Sashe 53
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina ta wani turo baki kasa kasa ta ce" raina ni fa ta yi, wai kashedi take min, ni banma fara dukam nata ba ta fara wannan haukan fa ABDUL"
ABDUL ya yi murmushi yana tare Rislaa dake son jin abinda suke fada ya kara rage amon muryarsa sosai ya ce" Gwara dai kar ki biyata ke ai baba ce ko?"
Amina ta gyada kai
Abdul ya ce" To kyaleta kawai kin ji?"
Amina ta gyada kanta tana dan lumshe idannuwanta dan yadda yake maganar cen kasa sai ta nutsu koda zata iya jinsa
A hankali Abdul ya zarro harshensa ya dan lashi gefen kunnenta da shi
Zabura ta yi tana wartsakewa ta ja gaba kadan tana kai hannunta hadi da sosa kunnenta ta juya tana fadin" Kin ci Sa'a, gobema ki zo min nan ki gani, dilla malama yara kanana sai raini......"
Su dukansu sunna kallon kofar da ta rufe ne a tsaitsaye, shi har ga Allah da tace yara kananan ne ta saka masa stop, in ya fahimta dai kamar matarsa ta janyo masa wajen uman biyu
Ita kuma abinda take son fahimta shin maganar da ta yi ya gane mai take nufi ne ko menene ya cewa Aminar?
A sanyaye tana dubansa ta ce" AR, dukana fa ta yi da bulalar nan"
ABDUL ya dawo da dubansa a hankali kanta, samun kansa ya yi da dan tsura mata ido, sai kuma ya budi bakinsa ya ce" A haka kuke yawo a cikin gidan kema gardaye na yawo? Wai ko so kuke yi na fitar da ma'aikatan gidan nan ne na zuba maku mata ? Koda yake yanzun matanma sai mutun na kula kar a sakashi uku ........"
Ya idasa yana nufar hanyar ficewa a dakin Amina
Dan daga kafarta ta yi sai kawai ta yi luuuuuuuuuu ta tafi da karfi ta kifu a kasa
Da sauri ya ja da tafiyar da yake yi ya juyo inda ta fadin
Cikin sasarfa ya karaso wajen yana fadin" Subahanalah, Risala, Risala"
Mace, du yadda ta so tafiyar da tsarin rayuwarta a sila na daukan alhaki ko cin galaba a wani abin sai dai idan bata saka kanta ba, shi yasa ko me take yi a yawaita yi mata nasiha, Adu'a, fada, da kuma uzuri
Du yadda ya gane cewa harda shari a lamarin Rislaa faduwar nan da ta yi take rike numfashinta sai ya daga masa hankali
Cike da damuwa ya nemi aboki kuma amininsa ya zo ya dubata harma ya banka mata allura ta dexa domin shi lamarin numfashi a yadda ka sarafashi ake ganninsa, haka masu ciwon huka idan ba a lokacin da ta tashi ba aka yi masu hoton wajen ba za'a taba gannin ciwon haka ba
Bata da shi, batada dalilinsa ta ringa jan jumfashin tana hucin mai huka a dole aka yi mata allurar da ta hadasa mata rawar jiki da bugawar zuciya , domin haka take ko baka da lafiyar ne ana yi maka ita take hadasa maka haka a hankali kuma ta saki
Dukka wannan azabar Risala ta ji ta gani ta dauka, zata iya jurewa in dai a kan Mijinta ne
Du yadda ya so mayar da ita nata bangaren abin ya gagara, da sauran kwanan Amina daya Risala ta kwana a bangarensa, sai dai bai yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba, du irin yadda ta bale mabalin riga ta langwabe da gangan sai ya tashi ya bar mata dakin, domin ba zai taba bari yana cikin hayacinsa ya saka kansa a uku ba..............ita dai ta karra daukan hakuri dan ta san ai daga gobe komai ya kare ta kama aiki, a nan zata nunawa Amina menene kula da miji
________________________________
Washe gari, kusan karfe takwas da rabi Amina ta karasa bakin kofar dakinsa ta tsaya tana tunanin ta yadda zata iya bugawa
A kadan ta dauki minti ashirin a nan, domin har zama ta yi ta rafka tagumi tana kallon dan rainin hankalin da ya hannata fita a gidan
Tunanin da ta yi da sake duba message din cewa daga yau har zuwa kwana bakwai je kake da damar ajiye takardunka , ta kuma san cewa tanada gyare gyaren da zata yiwa takardun nata, ga kuma gyaran kulin wainar Baba domin gobe ne juma'a ya sakata yin safiya dan ta je ta gama komai da wuri ta dawo, ga yar uwarta da ta kwana a ranta, idan tana tune da irgen bai fi sati biyu ba Fido ta cike lokacin haihuwarta, a irgensu fa , domin ba asibiti ta je aka fada mata ba
Sake mikewa ta yi ta kai hannunta a hankali ta shiga kwonkwasawa sannan ta dan dakata
Sake saka hannun nata ta yi ta kuma kwonkwasawa sannan ta saka hannunta wajen abin budewar ta murda da fatan Allah ya sa ya tashi ta shiga da salama a bakinta
Ido ta zuba a abinda ta samu tana kallo
Da wani irin langwabewa Risala ta rigo hannunsa tana furta" Weshhhh baby ba zan iya zama ba ka bani a bakina plz"
A hankali ya kamata da kyau ya zaunar da ita
Risala ta karkatar da zamanta tana wani irin dantse lebe tamkar a kasanta ne take jin zafi
A hankali Amina ta bi yannayin nata da kallo, ta samu kanta da sake zuba mata ido na yan dakiku sai kuma ta dawo da dubanta kan ABDUL dake tsaye yana kallonta, yar simple din makup din da ta yi ta fi komai shiga idannuwansa, abinda ba koda yaushe take yi ba shi yasa komai kankantarta idan ta yi takan yi kyau sosai
A hankali ta bi shigar jikinsa da kallo, farar riga ta ciki irin ta maza fara kal kal ta lafe a ginanen jikinsa ta dan hau saman wandon dake jikinsa na yadi ruwan madara wanda har arzuzumin dake jiki ana ganni da kuma irin yannayi dai na tsarin hakitar gamjin namiji sannan ta hauda dubanta har zuwa lebensa mai ruwan na jarirai ta kai wajen hancinsa sannan ta sauke idannuwan nata tar a cikin nasa idannuwan suka yiwa junna kallon ido cikin ido
A hankali ta janye ta juya tana manta kwata kwata abinda ya kawota dakin
"Aminah".....ya furta a sanyaye yana kallon bayanta, tar saman bayanta dake cikin hijab har kasa ja, ama irin dinkin hijaban yan matan zamani hijab kamar doguwar riga jama'a ya bi ya lafe a jikin matar mutun?
