← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 83

Sashe 32

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kureshi ta yi da ido, dukkan farin cikin da ta kwasa na rarashin mijinta da ta yi da kyar ya saurareta suka sasanta kansu, da kuma jin dirar motocinsa ya nemi bacewa battt

A hankali ta sauke dubanta a wajen da ya ajiye yaron da irin zaman da yaron ya yi sai ajiyar zuciya yake saukewa ga dukkan alamu kuka ya sheka ko meye oho

"Aa, subahanalah wannan kamar mai tsuntsaye na hadiyar zuciya, Abdallah ina ka samo Mai tsuntsaye haka ne?"

Takardun ya ninke ya ajiye gefen kujerar shima ya zauna saman kujerar yana kallon kakanin nasa irin zaman da suka yi ya nuna masa sun shirya

Baki ya tabe yana girgiza kansa da ya tuna irin bali da jama'ar da suka tara masu har ana wani ririke su gaba dayansu

"Hum" ya fada takaici na tiko shi, yanzun du irin abinda suka raba da tataro mutane dan a shiga tsakaninsu a yiwa daya magana ana wani rike su sunna iface iface bama kamar Hajia har ya wuce sun mance? Ah to su sun mance sun rabawa duniya abin fada sun dinke abinsu a daka, uhum

"Magana fa nake yi bawan Allah nace ina ka samo min mutumen ne na ga hankalinsa tashe?"

A takaice ya ce" Wajen mamansa"

Sai da ta kusan zabura a bayane, sai kuma ta dane kanta tana kallon ABDUL ddin da son su hada ido hudu da shi dan ta fahimci abinda yake nufi ama ya gagara, domin kiri kiri ya wani basar kamar bai san abinda ya fada da bakinsa ba

Sai da ya gama shan kanshinsa shima yana gannin yadda kakansa ya taso ya kama hannun Hasan suka koma wajen zamansa ya raba yaron a jikinsa yana ta yi masa tambayoyin da yaron ya ki fadin koda A ne a cikin tambayoyin yana ta hakinsa dai

Gaba daya abinda ya dan birge shi irin yadda hankalin Kakan nasa ya ki kwonciya a kan lamarin yaron,
Murmushi ya saki a ransa yana ayanna ' Bafa zai yi maka magana ba, gwarama ka kyale shi'

A bayane kuwa a dole ya amshi gaisuwar kakarsa da take ta tankwalowa ya shiga gaishe su gaba daya harda su tambayat yaya Risala? Ya bata amsar tana kalau.............,

Hajia ta gyada kanta tana sake kallon yaron da ya tsaya mata a wuya , si take ta yi tambaya, sai dai tana tsoron amsar da take iya samu a gaban mijin nata, bale yanzu suka gama sasantawa da kyar da walahaula da jibin goshi

ABDUL kuwa kallon kakansa yake yi har ya ga ya dan rabu da tambayar yaron abinda yake damunsa dan ya ki ya yi magana

Maganar anfanin gonar ya fara daukowa yana masa bayani a kan nomar da suke yi da talafin sababin kayan aikin da suka kawo, sunna yin noma ne irin na kasashen da suke da karancin wadatacen ruwan sama ama kuma babu wanda ya kaisu kayan alatu da na anfanin abinci domin sunna anfani da ruwa a lokacin da ba na damana ba su yi noma har su samu anfani mai yawan gaske da kuma gardi,

Baba Mai SHANU ya dafe haba yana girgiza kansa ya ce" ABDUL RA'UFu, anya kuwa wannan anfanin gonar yana da inganci kuwa? Kai zamani na tafe da abin tsoro, yaushe za'a yi noma ba lokacin damana ba?"

Yar dariya abin ya bashi domin haka suka sha da mai garin da gonakinsa suke , har jiya da ya bugo masa waya haka yake salalami yana fadin dawa ta yi tsayi har ta fito? Jama'a hatsi har ya yabanya? Tumaturi kwonce rututu jajajir rudu rudu? Santin abin dai ba'a magana, wai anya kayan nan ba cutarwa a cikinsu?

Zamansa ya gyara yana fadin" zaka sha mangwaro a rani kuwa bana Elhajin Hajia"

Murmushi Hajiar ta yi tana hango lamarin, gaba daya a kasar fa yanzu shi kadai yake da budaden kampanin da zaka samu kayan masarufi sabon fita ba dadadiyar ajiya ba, da farko da ta ga yana da nacewa a kan nema ta hanyar nan haka zata saka Mai SHANU a gaba da rigimar ga sana'a su gwal , su waye waye ama ya nace noma da wani kiwo da waye waye? Me zai tsinta a ciki? Sai Mai Shanu yace da ita abinda kika tsinta da kika auri makiyayi, watau shi,
A yanzu kuwa har wani salo ake kiranta da shi, uwar mai sana'a goma bama kakarsa ba.....to ita kuwa wannan dadi har ina?

