsai, a hankali ta ce" Ama husband, ita fa da ka barta ta tafi gidan hajia ba zabinta bane? Sai nice zaka hanna?"

ABDUL ya dafe kansa, wai dama haka ne hada biyun? Bale idan masu jinini ne? Wannan tace wannan, wancen tace wannan

A tausashensa dai ya ce" Risala, haihuwa fa ta yi, ina zata je ta yi wanka ne? Wankan jego zata yi a gidan ai, kuma kema nace idan kina son cen din ku tafi tare ko?"

Risala ta cire kanta idannuwanta na cika da kwallah
Zuciyarta na haharbawa

Muryarta a raunane ta ce" Allah ua sa dai ba bakin uwa zan gani a zamana da kai ba, du inda na bi sai ka hanna ni, ita kuma du abinda take so ka baza mata, yanzuma daga wajenta kake, kamar wanda ke sonta bayan asiri ne, babu wanda zai ji labarinku bai tabatar min da asiri ta yi ba, ta rabani da Hajia , yanzu tana son rabani da kai gaba daya, na ce ka je chaina da ni kace aa, gidanmu ka ce aa, Allah ya nuna min karshen masifar nan, dan ni da Allah na dogara!"

A hankali ABDUL ke girgiza kansa yana kallonta

Niyar bude Salak din ya fasa ya ajiye ya juyo da kyau yana fuskantarta

Da siga ta nasiha ya ce" Risala, kin san a duniya bawan da ya saka irin tunaninki ya fi kowani bawa wahala a rayuwa kuwa?, Da yawama wa'inda ke bin bokayen suke fama da irin wannan matsalar, zaki ga kullun su cikin maganar an jefe su, an masu asiri, an shiga gabansu suke domin sun ba dan kasuwa yardarsu wanda abubuwan siyarwarsa wannan buga kasar ne ya fada maka karya dan a ciki abincinsa yake, idan ya fada maka cewa lafia kake ai ba zaka dawo neman magani ba, a haka wa'inda ke fama ke fama, sai gashi kema kina irin tunanin nan?, Zan so ki ba kanki lafiya, ki cire wannan tunani a ranki, ki rungumi abinda yske gabanki, babu abinda ya kai gaskiya dadi a duniya, domin itace raminta ba kurare ba Risala, ko me zaka yi kuma gwara ai ka yi shi a kan gaskiyarka ko? Da ka yi shi a kan hasashe ko son zuciya, Risala Amina matata ce, kamar yadda kike matata, ina sonta kamar yadda nake son ki, ke da ita ba bambanci, yadda zan kare mutuncinki haka zan kare nata, ki cire tunanin an hadani da ita dan dole an min dole, ke babu wanda ya isa ya min dole fa ? Ra'ayina ce ita , kamar yadda kike ra'ayina, ki kwontar da hankalinki, ki nutsu, ki cire komai a ranki, ki fuskanci me ya dace ki gyara ko me ya dace ki daina, zaki ga mu'amalarki da kowa dake tare da ke ta daidaita, koda ba yadda kike so ba zaki ga akoy fahimta kin ji?"

Risala ta ringa daka tissu tana goge hawayenta, domin ita dukka kaf jadadawar soyayarsa wa Amina da ya yi ta dauki haka a matsayi aiki irin na sihiri!, ABDUL dinta? Haba dai, haba!,

Tana hawayen ta ce" Kennan dai ba zan je gidan namu ba, dan kana tsoron kar a lalatani ko me kake nufi ?"

ABDUL ya kureta da ido, kennan dai ba zata gane me yake nufi ba?

Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki jug din ruwa ya mike ya nufi ciki, kwata kwata ba zai ci salak din bama, Allah kuma ya shiryeta idan tanada rabon shiriya ( kina fa da dama, kina iya tankwasashi har ya yarje makin, kina iya morar kuruciyarkin, da kyanki, ama A haka, a haka ko?, kwonci tashi, tun ana sauraronki, za'a zo a daina, zai zamto da kin bude baki ba'a ba abinda ,aki fada mahinmanci, domin an san me zaki jajanta, koda bakinki na dauke da magana mai mahinmanci......dan Allah ina anfanin kashe kai da kai? Ai gwara a hakura walahi a gabatar da kishin da ya dace, ke mu fa a kishi muna iya yin burgima abinmu😂😂😂🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️ i com in peace)

Mikewa ta yi itana ta fice ranta a bace, ta sani rayuwar bambanci in dai da aikin asiri ai kadanma ta gani, yau zata yi ta kiran mamanta koda zata kwana tana yi ne dan su shirya, domin batada wanda zata kaiwa matsalarta sama da ita, a hankali zata kwatanta mata ba gida zata bita ba, aa ta tayata da Adu'a ko menene ya karye itama ABDUL dinta ya dawo nata ita daya.

_____________________________________

A gidan Baba mai shanu

A tsaye suke gaban madubi, ko nace ita tana tsaye tana saka dan kunne a kunnenta bayan ta fito daga wankan yamma ya shigo dakin nata harda murza ky

A hankali ya rungumeta ta baya , ya zamto malunmalun din jikinsa ta dan dagu ta kareta sosai a jikinsa

Kasa kasa ya ce" Zan tafi......"