A hankali ta juyo tana sake kallonsa
Sai a lokacin ta tuno abinda ya kawota dakin
Ido ta dan lumshe a hankali ta ce" Dama, zan fita ne, wai sai yace ka saka dokar sai ka sanar masu idan wani zai fita a gidan.....gashi ina sauri inada muhinman abubuwan dake gabana"
Har ta dire aya yana biye da hannunta na dama da take dan nunawa da shi tana dan wanawa da shi kadan kadan haka.........., Sannan ya sake zuba mata ido da yannayin da ta ajiye maganar tana sake kai dubanta wajen da Risala ta kara karkacewa tana furta" Baby....zafi nake ji......................"
A hankali ya dauke dubansa bayan ya sake kallon Risala da tunanin hukar nata har hanna mata zama yake yi?, Ya sake duban Amina ya ce" Uman Biyu, ina da ina zaki je ne?"
Amina ta kai hannunta gaban goshinta ta dan murza tana fadin " Zan je gyaran takarduna ne, sannan na biya wajen Baba"
Zaunawa ya yi saman kujerar yana dauko kofin lipton din still yana binta da kasalalen duban nan ya ce" AA ba zaki tafi ba"
Ku gafarceni dan Allah, abubuwa ne a kusa kusa hidimun biki
Na gode sosai😍😍😍😍
*NZL PAGE3️⃣4️⃣*
Maman Risala da mamaki ta ce" ABDUL, yanzu a kan wacen matar ne zaka sakamu a gabaa ka nemi rainamu har ka nuna kana iya rabuwa da RISALA yau daya kwana daya?"
A zabure Risala ta kalli Uwar hankakinta tashe ta ce" Mama sakina kuma?"
Abdul ya sake sauke ajiyar zuciya ya mike gaba daya bai kuma cewa dayansu ufan ba , ciki harda kakarsaa ya haye sama
Mikewa Hajia ta yi harta jakarta da wayarta ta bari a nan ta shiga binsa saman da dan sauri, inda gaba daya suka rakata da kallo
Yana shiga tana shigowa ta bude kofar da karfi ta jiga ta kamo shi ta juyo da shi yana dubanta a rikice ta ce" ABDUL, yau ni zaka wulakanta? Abdul ni zaka watsawa kasa a ido a cikin mutane ka wulakantani?"
Abdul ya ja numfashi a hankali ya kama hannunta ya nufi bakin gadonsa da ita ya zaunar da ita, sannan ya tsuguna a kusa da ita kadan yana dubanta a nutse ya ce" Hajia, me yake faruwa ne? Me yake damunki ne haka?"
Hajia ta ce" Ni za'a tambaya abinda yake damuna ko kai Abdul? Kai za'a tambaya abinda yake damunka da har ya rufe maja ido haka"
ABDUL ya yi shiru kadan, sai ya sake riko hannunta yana dubanta ya ce" Menene abin daga hankali acikin abinda Allah ya hukunta?, Du da ake wannan rigimar idan Allah ya yi sai mun zauna zaunawar fa zamu yi, idan kuwa Allah bai yi ba muna kallo sai dai mu yi hakuri fa Hajia"
"Dama kanada niyar zama da ita ne Abdallah? Dama kana soyaya da ita ne?, Dama ka jima da sanninta ne ko menene? Abdallah ta girmeka fa?" Hajia ta fada tana tarar numfashinsa
A hankali ya ce" Hajia , halal ne, kuma sunna ce mai girma wace Ma'aiki ya raya SAW, ita shekara daya ce tsakanina da ita wace idan za'a zauna a duba yarintarta sai ace na bata shekara takwas ko goma a haife............, Hajia shekarunta be matsalar ko mene?" Ya idasa a sanyaye yana kallon Hajiar............
Hajia ta ce" Magana kake yi a kan shekarunta kadai?, Kosai fa take saidawa, kwararo kwararo tana yawo da yayanta da kake cewa wai ba nata bane"
"She's virgin Hajia" ya fada kasa kasa sosai wanda hakan ya saka su dukansu yin shiru kamar an yi ruwa a dauke, domin shi din da kansa ya zame masa dole ne fadin hakan, ita kuma hajiar wata irin kunya da nauyi ne suka zo lulubeta, gaba daya ta rasa kallonsa zata yi ko sada kanta zata yi kamar tana gaban sirikanta?