← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 83

Sashe 28

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsaye take ta ba kofar baya, jikinta sanye da wando irin budaden nan sosai, domin iya kugunta kadai wandon ya rike kuma kalar ruwan madara ne, harda yar igiyarsa da bai san bata daure igiyar bane take reto ta tsakankanin kafafuwanta ba ko menene? Sai kuma rigar dake saman wandon ita ba budadiya ba ita ba damamiya ba, kuma hannu daya a yanke daya har tsintsiyar hannun, kanta sanye da hula ga bulala a hannunta tana rike da kugu da hannu daya ta saka yara a gaba tana cin zali

Daga bulalar ta yi tana fashewa da kukan da ya kusan sakashi fashewa da daria, domin tana dagawa doka masa zata yi ama fadi take" Au baka tausayina? Na dake kan ko? Na mutu ko Fadeel? Na dake ka ba zaka yi min magana ba ko fadeel? To bara na karra maka idan na farfasa maka jiki ai shikenan!"

Kukanta take yi bilhaki, ga kuma yaron jikinsa na rawa kuma yana so ya matsa jikinta ama ta ki bashi dama dan ta san idan ya rukunkumeta an kare ba zata dake shin ba

Shigowa ya yi gaba dayansa yana sake kare masu kallo , a makoshinsa ya dan yi gyaran muryar da ta sakata juyowa a zabure dan bata san da an shigo dakin ba

Ido ya zarro sakamakon yelow din kwabin kwan da ta shafawa fuskarta da tumaturi ya bushe mata ga kuma hawaye na zarya a kai

Hannunsa ya kai wajen bakinsa yana dan sake kallon fuskar da nan take yake karantar shirye shiryen tafka masa fitsarar ake yi
A hankali ya mika hannunsa wajen da Hasan ke tsaye bayan ya cire dubansa a kanta yana kallonsa bai yi masa magana ba, yana nufin ya zo wajensa, dan ya tabata yadda yaron ya cika hadiye harshe kalamansa na fita ne ta hanyar motsi da hannayensa ko yannayin idannuwansa

Da sauri ta saka hannunta tana share hawayenta hadi da rarumar hijabinta ta zurma a jikinta tana hade fuska ta ce" Malan ya haka da shigowa dakin mutane ba ko salama, Allah dai ya sa lafiya?"

Bai ce da ita uffan ba, a hankali ya sake rage tsayinsa ta hanyar dan dukar da gwuiwoyinsa kadan yana sake duban yaron da haka kawai yake ji yana so ya zo gareshi, sannan ya sake mika masa hannayensa duka biyu yana kallon fuskarsa da yannayinsa

Hasan din dake ta haki ua ya cira dubansa ya sauke a kan fuskar Mamansu da ta cire kai ta turo baki gaba yadda ka san wata yar baby ita ala dole fushi take yi ya sake kallon ABDUL RA'UF wata ajiyar zuciyar na kwace masa , ya kalli hannayen ABDUL RA'UF din da kallo irin na nacewar nan sai kuma ya sake sada kansa yana ta wani iri shi ba kuka ba, shi ba hakin summa ba

A hankali ABDUL RA'UF ya dantse lebensa na kasa yana sake kallonsa, bai janye hannunsa ba, haka kuma bai daina yi masa tausasashen kallon ba

Tun Hasan na cire dubansa a kansa har ya dawo ya tsayar da duban nasa a kansa, sai kuma fuskarsa ta ringa nunawa, a hankali a hankali ta ringa wani irin shagwababewa, a hankali kuka ya kwace masa ya daga kafarsa da sauri ya karasa ya fada jikin ABDUL RA'UF ta hanyar shigewa cikin hannayensa ya rungume shi a cikin kirjinsa yana murzar fuskarsa a gaban rigarsa

Daga ita har Husaini ido suka zarro na mamaki
Matsanancin mamaki ne ya kama su na gannin a yau Hasan hankalinsa ya kai kololuwar tashi ya doshi wani mutun daban dake bako a gareshi
Shi husaini kasancewarma tsoron mutumen nan yake tunda ya ganshi sau biyu baya masa fara'a na farko a office dinsa, na biyu a bakin layi ya sa ko a yanzu da ya shigo da sauri ya labe a bayan mamansa , gwara maman tasa ta masa dukan mutuwar kawai da wani bako ya daki banza!, Sai ga Hasan, Hasan dai Fadeel nasa, Hasan na gidansu ya rungumi wannan mutumen marar fara'a

A hankali yake shafa kansa da ya fara tara suma yana jin kukan yaron a ransa
Idannuwansa ya dago dake risine a bayan yaron ya sauke mata duban da zata fasara na ta ji kunya ne? Ko kuma shashasha ne? Ko irin kamar ta sato ɗan nan ne? Ko na zalinci ne? Ita dai duban gashi nan kala daban kamar na wata yar kidnaping, bayan shi din nan ba dansa bane, ya tardo mace da danta ya yi mata ba daidai ba? Lalle yaron nan ya cika raini da wulakanci ! Abinda take ayanawa a zuciyarta

Bata ankara ba ta ga ya mike tsaye da Hasan ya daga shi sukut a jikinsa ya juya mata da ɗa zai tafin mata da danta

Daga iya har Husainin ji suka yi kamar za'a tafi da rayuwarsu ne, dan haka da sauri ta biyo shi daidai ya sake bude kofar zai fita tana fadin" Ya haka wai, bani dana mana Malan!"

