← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 83

Sashe 82

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haukace ya bale motar ya fito ya nufi wajen da tuni aka fara tsayawa ana son fara yiwa wajen taro

Mutanen dake wajen kofar ya kautar ya kama ya bude kofar hankalinsa tashe

Da sauri ya dago Abdul dake kwonce jikin sitiyarin motar kansa saman sitiyarin a haukace ya ce" ABDUL?"

Ido ABDUL ya rintse dan ihun ya ratsa masa kunne sosai yana bude jajayen idannuwansa ya kalli Muhammat

Muryarsa cen ciki ya ce" Ta yiwu ta shige cikin gidan Baba ko?"

Masu gadi da suka zaburo jin an ce an yi hatsari du suka nemi rudewa gannin wanda ya yi hatsarin, sai dai yadda ya ki a talabeshi ya fi komai damunsu

Cike da damuwa Muhammat ya ce" Sir buguwa ka yi fa ka tsaya mana a rikeka mu karasa gidan"

ABDUL ya juyo yana nuna masa marfin motar ya ce" Ka manta wace irin mota ce?, Muhammat nakuda take yi, ban san inda ta shiga ba"

Muhammad ya bi bayansa yana bashi baki dan motar tuni mutanen gidan Baba sun shiga kulawa da wanda ya bugun mata da motar kanta, duda shine bashida gaskiya kuma shima bai wani ji ciwo ba, babur din dai ne ya dan tatabu

A hankali ya karasa wajen da Baba ke tsaye yana jira a dawo a sanar masa Allah ya sa ba'a ji ciwo ba, an fada masa an yi accident a kan kwanar gidansa shi yasa ya fitoya tsaya kamar wani mai anguwa yana jiran dawowarsu, ai ga motar gidan ABDUL RA'UF ta shigo

Hankalinsa a kan ABDUL RA'UF din har suka zauna yana jin gabansa na faduwa, yana duban Muhammat ya ce" Muhamadu, lafiya? Me yake faruwa ne?"

Muhammat ya cire takalman ABDUL ya nufi waje yana fadin" Ina zuwa baba bara na janyo motar cen , walahi kar aje su raunatata "

Baba ya kalli ABDUL yana jin kamar ba zai iya tambayarsa ba, dan yana tsoron amsar da zai bashi

Da kyar ya daure ya ce" abdulahi me yake faruwa ne? Lafiya?"

ABDUL ya jinginar da bayansa a jikin kujera yana fitar da zazafan nishi , da kyar ya ce" Baba, ban san inda ta nufa ba, kuma dai inda ta tashi na ga har kamar ta fara zubar da ruwa, nakuda take yi"

Baba ya fuskanceshi da kyau ya ce" Kana bani magana a dunkule, ina Uman biyu? Dan na san itace da ciki a tare da kai"

ABDUL ya furzar da iskar dake bakinsa da daci ya ce"
A sanyaye Risala ta ce" Bab, ka je da ni mana Chainar, me yasa zaka tafi kai daya bayan kanada mace?"

Idannuwansa ya dan lumshe ya dauki ruwa dan ya jika makoshinsa ya kurba kadan sannan ya fuskanceta ya
ce" Risala, na fada maki , aiki ne zai kaini chaina, aiki irin mai wahalar nan, idan na fice tunda duku duku idan da rai da lafiya sai da wani duhun zan shigo, na barki ke daya a dakin hotel, chaina gari ne na aiki, ba zama , ba wasa, idan na je da ke ba zamu ribanci zuwan ba, ke me zai hanna ki zauna ne har Allah ya dawo da ni?"

Risala ta juyar da fuskarta gefe tana ta tunani, sake rage garajen muryarta ta yi sosai tana dubansa ta ce" Kennan ni kadai za'a bari a gidan? Sati daya fa ba wasa ba, ga gidan nan da girma"

ABDUL ya ce" To ko zaki je gidan Hajiar ne kema?"

