← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 83

Sashe 4

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali suke tafia, tunda ta shigo wajen ta karanta layin abinda take nema ta dauki hanyar ta nemi shagalta da kalle kalle da mamakin kayayakin dake cike a wajen
Lalle babu ce kawai babu, harta da albasa sai da ta ga kala uku , dadawa ta kasa kasa, kai harta da atarugu gashi a kilace a wajensa, gaba daya sai ta shagalta tgana tura abin tana karanta kudin abubuwan tana dauka a hankali har ta gama siyayar ta koma zagayen kwanonin ta shiga bi tana karanta kudadensu tana zarro ido da mamakin yanzu wani fa sai ya siyi wannan kwanon mai kudin gadon budurwa na aure ya zuba abinci ko? Har ta gangaro wajen kannanun masu kannanun kudi tana karantawa tana waiga manyan ta jinjina kai tace gaskiyane, da bambanci ko a kallo, tana yi ne ba tare da ta kula da kowa ba, koda yake babu wanda ya damu da wani, daidaikun matan nema wata kan alli skin dinta a fuzge ta sake kallonta a fuzge ba tare da ta kureta da kallo ba a ranta ta ayana masha Allah, bata taba gannin black beauty mai lalausan kyau irin wannan ba, bakinta mai birgewa ne da shiga ido sosai, du kuwa irin yadda ya ciza haka yske da shiga ido da birgewa

Sai da ta dauki kwano daya da miya tana duba kudinsu gabanta ya fadi ta juyo da sauri bayanta dan son gannin yarenta
Wayam din da ta gani ya sakata sake wara idannuwanta tana dubawa cikin mutanen dake bangaren kwanonin ko sunna cikin su? Ama wayam babu su babu alamunsu

Da sauri ta juyo kurar ta shiga bin bayanta hanyar da ta biyoa hankali tana furta" Fadeel? Farid? Hasan? Husain?"
Rashin gannin alamunsu ko mai kama da su jikinta ya fara rawa, lokaci daya ta nemi rikicewa tamkar ba ita ba, bata taba jin tashin hankali irin na wannan ba bayan rasuwar iyayenta, kai ko halin da kanwarta ke ciki bai taba daga mata hankali irin wannan ba
A hanzarce ta shiga tura kurar da dan gudu gudu sannan ta kara ware muryarta tana kiran sunnayensu

Da karfi ta bangaji kurar wani mutumen da ya fito yana tura tasa kurar shima , mutumen ba yaro bane gaskiya baban mutun ne kuma kasancewar tasa kurar abinda ke ciki ba wani bane sai batirin da ya zo siya da abin gyaran gashin maza kurarsa ta kifa a wajen lokaci daya ta dafe bakinta da hannayenta ta fashe da kuka tana juyawa ta saki dayan hannun nata ta dora saman kanta da da dan karfi ta shiga fadin" Wayo na shiga uku kardai an sace min y'ayana? Wayo Allahna na shigo nan da y'ayana basa yin nisa da ni yanzu kuma basa tare da ni! Hasan? Husain!?"

Ma'aikatan da suka kwashe kayan suka riko mata kurarta ne macen ta karaso tana kamota tana fadin" Calm down Madame, y'ayanki ba zasu bace ba akoy CCTV ta ko'ina a nan mu je cen baban dakin kusa da office din oga a hasko su na tabata sunna cikin nan sunna yawonsu ki daina kuka ba'a satar yara a nan"

Ita dai bata daina kukan ba, haka kuma bata gamsu da kowa a wajen ba, da sauri take bin matar tana riko fari kal din hijab dinta da ya karra haska hasken duhun fatarta suka zo shiga wajenma abin kallo ne , watau wajen sai ka tsaya nanma an cajeka da abin nan na caje mutun sannan sai an maka daukan zafin zazabin wannan cuta ta zamani mai taken covid 19
Du ta kagauta, bata taba jin tana iya zma terrorist ba irin na yau, a cen kasan zuciyarta babu irin abinda shedan la'anane baya kitsa mata, ciki harda idan har dauke mata ya'ya aka yi ta tabata mai wajen nan ne ita kuwa da hannunta zata bankawa wajen nan wuta kowa ya kone, domin ta san wannan din ba abokin gabar gwamnati bane!

Sunna shiha wani launin kanshi da sanyin daban da na baban filin sana'ar ya buso su, ama ita Amina sam bata ji shi ba, matatakala suka kama hawa sai da suka yi hawa biyu sannan suka shiga Lift ya hauda su hawa na nawa bata sani ba ita dai ta ga an bude nan da nan sun fito
Yan tafia kadan ce suka yi yanzun suka ido mamakeken ofice din dake dauke da na'urorin da ma'aikata manya manyan masu ilimin dake kula da aiki da na'urorin wajen

Sunna shiha kunnayenta suka ringa jiyo mata muryarsa da gura gura watau Husain yana fadin" To kai Hasan tsakani da Allah kaima baka ji ya birgeka ba biscuit din cen? Kuma fa ka ga yinwar yama nake ji, ni walahi dama sauran suka bani na cinye dan na san mama zata biya idan ta zo!"

