← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 83

Sashe 64

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina ta tuje hijabin, wani mahaukacin kyau da ta fara yi na daban fiye da gyaran amarcin da ta sha, da wani irin luf luf da gashinta ya karra yi sai wanda ya gani, tana tuje kafafuwanta ta ce" Ki daina ce min Hajia, ni ba HAJIA bace, hasalima filin jirgin kansa ban san a wace anguwa yake ba, kawai sai ki ringa min abinda raina baya so bayan ban maki komai ba?"

"Annabi Muhammadu Rasulullah salalahi alaihi wa ahlihi wa salam, na shiga uku ni Hindatu jikar Maryama, Hajia ki yafe mib baki daya rankatakaf laifin da na yi maki, ki kuma dauka kan ba za'a kuma ba, duka kaf abinda bakya so zan daina yi miki har karshen rayuwata a gidan nan kin ji Hajia?" Hindatu ta fada tana sake dukawa gaba daya hankalinta a tashe, ita tama manta tana sake maimaita Hajiar da aka hannata fada

Da haushi Amina ta mike tana jin juwar na daukanta, dan walahi juwa take ji sosai , gaba daya hadin turaran nan ya mata karfi shi yasa ita bata anfani da turaruka masu karfi, dan sunna cutar da ita ko cenma

Hijabinta ta amshe tana hararar Hindatu dan ganu take yi ai du laifinta ne, ta hannata ce mata HAJIA ta wani sake fada mata

Dakinta ta nufa tana fadin" Sai ki yi ai , ki yi ta cewa Hajiar Hindatu, nace ki kwana kina fada"......
Tsuru Hindatu ta yiwa kofar , sai kuma ta yi hanyar kicin har kamar zata kifa tana adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta koreta, ita ta rasa me ta yi da zafi haka har Hajiar take kuka? Wayo duniya

Tana shiga dakinta ta yi bayi tana wurgar da abubuwan dake jikinta

Wanka ta sake yi dan zafi take ji du irin sanyi sanyin garin

Tana fitowa ta dauko yar yololuwar riga fara ta saka , sannan ta dauki hijabinta ta zurma ta fita falo

Wajen abincin ta bubude tana dubawa, gannin abubuwa irin na turawa sak ta rufe tana jan dan tsaki ta nufi kicin din da kanta ta dauko dadawa da tafarnuwa da dan kayan yaji mai kanshi sai magi ,
Friza ta bude ta babako kaza guda ta tsomata a ruwa ta zauna tana jira
Sai da kazar ta saki sannan ta yayankata ta cire bindin ta sakata cikin tukunya ta zuba dadawar nan da komai da komai sannan ta dora saman gaz ta sake hayewa tana dan balancing din kafafuwabta tana jira

Kanshin dadawar ya sakata hadiyyar yawu har kazar ta silalu sosai ruwan ya janye saura kadan, ta juye a kwano ta yi zamanta a cikin kicin din ta ringa dangwalar kazar nan da yajin dadawa tana ci, har wani lumshe ido take yi, a irin wannan lokacin babu abinda ya kai mata kazar nan dadi du duniya

Kwafa ta yi ta ce" Husaini harda kai a kin biyoni ko? To gashinan ina cin irin dahuwar da kake so ni kadai"

Tana gamawa ta kimtsa komai ta koma dakinta ta sake wanke bakinta taa kuma murza humurarta sannan ta hau saman gadon ta zauna tana zubawa waje daya ido

Samun kanta ta yi da yin kwafa kasa kasa ta ce" A me ka dauki kanka? Me kake tunani a kaina? Ko me kake tunani daidai nake da kai walahi!,ina nan gobe sai ka bani sakina malan!"

Ta jima tana fama da tunani da fadace fadace sannan ta koma saman gadon ta kwonta ta yi Adu'a ta yi shiru tana tunanin ta yaya zata iya yin barci a irin wannan lokacin , sam bata jin barcin walahi, gaba daya ranta a wani bace yake bata san dalili ba

Sai da karfe goma ta gota ya shigo dakin bayan ya kashe komai ya sadada a hankali saman gadon ya haye ta bayanta ya sanyo hannunsa a hankali wajen mararta yana dan shafawa

Matsawa ta yi tana son juyowa dan ta mike lokaci daya ta fashe da kuka

Da mamaki kasa kasa ya ce" Na shiga uku mai kuka ne shi kuma"

Tana kukan ta ce" Ka sakeni, ba dai nice abin wulakantawar ba ko?, Mema na maka a duniya da zafi ne wai? Haka kawai ka ringa sakani kuka , da me kake so na ji ne? Harda zaka yi magana kuma ka ki bani amsa a bayane , kuma ka min alamun zaka zabga min mari? Abdul yayarka ce fa ni idan ka mareni ina zaka kai abin kunya?, Ka sani sarai a duniya Hajia batada makiyi irina, bata so, ta taki Sa'a nima bana so, kaima baka so to ba shikenan ba? Babane zamu san yadda zamu bashi hakuri ya yafewa kowa idan yana so dan ya huce ya bani wani datijo mu je mu karata ko?"

A hankali ya sakata a jikinsa ya yi mata rumfa ya juyo da ita barin da yake ya sake riketa a jikinsa sosai yana jin yadda kanta ke sarawa ama rigima ta ki ta daina kukan

A hankali ya ce" To ki yi hakuri kin ji?"