Dan dakatawa ya sake yi ya juyo yana kallon fuskarta hadi da yatsina nasa fuskar, domin walahi karnin abin ke dukansa, shi ya rasa me ke damun yarinyar nan da take yaba abubuwan wari a jikinta haka, meye anfanin abubuwan nan ne? Wannan din dake jikinta sai wani iri ya mata da ta sha kukan ama bata kyankyami tana wani dakewa da fuskewa abinta

Wajen da takardu ke ajiye biyu ya kai dubansa

Da Hasan din a kafadunsa ya juya ya dauki takardun sannan ya janyo kofar ya rufe ya yi gaba da shi a jikinsa ya nufi sama wajen Baba

Amina dake ji kamar zata haukace dan gannin ya fa tafin mata fa yaro sai da suka bude suka fito ita da shagwababenta, sai dai inda ta ga ya haura da ɗan ya sakata komawa tana sakin ajiyar zuciya tana rike da hannun Husaini taf a hannunta suka zauna a jikin kofar Husaini ya kwontar da kansa a hankali jikinta yana fadim" Mama Hasan fa? Zai dawo ne?"

Kai ta gyada da sauri murya a rarabe ta ce" Zai, zai dawo, zai dawo in sha Allah, muna jiransa zai dawo ka ji? Mu yi jiransa a nan"

A hankali ya saka hannunsa ya tura kofar ta Baba sannan ya shiga da salama

Tunda ya shigo gabanta ya kwonci kwonci ya fadi abinda ta gani a rungume a jikinsa
*NZL PAGE1️⃣6️⃣*

A sanyaye ya ce" wa ya kawo ki ne?"

Itama a sanyayen ta ce" Ni na yi driving "

Kansa ya gyada yana dan tabe bakinsa, sai kuma ya yi shiru yana kallonta tanai masa byby har ta fice a falon

"Why ba zaka ce da ita auren hadaka ne aka yi da yarinyar dan hankalinta ya karra kwonci?" Mansur ya fada da mamakin irin yadda ABDUL ya ki fadin gaskiya dan ya kare kansa a wajen budurwar tasa dan su zauna lafiya ba sai an yi ta jan zancen ba

ABDUL RA'UF ya yi dan murmushi yana kallonsa ya ce" A kan me zan zauna na bata labarin abinda yake sirrin gidanmu bayan bata zama sirrina ba?......koda sirrina ce idan abun zai iya haifar da fitina gobe ai zan rufe mata shi, bale auren da ba zai zarce gobe ba in sha Allah?"

Da mamaki Mansur ya wara idannuwansa yana kallonsa ya ce" Kamar yaya?"

ABDUL ya tsareshi da duban mamakin shima, tabas yayi mamakin da Har MANSUR ke tambayarsa kamar yaya idan auren nan ya zarce gobe, lolz auren na gigitar Baba? Tabas kakansa ya rikice ne a jiya zuwa yau da ya dauko nazawara uwar ya'ya biyu matar da wani katon ya aura ya saki ko yaya ne oho ya maka masa shi ga shashasha!, Y'ar fa ta daga hannu zata sharara masa mari? Shi fa bai taba gannin mai hayaniya irinta ba, bai taba haduwa da ita bata hadasa masa ciwon kai ba, wannan aure na *SA'O'I?*, Uhum.......
Bai ce masa komai ba ya ciciba ya mike yana duban hanyar hawa sama ya ce" Barci, Mansur barci nake ji sosai, Ni kam bara na je na ga ko zai samu"

MANSUR ya mike shima yana dubansa a lokacin da ya fara hawa ya dan daga muryarsa kadan ya ce" Sai ka sauko zan kalli balll, Hei Man?"

ABDUL ya dakata yana juyowa
MANSUR ya ce" Ka yi dogon tunani a kan lamarin nan"

Murmushi ya sakar masa ya idasa hawa ya nufi dakinsa dan ya huta

A ranar kwata kwata bai amsa kiran kowa ba, haka kuma bai nemi kowa ba, Mansur ne da dare da ya fito daga asibiti kafin ya isa gidansa ya biya ya duba Mai Shanu da Hajia, a nan ne ya hadu da biyu , Husain ya fada masa cewa mamansa na daki bata yiwa kowa magana Baba lauratu na shafa mata kwai a fuska karni jirr
Hasan kuwa bai ce masa komai ba , ama kuma yau ya dan sake da shi dan yakan dan yi masa murmushi kadan , ama baya yi masa hira
Da wannan ya wuce gida zuciyarsa cike da dariyar yar kakanin nasu, Shi Baba Mai shanu yana bangarensa hankali kwonce yana ibadarsa, matarsa kuwa ta kile ta kulle bata kula kowa ta labewarta itama a nata dakin, dan tunda ta shige bata sauko ba, bata nemi kowa ba, danma mai aikin nasu an jima da ita ta san kan gidan fiye da tunanin mai karatu, ita ke kula da abubuwa da dama, dana Hajiar kan bata umarnin a dafa kaza, ko a kiyaye da tsaftar gidanta , da irin cimar Elhajin wadda yawancin lokuta abinda zata ce a girka masan baya son cinsa a ranar sai an yi ya sa a tuka masa tuwonsa da man shanu ya rangada

Washe garinma tun karfe tara ya wucewarsa bakin aikinsa, ya sauka a ma'aikatarsa ya shiga aikinsa tukuru, neman kudi a jinninsa yake, baya gajiyawa da mayar da biyar goma, ya fi sakewa a harkar neman kudinsa, a nan nema ya ringa samun kira jefi jefi daga manyan abokanan aikinsa ana masa barkar auren da aka daura a lulube
Shi dai yakan amsa kawai idan ya kashe sai ya yi murmushi ya girgiza kansa
A haka ya gama ya koma gidansa yauma bai nemi kowa ba, ciki harda kakansa
Chapter 28 · 0% Book details