← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 83

Sashe 42

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana komawa ta tarar da Mahaifiyar RISALA ta dage sai fada take yi da fadin magangannu tana kallon kawarta kamar haka" Ke Hajia ki bar maganar nan, an yi ci gaban da namiji karyarsa ta sha karya yace zai yiwa mace haka, na tabata yaron nan wani salon raini ne da nuna isarsa a kan wajen da bai isa ba, a kan wani dalili zai saka min ya ta yi kuka?, Walahi kin ji na rantse bai isa ba, shi din banza shi din wofi, a kan yata zan iya aikata aikin da kare ba zai ci ba, dole ya fito a je a yi dinen nan a gama, du irin kwaliyar nan da Risalah ta sha za'a fito min da wani wasan na rainin wayo? Ai ni kaf a dangina babu talaka, in dan wannan ne, dan takamarsa kudi ai gidan ya tarar, walahi walahi karya yake shi karamin dan duniya yace zai zageni, shi da ya garwayu da talakawanma har yanzu talaucin ke bibiyarsa ya je ya dauko mace yar talakawa ba gaba ba baya futuk kamar beran masalaci? Idan har ABDUL RA'UF ya yi wasa da ni, tabas zan yi wasa da shi!"

" Ke dillah rufewa mutane baki!" Hajia ta fada a kufule cike da matsanancin mamaki tana kallon maman Risalar

Takowa ta yi ta karasa shigowa tana kallonta tamkar zata dauketa da mari a kausashe ta ce" Ke?, Har kin isa ke ki budi bakinki mai tsami ki zagi ABDUL RA'UF?"
Hajia ta dire maganar tana sake bin dakin da mutanen dake ciki du da aka mike ana son basu hakuri baki dayansu

Hajia ta mika hannunta ta dakatar da Uma ta ce" Ina yake kudin? I said ina yake kudin dan Uban Ubank.............."

"Subahanalah Hajia zagi kuma da girmanki? Dan Allah kar ku yi haka a yanzu da kuka zama daya ai ba maganar haka ta fara shigowa a tsakani, maganar Diner kuwa idan wanda ya aurwta yace ya fasa ai inaga aljihunsa ne sai a ba baki abinci su ci su watse ai ba yau ba aka fara taro ba ango da amarya ko?" Auntyn Maman Risala ta fada tana son katse rigimar domin falon cike yake da yan zubawa wuta essence su hasata maimakun su kasheta, duda zagin da maganar ina kudin itama sun tsaye mata a rai harma tanada amsar ba Hajiar sai dai ba zata so a tafi da su haka a baki ba, uwa uba idan har mahaifiyar RISALA ta yi wasa da lamarin soyayar da y'arta ke yiwa ABDUL zata shiga uku ne da kanta, domin abinda take gudun ne zai faru, y'ar tata ce zata zama abin tausayi, babu wanda bai san cewa Risalah ta fi Abdul karfafa soyayarsu

Saukowa take yi da gudu gudu daga sama, kuka take ci na maganar ABDUL, sai dai ana fada mata abinda ke shirin faruwa ta ji hankalinta ya karra tashi, Umanta ta zagi Hajia? So take yo a saketa ne? A haukace ta mike ta cakumi rigar amarenta ta shiga saukowa da gudu gudu tana fadin" Mama, mama dan girman Allah me kuke yi haka? Mama!" Ta idasa fada da karfi tana gurdewa a abin hawa na biyun ta rike karfen da ake dafawa ta fashe da ihun kukan da ya sake daukan hankalin jama'ar wajen dake ta bada hakuri sunna ririke Hajia da umanta tamkar zasu daku

Hajia ta janye hannunta daga na wata datijuwa dake bata baki a hankali ta ce" Its ok Hajia"

Sai kuma ta sake juyawa wajen da maman Risala ke tsaye ta ce" Ki gwada min aiki irin na isasu ki je ki dauki yarki ku je wajen diner ku raya daren nan, ni kuma a yau zan nuna maki aiki na wace ta isa na baki sakamakon hakan, ABDUL yace kar ta je na ga Ubanda zai taka dokarsa! Yarinya baki san maza ba sai kin ji kanki baya jikin wuyanki!"

Daga haka ta juya ta nufi waje tana kokarin sake kiran number Umaimat dan hankalinta gaba daya ya yi gidanta irin yadda gabanta ke faduwa a kan lamarin ya fi komai daga mata hankali, bata san waye wannan mai kuka haka ba, koma waye Alkali na tare da shi, bata san wacece ke kiran mijinta haka ba, wacece ke neman ceto haka ba, loma wacece wani baban lamari marar dadi ya tunkarota............
Bayan motar ta bude da kanta ta shiga ta rufe tana fadiN" KAINI GIDA"

A KAIKI INA? 🧐😫😫😫😫😫😫😫😫😫🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢

Hello mutanen.....
*NZL PAGE2️⃣7️⃣*

Ido amina ta rintse ta kasa amsawa , Babar kuwa tana kalle kalle har idannuwanta suka sauka a kan Amina

Da mamaki tace" Toh? Barci ne haka? Kefa akoy nauyin barci bale idan kika gaji, to maza tashi tashi mu tafi umarnin Baba"

A hankali ta bude idannuwanta ta sauke a kan Baba Lauratu dake kallonta

Ido Baba ta zarro ta ce" Subahanalah menene a idannuwan naki haka ne? Ko bakida lafiya ne Amina?"

A hankali Amina ta iya budar bakinta tace" Lafiyana kalau Baba, lafiya na ganki warhaka? Ko Fido ce?"