Da sauri ta zarro ido tana girgiza kanta, ita kuma me zai kaita gidan hajia ? Ai har an yanka mata wuya saboda kiyaya, matar da ta tsaneta ta zabi kishiyarta a kanta? Ina ba zata je ba walahi ( Ina jiran irin wannan lokacin dan na kawo wani misali kadan a garemu baki daya, ba dan na fiku sanni ba, ko dan zan koyar da ku ba, ban kuma isa na cenza wanda ya dauki maganata da zafi ba, naci ne irin nawa ya sakani zan yi maganar nan, Yan uwana mata, mun san cewa aure abu ne dake kamawa ba dole sai an tsani mace, ko dan ta gaza ta wani fannin ake kawo mata abokiyar zama ba, ta yiwu laifin nan na mijinku ne, ko kuma haka kawai kika tankadawa kanki garin wahala mai cike da tsakuwa, kina tunanin ke kece mace ke kika isa ki kawowa namijin nan da ya auri matarsa ta farko shekara a kadan biyu, ko uku, har zuwa goma ko sama cenje cenje da jin dadin rayuwar da bai taba yi ba? Albishirinki, itama a ledarta ya daukota, yar shila sabuwa dal, ya murza ya dannan son ransa, komai lalacewarta da ita yake kwana saman gado daya, yan yayan da kike ganni nasu ai kin san ba fyade yake mata yana bata su ba ko?, Soyaya mai sunnan soyaya ta yiwu wace suka yi ba zaki taba ganninta a wajensa ba, ta yiwu lamari ne na bukatar karo ki dan karrin jin dadi na namiji, kina sane da cewa namiji na karra aure dan ra'ayi, yana karra aure dan karin gidan hutu, yana karra aure dan matarsa na kyautata masa ya karra samun kyautatawa? Yana karo ki dan yana so a cika masa gida da ya'ya, yana karro ki dan shi din mai yawan koyi ne da wanda ya isa a yi koyi da shi sugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wa salam, ama sai ki tashi, ki cika kwakwaluwarki da abubuwa, tunani kala kala, ke kece mace kece isashiya kece matar so, wata zata shigo ne da kudurin mayar da matarsa banza ya zamto komai ya dawo hannunta itace mai waje mai tabarmar ta nade?, Wata dama nufinta waje zata yi da uwar ya'yansa bayan ita ko yayan ba zata iya rike masa da zuciya daya ba, wata da nufin lalata gidansa wargaza gidansa ya zamto kowa bai ji dadin zama ba, wata da nufin haifo wa'inda zasu gaji gida, abubuwa dai gasunnan barkatai subahanalah, ta yiwu wannan namijin da kike hobara a kansa shine asalin wanda zai kasheki kamar yadda ya kasheta, idan nace kashewa ba na kai mutun kiyama ba, yau wani namijin irin mumunan zaman da yake da wata macen kamar zaman kiyaya, kamar wace aka kawo dan ya kashe, ya daureta ya ringa yi mata kisan mumuke, bai saketa ba bai jiyar da ita dadin zama ba,sai kin zauna ki gane, idan kuwa ba haka bane kika samu macen nan a gidanta, macen da ta san kanta, take zaune da ciki daya da jama'ar dake zagaye da ita, ta samu kyakyawar mu'amala, idan bakida wayo kika kasa yin koyi da ita kika samu kema naki waje har kika gina taki rayuwar sai ki dawo kina batun cewa ta asirce kowa ta malake miji baya gannin kowa baya ganne komai sai ita sai zancenta, baki san irin wahalar da ta sha na biyaya da takewa da gannin kaskanci kafin su zamto aminan junna ita da mijinta ba, baki gane a haka dinma yakan birkice ya rufeta da fada ama kanta a sade bata dagowa ba dan haka suka saba rayuwarsu dan haka take masa biyaya, saima ki ce ai ke ba zaki dauki wulakancin namiji ba, itama matarsa kissa ce, ke baki yardaba kennan da ana iya yin biyaya domin Allah ba dan a yi kissa da kishiya ba ko? A haka da yawa zaman ya gagara a ringa cewa ta fitar da ke, a ringa magangannu, idan kuwa zaman ya zaunu a wahalce, kulun cikin cin zarafin junna? Ki sani idan da kika tardota ta dan yamuge ne, fatarta ta dan ja ne, ko kwali ta saka baya mata ram ya zauna mata dasss hakan rayuwa ce, yau da gobe ne, kwonci tashi ne, haihuwa ce, shekaru ne, Mace daman ta fi namiji tsufa, namijin nan naku da kike gannin kin zo ki ririta kema haka zai didirka maki naki cikin a hankali ki fara janyewar fatar shi kuwa ram abinsa..........dan Girman Allah mu ringa yiwa kanmu fada, mu rayu da sannin ko me muke takama zamu mutu baki daya, ban yi maganar nan dan na fi wata ko ni ba zan yi kishi da kishiyata ba idan Allah ya kadarto min ita ba, na yi be dan baki daya mu ringa tunani a kan lamuranmu, kishi halal ne, kishi akoyshi, ba karya bane, ama kuma wani kishin mu da kanmu zamu hanna kanmu sukuni da kwonciyar hankali/ Maganata ba wai iya Amaren da suka tardo iyayen gidansu nake ba, harta ke hajia uwar gida, ki sani yarinyar nan da aka kawo maki idan kika dauketa kika riketa dan ki cutar da ke Allah zai saka mata, idan dan kinada dama wajen mijinku kike anfani da damar nan kina kunna mata wuta Allah na jiranki, idan dan kin fita sannin danginsa ba zaki sakata a hanya ba kina kallonta ta ringa aikata abinda zasu tsaneta kema kin haifa!, Idan dan kece Hajia mama uwar gidan Elhaj zaki rike kambun nan ki munana mata, ki wulakantata, ki sakata labewa a daki dan tsoronki da tsoron kaidinki sai ki yiwa kanki karatun ta nutsi ki kalli fatar hannunki, na tabata zaki gane tsufa kike kara yi yau da gobe, yau ko ba mutuwa a barki da tsufan nan zaki zo shekarun da kanki ba zaki gane ba bale wani, DUNIYA AI MAKARANTA CE, du abinki ba zaki kasheta ba idan lokacinta bai yi ba, dan an aurota ne ta maki laifi sai ki bada hima a takaitaciyar rayuwar ki munana mata, idan kin je kiyama sai ki amshi sakamako daidai da laifinki!, Sai kai baba, idan ba zaka iya rike biyun nan ba ka yiwa girman Allah kar ka karro, ko ka salameta ka dauko tunda bakada adalci!, Kaine gyaran gidanka, kuma kaine mai batawa!, Idan ka yi aiki irin na munafurci ka bata daya a wajen daya dan ka faranta ran daya ka lalata gidanka da kanka!......Na gode )

Risala ta girgiza kanta tana fadin" Aa, wai da cewa na yi nima na je gidanmu har ka dawo?"
Chapter 82 · 0% Book details