" Na yi hakuri fa kace fa, cewa fa ka yi na yi hakuri? Bayan kana kallona na dawo baka biyoni ka bani hakurin ba, ni kawai ba'a yi min adalci a gidan nan" ta kuma fada tana dago udannuwanta tana kallonsa

Shima tsai ya yi yana kallonta, har ga Allah tausayinta da son fashewa da dariyar rigimarta ke dawainiya da shi

Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya ce" Ni kam ban san me yasa yanzu kike da kuka ba Uman biyu, Haba auntynmu wai menene na kukan a ciki? To maganar ba mun san da zamanta ba me ya sa za'a ringa maimaitata?, Kuma ni babar damuwata Baban ne, shi nake jira na yiwa wayo ta yadda zai yarda ya yafe mana ko? Ko baki damu da fushin Baba mai shanunki bane?"

Aminaa ta dan kikifta ido tana ta jan ajiyar zuciya, a zuciyarta tana aauna furucinsa

Ya dora da fadin" Ranar da na ce masa soma kike a rabu cewa ya yi da kuwa ba shi ba mu gaba dayanmu ko a lahira"

Gabanta sai da ya fadi ta dago tana kallonsa da alamun maganar ta tsoratata

Abdul ya ce" Ni kuma da na ga haka sai nake ta son samo hanyar da zan yi masa wayo, baki gani ba ko yanzu da yace maza mu tafi gidanmu na kamo hannunki a gabansa? So nake yi idan ya zo abin kawai ya dangana ya dauka haka Allah ya hukunta ba tare da ya yi mana fushi ba Ko Uman biyu?"

Amina ta gyada kanta a hankali cike da tunanin maganar
Ta dago tana kallonsa ta ce" ABDUL kuma sai ya fita a harkar tamu?"

ABDUL ya gyada kansa ya ce" Sosaima, shi kam yana son hadin nan sosai bayan mu ba wani so muke yi ba"

A hankali ta ce" Hakane"

Abdul ya ce" Shi yasa nake so mu bi komai a hankali ta yadda zamu kai ga ci a hankali ko?, Kin ga akoy abubuwan da ya dace ace kin fara a matsayinki na ke, irin su fitar da taimakon gajiyayu, taimakawa marayu dai da sauransu ko?"

A hankali Amina ta ce" A matsayina na ni wa?"

ABDUL ya zubawa fuskarta ido, shinning din da bakinta ke yi idan tana kuka ya fi komai daukan hankalinsa

A hankali ya ce" Wai da a matsayinki na Matata ko?"

Fuskarsa har zuwa karshen karen hancinsa ta zubawa ido har sai da ya dan dage mata gira ta ankara ta dauke idannuwanta

A hankali ta ce" Kennan kafin mu rabun ka rabani da sana'ata?"

"Kece bakida hakuri, ba zan rabaki da nemanki ba, za'a fara yi maki gyaran baya ne a zuba maki kayan gyaran amaren.......gyaren nima ai na anfana da shi ko?" Ya idasa yana kane mata ido daya

Kunya ta sakata turo baki hadi da son juyawa

Riketa ya yi a yadda take kasa kasa ya ce" Amina, da gaske sai da na kusa summa fa......"

"Ya Allah" ta fada tana zuba masa ido

Murmushi ya yi ya dora da fadin" Takardunki na amsa a wajen Baba, zaki zana ko me kike so, ama........"

Da dan zumudi tana kallonsa ta ce" Ama me ABDUL?"

"Ama bana son maganar aiki Amina, bana son ki fita aiki ne, kin ga ai ga aikin nan a gida ko? Tunda na gida ne ni ba zan hannaki ba" ya fada yana sake kasheta da kallon da bata san me yasa bata sonsa ba

A ranta kuwa ayanawa take yi' Alhamdulilah, dama nima ai ba son sana'a a titi nake yi ba, kafin a rabu dai da sana'ata, kuma indai na zana jarabawar nan ai shikenan du wani tashin hankalinama ya ragu in sha Allah'

Da sauri ta saka hannunta tana damkar nasa jin ya shiga yin wani abin daban

Da matsananciyar kunya ta ce" Menene haka kuma?"

Fuska ya shagwabe ainun yana kallonta ya ce" Marata ke ciwo fa"

"To ni kuma me hadina da haka?" Ta fada muryarta na gargada, tsoro na fara kamata

Kasa kasa ya ce" Ba yi zan yi ba ai, kadan ne zan dan yi wani abin ko?"

"Ka ga babu wannan a tsakaninmu"

Amina ta fada idannuwanta na yin rauraurau

"Na sani aunty.........just wannan.....".........ya fada yana hafe bakinsa da nata a hankali ya shiga kising dinta
Ya dan saki kadan yana sake hade jikinsa da nata ya ce" Kadan ne zan dan taba......"

..........."uman biyu dan kadan ne nake son yi.....mmmmmmmm ......mmmmmmmmmm"

A hankali ya ringa tareta a jikinsa, du yadda ta so kaucewa ya juyota ya tarota a jikinsa, a hankali ya ringa ribamtarta, har ya zamto ta daina son kwace kanta ta ringa binsa da shanyayun idannuwanta da sukai mata wani irin nauyi
Irin yadda yake yi mata ya girmami tunaninta
Wani abin kamar ta kurma ihu ko zata ji sanyi sanyi, ama ta maze ta matse ta rike
Chapter 64 · 0% Book details