Sashe 39
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsayen da yake in ba ABDUL ba maimakun ka yi gagawar shigewa tunda ka ga mutun ya gaza dagowa sakamakon shigarsa da ka tarar a haka, sai kawai ya zubawa gashinta ido da dan kwalin yan gayun ya zame ya bar mata gashi a fili, gashin Amina ba gashi mai santsi bane irin na larabawa, gashi ne sak namu na hausawa mai tauri a ido da cika sosai, sai dai guaran da yske samu da wankin karkashi ya sa gashin nata yake da laushi idan tabawa ne, kuma yakeda tsayin gaske domin idan kitsashi ne za'a yi haka wutsiyar ke yin bardan abinta
Suraya ta ce" Aunty, indai irin kanshin nan naki nima fatata zata aura ni kam ina so, ina son humurar da turaren ruwa na zannin gado da akace kina hadawa shima kin ji Aunty?"
Jin shiru bata amsata ba ua sakata itama jan bakinta ta yi gum da tunanin ko Aminar ta koma ciki, ko kuma yan shirun sun juyo ne
Lalle Amina an dace, wannan gida haka? Lalle rayuwa Allah mai ba bawansa
Samun kansa ya yi da nufar wajen da Hijabinta ke ajiye ya dauka yana rike numfashinsa dan ya tabata warin abin nan nata ba zai bar hancinsa ya huta ba
Kawowa ya yi inda take tsugunen ya dora mata shi a kanta, hakan ya sa ta dago idannuwanta a firgice ta sauke su a saman fuskarsa
Muryarsa cen cikin makogwaronsa ya ce" Kowama zai iya riskarki da suturar nan a jikinki"
Hannunta dake cikinta a matse ta so fitarwa dan ta bashi amsa, a nan kirjinta dake daf da lekowa ya leko din ta saman rigar
Dan bakinta mai zannen na mashaya ta murguda da balagagen rashin kunyarta ta ce" To ins ruwan mutun ko a yaya aka tardo ni ne?".......
Bakinsa ya tabe shima kasan sosai ya ce" Hakane kuma, to ama na nuna maki hanya shine daidai a matsayina na..............murmushi ya saki dan dama burinsa ya ga tataciyar fitsarar, ai kuwa ya ga alamu domin an fara masa mar mar da idannu irin za'a idasa hararensa da su din nan
, Ya idasa fadin " A matsayina na jagoranki, bangonki, Uban gidanki.....kuma yayank....."
Amina ta mike tsaye dan kusancin nasu na neman zama haramun, zomin har iskar furucinsa ke shiga hancinta tsabar yana kaifin harshe , rai bace ta ce" Kai!"
Yanzunma tun daga kan nata har kasa ya sauke dubansa, sai kuma ya dan tabe baki ciki ciki sosai yace" Kwaila "
Daga haka ya juya ya kama hanyar shigewarsa ta kicin din, inda ya bar Amina idannuwanta tamkar zasu zazago daga raminsu su manu a jikinsa dan mamaki da takaicin duniya da suka sameta da yamacin nan
Har ya kusan shigewa ya dan saci kallonta ya samu kansa da sakin murmushi, sai kuma ya gimtse bakinsa a ransa yana ayana' Wai ita uwar son girma, in ba shirme ba ina hadin mace da namiji ta wannan fannin ne? Yau ko yaro dan shekara goma sha biyar da balagar ke masa kwalele sai ki ji tsoronsa bale ni, in ba dan takeki zai zamto min matsalar farin cikina ba da kafin mu saki hannun junna sai na take ki ta yadda zaki bambance waye yayan......shekarunki na sunne abin duba ba!'
Amina kam da sauri ta juya wajen suraya du a tsarge tana kallonta da son fahimtar idan bata ji ko gannin fitsarar da yaron nan ya yi mata ba
Gannin ta nutsu hayakin na hauhawarta ya sakata dantse lebenta da haushi ta dauki hijabinta ko hannun bata wanke ba ta zurmuka ta zauna a wajen zamanta abin na ciyo mata zuciya
Shin jama'a ina zata kai wannan abin bakin ciki?
Ace kannin bayanta ya dubeta ita Amina yace da ita kwaila? Shekararta da yannayin jikinta kadai ai ya girmi yara ama shii da balagagiyar rashin kunya ya kireta da kwaila? Kai , kai kafin ta bar gidan nan ko yayane sai ta dauke fuskarsa da mari , da yaa bataa takardarta wannan ne burinta na farko dan ta huce takaicin da ya guma mata na kwana da kwanaki a gidansu
*NZL PAGE2️⃣2️⃣*
Tun daga wannan rana Baba ya saka a yi masa bincike a kan lamarin yarinyar
A hankali aka ringa kwana ana tashi har ya rage kwana hudu da son turawar da ake so ya yi , ama bai ce komai ba
A kwanakin nan du wani kwontar da kai da biyaya yana samu daga Hajia, abin ba'a cewa komai domin harda Hajia a yan kicin dan yi masa yan girke girke
Idan ya sauko yakan zauna da uman biyu, da biyu, su dan zanta sai kuma ya fice rawatawarsa da datijan anguwa da abokanansa na arziki
Jikansa kan zo ziyarar kakannin nasa jifa jifa dan kuwa har tafiya ya yi ya yi kwana biyu ya dawo ita bata da labari, idan aka yi katari ya zo sun hadu ne a ajiye take sai sun taba yar tsamar da suka saba, yawanci kuma Aminar ce zata yi gaba rai bace tana gungunnin itafa bata son raini a kiyaye!, Shi kuma sai ya yi murmushi kawai ya cira kansa ya ci gaba da lamarin dake gabansa,
A haka lokaci ya sake zuwa, a daren da ya rage kwana biyu a tura mahaifin Risalah ya yi kiran Hajia ya fada mata cewa yau su Alkali sun same shi a gida shi da aminansa biyu, har sun tsayar da maganar auren komai da komai, Alkali ya nuna yana so matan su tare su biyu dukansu a gida guda? Shin Hajia dama bata ce masa auren na hadi ne Honorable din kansa baya so ba? Yarinyar dai gatacen sai murna take yi, aman mahaifiyarta ta rikice kan ba zasu zauna gida guda ba, wai ba za'a wulakanta mata y'a ba
Hajia tunda ta kashe wayar a zaunen nan da take ta kasa katabus
Hankalinta ya yi kololuwar tashi da irin hanyar kuma da mijinta ya billo mata
Shin yaya zata yi da Alkali ne?