Baba Lauratu tace" Lafiya kalau, kiran Mai Shanu ne ya sameni daga direba tunda duku dukun asubahi yace a zo da ni, ina zuwa yace maza na sadaki da dakinki, nace da shi me zai hanna a bari sai da dare ? Yace aa haka yake so , baya so ace uwar gida bata gidanta a lokacin da zata tarbi amarya, ashe shi baima san bakida lafiya ba, tashi ki yi wanka ki kimtsa mu tafi ana jiranmu fa"

Murya a raunane Amina ta ce" baba wani irin gidana?, Baba wani irin gida nake da shi da ya wuce na cen gidanmu? Baba dan Allah ki saka baki a bani takardata"

Baba ta sake kura mata ido, lamarin Amina ya fara bata tsoro fa kuma, irin yadda take saka damuwar abin nan a ranta ya fara damunta itama
A sanyaye tace" Amina, ina cewa mun yi da ke ki yi ta Adu'a ki fadawa Allah sannan ki yi hakuri ta tare a hankali sai a sake yin maganar nan?, Shin akoy wani abu da yasa zaki dawo ki take maganar da muka ajiye ne?"

Amina ta lumshe idannuwanta sakamakon rashin amsar bayarwa
A hankali Baba ta kama hannunta tana fadin" Ciciba ki tashi, keda kike fadawa Allah? Muma muke fada masa? Ki kwontar da hankalinki in dan rigimar kakar ABDUL ce, yanzu haka da na tambaya idan tana nan dan na gaisheta mai aikintace tace ta tafi asibiti, irin mutane masu halayanta Allah kadai ya isa ya daidaita su idan sunnada rabon shiryuwa, shi kuwa ai mun yi da ke ki kyale shi idan kun hadu gaisuwa ta hada ku, idan baku hadu ba babu ruwanki da shi ko matarsa ko?"

Amina ta rintse ido hadi da damkar hannun Baba a lokacin da Babar ta zaunar da ita dangalgal a saman duwawunta

Kasa bata amsa ta yi sai hawayen da ya shiga bin kumatunta
Baba ta dakata tana kallonta sosai tana son gane abinda ya sakata cije lebe haka

A hankali ta sake kamata tana son mikar da ita sai ta ga tana dudukewa haka kuma abinda take sin damkewa dan karta gani sai da ta ganshi domin hijabin dake jikinta fari ne tas

Hankali tashe ta sake duban yannayinta , sai kuma ta samu kanta da kallon gadon dakin
Sosai ta ji ta girgiza da tunanin da ya shiga kwakwaluwarta, kai harma ta so karyara hakan da ajiye haka a matsayin sharin kwatse kwatse ne na tunani

Da kula ta ce" Amina ki mike da kyau mana ki shirya kina ganni lokaci na tafia?"

Mikewar ta so yi, dan kwata kwata bata so asirinta ya tonu, duda Baba ce, ama Babar ce wace ya dace ta boyea tashin farko.sai dai ta makaro domin idan tace zata mike din kafafuwanta kuwa sai dai ta wara su

A hankali Baba tace" Me ya samu kafafuwan naki ne? Kuma jinni ne kike yi haka baki sani ba ya bata maki jiki?"

Amina ta dakata kanta a kasa, a hankali ta shiga shashekar kuka, sai kuma ta kasa rikewa ta fashe da kukan har ta kusan zubewa a kasa

Da sauri Baba ta tareta a jikinta ta riketa sosai tana sauraron kukan nata, har ta tsagaita tana jan ajiyar zuciya

Baba a hankali tace" Kin ji ciwo ne?"

Amina ta cije lebenta , a hankali ta gyada kanta dan koda bata san meye ko yayane ake jin ciwon nan ba tana ji a jikinta tamkar yankan reza akai mata a wajen nan

Baba bata ce komai ba ta rakata bayin ta taimka mata da komai a kusa ta ce" ki yi wankan ina zuwa"

A hankali Amina ta gyada kanta dake sade Har baba ta bar bayin wannan karronma a ranta ji take yi ba zata iya yafewa yaron nan ba gaskiya

Dukkan abinsa yake na bukatar Amina Baba ta daure taf sannan ta je ta kirawo ma'aikatan tana miko masu sunna saukewa wajen morocin dake jiransu wa'inda Baba ne da kansa ya bada umarnin a fitar da su

Kasa inda Baba yake ta koma, cike da jin kunyar maganar dake bakinta da nauyi bayan sun gama magana a kan sauke kaya da komai, cike da kula da dan jimamin dake saman fuskarsa wanda yake nufi da ya san abinda ya faru kennan ya tambayeta Aminar?, Kanta a kasa cike da takaicin Hajia, wadda ya dace ace da ita aka yi maganar nan, ko dan kasancewarta mace, ama firrrr ta ki abin ta ture, ta ce" Alhamdulilah Baba, sai dai jikin nada bukatar gannin likita"

Da kula Baba yace" subahanalah, aya, to ko zata iya yin jimirin zaman mota har zuwa gidanta ne sai likitan ya sameta a cen?"

Baba ta amsashi da eh
Baba ya ce" Allah ya bata lafiya, ku je Lauratu Allah ya tsare, zan zaunar da su idan kura ta lafa na masu nasiha, sannan za'a kawo biyu da yama idan suka sauko daga school, kin san tau litinin ta nasara muke"

Baba ta amsa baba da biyaya sannan ta mike ta koma
Chapter 42 · 0% Book details