Sosai suke dan zantawa tana jefo nata maganar itama, duda bata san dalilin da ya sa za'a bar yaro zaune cikinsu yana cika yana batsewa yana sauraron sirinsu ta hirarsu tsakaninsu ba, ama irin yadda hirar ta dauko dadi ana ta maganar kudi ya sa ta lume take shawagi da sauraron manyan kudade na harkar neman jikanta, kai Allah jikan iyayen yaron nan, su suka faro suka bara masa gadon da ya sake rarabawa yau ya zama haka, lalle da kudi ake neman kudi, ba irin zazabin da bata yi ba da aka bashi gadonsa, ta ringa hauka da iface ifacen a kan me za'a danka masa kudi yana da danyen kai da kadarori yaje a yi masa wayo? Akace da ita harkar gado ba'a mata haka, idan har da rabon ya tara nasa zai tara, ama ba wai a kN gado ba, kar ta kankara hakori da rigimar gado,kayadadiya ce, iska ce mai saurin wucewa

Sai da ya gamsu da degrren saukowar kakan nasa sannan a nutse ya ce" Maganar wajen Risalah"

A zabure Hajia ta dago tana kallonsa da dan zarro ido, wallahi abin sai da ya daketa, bata taba kawowa kanta zai tunkaro kakan nasa kai tsaye da maganar a irin wannan lokacin ba, ta yaya ABDUL ya aikata wannan shirmamen aikin? ME yasa bai yi mata shawara ba kafin ya kawo zancen? Ta gama daidaita cewa zasu zo da baba Rabi'u a masa zancen sai gashi shi ya masa haka kawai?

Baba Mai SHANU ya dan yi jim, sai kuma ya ce" Uhum?"

ABDUL RA'UF ya ce " Ina so a turaa karshen watan nan a gama komai ne"

Baba Mai shanu ya gyada kansa yana fadin" Masha Allah, masha Allah, kace komai ya daidaita, nan da kwana goma sha shida kennan?, To yaya ina fata Uman biyun ta aminta da hakan?"

Tsatsare babban ya yi da ido yana son gane wai da gaske yake abinda yake fada kuwa? Ta aminta? A matsayinta na wa?

Shima yannayin sakewar tasa ya fara daukewa yana kallon Baban ya ce" Tana da hurumi a wajen da bata da zabi ne?"

"Kake tunanin bata da hurumi a wajen da yake malakinta kafin watanta? " Baba ya bashi amsa shima da tare numfashinsa

"Dama dunguru gum canki canka zai zamto malaki? Ko zabin rai kan malaki wani abin ne ba wannan ba, Baba dama akoy maganarta ne?" Ya fada shima yana sake kure kakan nasa da kallon da ya sa Hajia jin kamar ta zurma ihu ta dakatar da su, ama ba hali

Baba ya yi murmushi yana gyara zamansa ya yi sak irin zaman da ABDUL din ya yi shima ya hade hannayensa waje daya ya ce" Akoy gadama ne a wajen tafka kokowa? Ko so kake ka ce min ka tsinke zumuntar da na hada ba tare da shawarata ba?"

Abdul ya dantse lebensa na kasa da takaicin lamarin nan ya ce" Wai dama cencenta ka hango ? Ta wani fanni kennan?"

Baba ya gyada kansa ya ce" Ta fannin da ya fi komai karfi, ta koyi da wanda ya fi kowa daraja, sannan ta dacewar kamarin, ko kana so kace min baka son bak'ar fata yar talakawa?"

Hajia ta kalle shi a zabure, dan walahi sai ta ji kamar habaici ya yaba mata

ABDUL RA'UF ya sake tabe bakinsa ya koma ya jingina da kujerar yana girgiza kafarsa kadan yana sake tunanin amsar da zai ba baba a dunkule ba tare da danta dake wajen ya ji zafinsu ba, dan gaba dayansu sun yi magangannun nan ne a dunkule dan yaron dake zaune, ba zasu so hakan ya zama wani cin fuska ko bacin rai ga yaron ba,
ABDUL RA'UF ya yi murmushi yana kawar da kansa bayan ya gama ayana abubuwa masu zafin da suka fi kona masa rai, shi baba zai wulakanta? Ya dauko bazawara ya maka masa, ya kuma ce sai ya tambayi zabinta idan ta aminta a aura masa wace yake nema? Lalle

A hade ya ce" Ladabin ya fi dadi idan aka cikawa kowa burinsa, naka burin ka cika baka cika nawa ba, anya hakan bai zama wani bigiri na danne haki ba kuwa?"

Cicibawa baba ya yi daga zaunen da yake ya mike tsaye, wanda hakan ya kayar da gaban hajia ta yi tsuru tsuru da tsoron kar aje abinda ya yi zai sake maimaitawa, sai ta ga wannan karron ya kalli jikan nasa ido cikin ido ya ce" Baka fahimta ba kennan, du wani rikici da tashin hankali da kokowar a mace ko a yi rai na shirya mata tsaf a kan wannan lamari, ba gudu ba ja da baya ciki harda barazanar take hakin na dindindin, ni fa a gobe ina iya zuwa na sake daura maka aure da dayar idan mai wajen ta aminta da haka!, Ita din mataki ce ta tarda naka burin!, Idan kun shirya ta amince zan zartar, in kuwa kanada wani da ya fini yake iya wakiltata da raina da kafiyata kuwa fine, na ga sanarwar a TV ko a redio"

Daga nan ya juya ya shige uwar dakansa harda rufowa da ky

Sai da ta tabatar da ya gama rufewa sannan ta juyo hankali tashe kasa kasa tana fadin" Meyake damunka ne? Ka kuwa san irin girman abinda ke dawainiya da shi a kan yarinyar nan? Laifina ne da na yi sake take bashi Wainayana ci ba lokaci,zan iya rantsewa yarinyar nan ta asirce min mijina, yama yi kokari da ba kansa ya aurawa ita ba a yadda yake kaunarta!"

Da sauri ya kalli kakar tasa, da idannuwansa ya mata alamu da Hasan
Chapter 32 · 0% Book details