Ita dake jiran ranar da za'a je tambayar nan ta yi gaya ta kasa da kasa manyan mutane su je tambayar nan shine kamar aurwn bazawara Alkali zai je ya yi tambayarsa a boye ya dawo? Shin me yasa Alkali yake son wulakantata a rayuwa ne a kan auren nan na Abdul? Du salon ta nuna wani abin ne ya hana auren? Ta tabata so yake ta yi wani abin kiris ya fake da shi ya ki maganar auren
Kasa fita ta yi, domin wata tsanar lamarin Aminar ya sake shiga zuciyarta, gani take yi ko menene akoy wani zagin kasa da yarinyar nan ke yi mata bata gane ba, ta yiwuma ita ta san da maganar nan bata fada mata ba!
A kasa kuwa Alkali ne da Rabi'u suke tataunawa
Da kula sosai Rabi'u ya ce" Aliyu, tunda muka je muka yi tambayar nan a haka kamar yadda ka bukata, in dai har mahaifiyar yarinyar bata watsa abin ba ka yi hakuri kawai a yi, kar ka manta jayayar kanta bata da wani anfani fa"
Baba mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Na sani Rabi'u na sani, abinda ke damuna bincike a kan yarinyar da ubanta da mahaifiyar tata kanta, lalle ba'a fada min wani tabo ko wani gigitacen al'amarin da ya gyasa yan matan zamani masu yayi selfi ba, ama magana a kan kudo da mulkin nan ya tsaye min a zuciyata, sai kuma natacen so da burin yarinyar a kan jikana na dawainiya da ni, shi yasa na yanke mu je din nan a haka dan na tabata ita da kanta ta cikin idan har ta ji to fa ko ana cen an fara raba hali ko ana jirana, ka san da har yanzu ABDUL bai nuna bukatar tarewar matarsa ba? Menene aibun uwar biyu ne ni?"
Baba Rabi'u ya yi dariya ya ce" Bata da wani aibu, kuma ai da kyauma da har yanzu take a matarsa, ita din uman biyun naka ba kai ke ce min ba uman biyu ba dai son girma ba? Aliyu mutanen nan biyu lokaci da garajensu zai shiryar da su ba tare da sun shiryawa hakan ba, ni bama na so ka saka damuwarsu a ranka, kamar yadda kace in dai sun baka amsar nan da kwana biyu sun shirya za'a daura auren nan da sati biyun to fa mu shirya mu kuma basu dama su yi bikinsu irin nasu na bajinta, kar ka hanna su yin komai , ka barsu su kashe koren arzikin su , su nuna murnarsu ka ji?"
Da wannan suka gama tataunawa suka yi salama
A daren bai leka dakin HAJIA Hauwau ba, sai da garin Allah ya waye ya shiga da sasafe
A zaune ya sameta a saman salaya ta kure waje daya da ido
Idannuwanta dake dauke da kunkumbali ya sheda masa bayan na shekarun da suka dan fara ja harda na rashin barci
A nutse ya zauna yana amsa gaisuwarta
Zai fara magana wayarsa ta shiga kuka dan haka ya janyo yana kankance ifannuwansa da dubawa
Sunnan da ya gani ne ya saka shi dagawa ya saka handsfree kamar yadda ya saba amsa kira
Gaisawa suka yi a mutunce, sannan mahaifin Risalah ke sheda masa ai har sun gama shawara sun yanke shawarar eh sun shirya
Jim ya yi da mamaki da wayar a hannunsa yana kallon Hajia da ta zuba masa ido
A nutse ya sake maimaita maganar da suka yi, Baban nata ya jadada masa kwarai kuwa hakan yake nufi
Murmushi ya yi hadi da yin adu'ar Allah ya sa alkhairi za'a hada ya basu zaman lafiya, zasu zo dan tabatar da saka rana da dukan sauran tadar malan bahaushe
Hajai kamar ta daka tsalen albarka ta saka ihun murna take ji , sai murza kafa take dan dadi tana kallon mijin nata
Murmushi ya yi ya ce" Kin ga, shigowa na yi dan na sanar maku jiya fa mun je gidan su sarakuwar taki, sai ga amsar uban yace sun shirya, " tiryan tiryan ya maimaita mata abinda ta sani tuni
Ai kam murna da farin cikinta ya kasa boyuwa har ya zuba mata ido yana murmushi yana kallonta