Hasan da haushi ya gama cika shi na maganar da matar dake tsayen cen ta fada a kansu cewa barayi ne su ko? Sun shigo ne da wa? Wa ya bari yara kananu suka shigo su yiwa mutane sata? Yau sai ta ga iyayensu sun biya kudin biscuit din nan gobema sa saki yara sunna masu barna a waje ya ce" Ka yiwa mutane shiru! Ba zaka ci biscuit din ba! Kai baka tunanin inda Mama take ne? "

" Fadeel" ta fada a raunane tana fashewa da wani kukan da ya fito daga zuciyarta hade da dariya tamkkar wata tabarariyar yarinya lokaci daya fuskar yaren da take boyewa ta bayana a tatare da ita ta duka kasa sosai suka zo suka fada jikinta karfin soyaya da shaukin ganninsu ya debeta yana ta rungumarsu tana kukan hadi da fadim" Ashe ba'a sace ku ba? Ashe kunna nan? Me yasa kuka fita a bayana? Ina kuka je? Wa ya kawo ku nan?"

Muryar matar ne fuskarta a hade tana tsaye cikin shiga ta sweet bakake irin uniform din du wani baban mahaukacin wajen mai dogon wando ne da farar riga daga ciki cikin yaren turanci ta waiga tana kiran wanda take gannin zai fasarawa wannan mai shige da village girl din ta ce" Wannan yaron aka kama yana satar kayan kwalam da makulashe yana budewa yana ci, irinsu ne ke zuwa su yiwa mutane barna a masana'anta, muna bukatar ki sadamu da iyayensu dan su biya barnar da ya yi sannan mu yanka masu kashedin kar su kuma zuwa da yara mararsa ji masu dauke dauke wajen nan, idan sun zo da su su tsaya iya park da su ba sai sun shigo nan ba!"

Tunda ta fara maganar take kallonta, a hankali ta juya wajen yaron da aka nuna, watau Husain yana tsaye sai turo baki yake yi, Hasan kuwa yana hararar matar kamar zai fashe dan takaici da jin haushi
A hankali kunanyenta ke jiyo mata fasarar da saurayin ke bata ama yana kiyaye mugwayan kalaman da matar ta fada kamar irin su kiran Husain da barawo da ta yi, da sauransu ya dai bata maganar a dunkule ne cewa yaron laifi ya yi ba'a bude abu a ci gashi yau oga na nan basa son abinda zai kawo hankalinsa kansu na rashin kula da wani abin

Idannuwanta ta sake zubawa mutumen a hankali ta ce" Ka tabata haka tace ka ce min?"

Sake kallonta ya yi,bama kamar lebenta dake dauke da kalar kasa kuma a kallonsuma sai kyalin laushi suke yi da fari tasss din idannuwanta masu dauke da siririn kwali zuwa hijabinta da ba zai iya fadin sunnansa ba gaskiy har zuwa takalmin dake kafarta dan soso da kuma irin na kafafuwan yaren wanda ya tabata wannan shiga ce ta saka Madame yanke mata hukuncin bata fa ilimin boko harma ta mata kallon talaka futuk da sauransu dai irin na wasu masu kudin da suka raina talaka daga kallon idannuwa suke ganne kai din su ya su ne ko kuma mu ya mu ne, ta haka zasu yanke hukuncin abinda ya dace da kai su yi maka ya sake gyada kansa zai maimaita mata matar da haushi haushi ta daki table din tana rankwafawa ta janye hannun Husain da ya juya zai dauko biscuit din ya nunawa mamansa cewa ba fa sata ya yi ba wannan ne kawai ya bude ya dauki daya shine aka kama su aka ce ina iyayensu aka yi ta nemanta wajen kayan miya ba'a ganta ba shine aka ce karya suke yi su kadai suka shigo, masu tsaron kofa suka ce aa ba su kadai suka shigo ba da mamansu ama aka ki yarda aka kawo su nan, tunda aka kawo su matar nan tale fada tana zaginsu da barayi, sai dai bata bari ya fadan ba ta ture shi da tsawa ta ce" Ka fadawa wannan bagidajiyar ta kira min uwar yaren ko ubansu na dalamesu su bani waje tun kafin sir ya leko ya ji karnin da Yaren nan suke yi da ganninsu a wajen nan ransa ya bace! Yaron nan da gani barawon anguwa ne!"
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️

*NA*

*SAJIDA NIGER*

Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida

Wannan Novel na kudi ne ba free bane

Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER

Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka

*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*

*Page 0️⃣3️⃣*

"please pull yourself together" Amina ta fada a sanyaye tana kallonta tana ta dane guguwar bacin ran da take tsoron fashewarta a irin wannan lokacin
Chapter 4 · 0% Book details