Amina ta lumshe idannuwanta, wani irin abu mai girma irin na rashin son mutun ya yi nesa da ita na neman damunta

A hankali ta juyo tana dago dubanta tans kallon kyakyawar fuskarsa da cikaken sajensa
Murmushi ta yi a hankali ta dan shafa gefen fuskar tasa ta ce" Da wuri Haka Taem ruhi? ( Abincin ruhi)"

Kallonta yake yi kasa kasa, zuciyarsa na hatsiltsila.......... A hankali ya ce" Ni ne abincin ruhinki?"

Amina ta sadda kanta tana dan wasa da yan yatsunta

Murmushi ne ya subuce masa da dan gagawar magana ya ce" ki ce min na zauna..... Ni kuma ba zan ki zama ba"

Fuskarsa take ta kallo, tana yaki da son ce masa eh zauna din da zuciyarta ke ingizata
Da kyar ta iya budar baki kasa kasa ta ce" Neman na shinkafar fa?"

ABDUL ya bata fuska ya ce" Allah ba zai hannamu ba ai"

Murmushi ta yi a hankali ta shige jikinsa tana dora kanta a saman kirjinsa

Shiru ya ratsa na dan lokaci
Kasa kasa ta ce" Aa, ka je Aban Amnah, Allah ya dawo mana da kai lafiya Aban Fadeel, ai tafiya mabudin ilimi ce ko Abbansu?"

Dan makwaloton wuyansa ke sama da kasa a hankali a hankali yana sake talabo fuskarta , har sai da ya dagota yadda yake so a hankali ya shiga kissing din lips dinta

Tun sunna yi a tsaye har ya karasa bakin bed da ita ya zauna ya dorata saman cinyarsa stll yana kissing dinta

A hankali ta dan janye kasa kasa ta furta" ABDUL........"

ABDUL ya sake talabota shima cen ciki ya furta" Meenart........i ndd u"

Da kyar ta iya hannashi kaita kasa, domin du ya cire mata su dan kwalin harta da rigar, da kyar ta iya jadada masa tana hali na rashin sallah, da kyar ta iya dawo da shi a hayacinsa, hannayensa jimke da cinyoyinta ya lunshe idannuwansa kanta a saman kirjinsa, kirjin nasa na bugawa pat pat pat

Da kyar ya samu ya dawo hayacinsa, muryarsa cen ciki ya furta" Meenart?"

Amina ta ja amsar a cen cikin makoshinta

A hankali ya ce" Ki kular min da kanki, ji ringa cin abinci sosai, dubi cikinki fa ya koma ya lafe kamar ba shine bulele ba"

Yar daria ce ta kubce mata, shima ya saki murmushi yana shafa gashin kanta, a hankali ya ja numfashi a wajen gashin nata yana shakar kanshin turaran gashin sannan ya furta" Zan tafi.........."

Idannuwanta ta lumshe tana jin kamar zata yi kuka

ABDUL ya sake dagota yana kallonta, ya sakar mata murmushi ya mike yana gyagyara malunmalun dinsa da ya yakunne sannan ya dan rage tsayinsa dan ta dauko hular ne ta yi dadage ta kafa masa tana taya shi kabewa, a hankali ta ce" Allah ya tsare"

Amsata ya yi da amen, yana tafia tana biye da shi a kan dokin kofar ta tsaya tana kallo ya kama ya bude, sai kuma ya sake juyowa ya ce" I love you wife........."

Murmushi ta yi ta juya da dan sauri
Shima ya yi murmushi yana lekata har ta boye, sannan ya rufe kofar ya juyo da nufin karasawa ya yiwa Baba salama da sauran jama'ar gidan suka yi ido hudu da Baba

Wani irin kallon kurullah da Baban ke masa sai ya ji du ya dan tsargu kamar wanda ya shiga dakin matar wani jama'a

Rigarsa da ta yakune ya sake kakabewa yana dan kokarin daidaitawa har ya karaso falon ya zauna yana hade fuska danma kar a ga damarsa

Baba ya kada kai ya dan rankwafo a hankali ya ce" Ai ba zata daidaita ba sai dai ka je ka cenza wata, wannan rigar ba zata daidaita ba"

ABDUL ya kalleshi yana kankance ido ya ce" To me kake nufi?"

Baba ya dan watsa hannayensa ya ce" Aa ba komai, ama ABDUL sam bakada kunya, yaya zaka tardo yarinya har gidan iyayenta? Kai nifa sirikinka ne ko? Kar ka karra shiga dakin yata gaskiya a ringa aro kunya koda babu ita a kusa kusa"

Haba ya dafe da shegen mamakin Baban, zai bashi amsa Hajia ta fito daga kicin tana tuta abin gungurawa na yaran a hankali wanda yake dauke da abin jarirai biyu ya zamto Amna na daya , Ammar na daya sun sha wankansu kowane da abin tsotsa a bakinsa yana dab tsotsa, dan Ammar barcima yake, Ambar ce ke kallon abin wasan dake jiki yana bada kaloli da yar wakar dauke hankalin jarirai haka, gefe guda kuwa pidarsu ne da ruwa da kuma madara, domin ana hada masu da madara nonon kadai ba zai ishesu ba

Baba ya yi murmushi ya ce" ka san Hauwa kamar ita ta haifi yayan nan? Na kusa cewa jego ya karbeta "

ABDUL ya dafe goshinsa dan yau ya kula Baba ido rufe wanda zasu yi yake nema, ya dubeshi ya ce"
Chapter 83 · 0% Book details