Sashe 2
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki take kallonta da son karrin bayani a kan wai tsoratar da maza take
Baba Lauratu ta ce " yawancin wa'inda basu sanki ba idan sun ganki kina yawo da biyu zasu dauka naki ne koda kuwa yannayin jikinki bai nuna kin haife su ba, aman Amina ba kowa ne ya san cewa biyu y'ayan Firdausi ne, wainda suka sanki kuwa idan sunna da ra'ayin zuwa su aureki zasu iya tsorata da yannayin rayuwa ciyar da y'ayan mutun biyu ba kowa zai iya dauka ba, ki yi hakuri iya gaskiyar nake fada maki Amina kin zo kin sakkawa ranki wahala, wahala ce mana, Allah na tuba a kasar nan idan kai ba kowa bane ba dan kowa bane ko ka samu ka gama karatun sai dai ka san yadda zaka yi da shi aman ba dai ka anfana da shi ta hanyar da ta dace ba, gashinnan shekaru na ja Amina shekarunki nawa yanzu? Sai zuwa nawa zaki iya gane me nake nuna maki ki dauki matakin da ya dace ne?"
Amina da idannuwanta ke lumshe tana sauraron dukkan bayanan Baba Lauratu zuciyarta na dan dokawa, ba dan komai ba sai dan ta san iya gaskiya ne Babar ke fada mata, aman kuma itama da nata maganar, tana da nata bayanin a kan maganar dan haka ta fuskanceta a nutse ta ce" Wani lokacin, du yadda bawa ya kai da son cenza yannayin kadarar rayuwarsa babu abinda ya isa ya aikata sai dai ya ci gaba da adu'a Baba, walau ala ni ban zo duniya dan na yi aure ba, ta yiwu kuma zan samu auren a hankali.......Abinda na fi rikewa da karfina Baba shine y'ayan nan y'ayana ne, yayan yar uwata ne, diyan zumuna ne, yanzu da nake cikin haka ina cikin niimar ubangiji, mijinta ya nuna nasa yayanma kama cen riko cen ne yake yi ina zan kaisu? Nawama suke yaren? Ba zan taba sakin hannayen biyu ba Baba, kin ga fa dangin mahaifinsu basa so, ina zan kaisu?......"
Ta sauke ajiyar Zuciya ta dora da fadin" Ni bani da inda zan kaisu Baba, shi yasa na koyawa kaina zama mamansu da soyaya a zuciyata, na koyawa kaina kula da su da basu tarbiya, na tabata wata rana zan samu wani datijon arziki ya daukeni da yarana koda a gidan gadonmu ne mu zauna.......Abu biyu da na san ba zan bari ba shine ci gaba da neman ilimi ta hanyar da ta dace, da kuma ci gaba da kula da biyuna" ta karashe a sanyaye haka kuma jikinta na karra daukan sanyi ainun, bama kamar idan ta tunna irin abubuwan da take fuskanta a wajen wasu mazan dan kawai ya kasance itace mace tal a gidan da suke zaune sai yan yaren na y'ar uwarta, aman ta san ko menene adu'a na gaba da shi, kuma ta san Allah ne gatanta
Baba Lauratun itama ta sauke wata ajiyar zuciyar ta ce" Allah ya dafa maki y'ar nan, Allah ya taya ki riko yarinyar nan"
Da amen amen AMINA ke amsawa ta mike tana duba wajen su Hasan ta ce" Husaini zo dauki bokicin masar Baba mu je, mai tsuntsaye kai yau ba zaka rike komai ba?"
Hasan ya kawar da kai yana sake hade gurarakinsa ya ki bata amsa
Baba Lauratu ta saka daria tana fadin" Sai gwamnati baban kowa, yau mijin kulin wainar abokin naka ne ba zaka dauka ba? Zan kuwa yafa mayafi na je da kaina na bashi kannun labari sai ya san irin zaman da zai yi da kai a gabanan nan"
Ita dinma bai tankata ba, yau gana daya yan hali ke tare da shi, shi yasa AMINA ke lalaba shi su wanye lafiya dan ba zata iya rigimarsa ba
Amina ta sake kallon Baba ta ce" Baba ba'a gyara shinkafar ba kennan yau?"
Baba ta tabe baki ta ce" kin ga Amina, ni ina yi masa hidima ne dan shi din mai hidima ne, aman matarsa ni fa ba zan iya ce maki ga kamaninta ba, a gaskiya ke kika ga kya iya wannan abin, ace waina sai kin yi kala biyu du juma'a ta Allah? Ita bata cin hatsi? Har yanzu bata san da ta tsufa ba ko dan bata samu haihuwa da wuri bane? Ga kuma Kumbar susa na kada mata gangar shedan, kin ga ki je ki gyara abinki da kanki Allah baki lada idan da ladan"
Yar dariya Amina ta yi tana mata salama cike da nishadin halayar Baba Lauratun, ita bata ga abin sakawa kai damuwa ba a lamarin mam da duniya, yadda ya zo maka kawai ka je da shi mana in ba rigimar Baba ba? Hajia dai ba za'a ce mata muguwa ba, mutun ce dai mai hali irin na son kai a lamuranta da son kare mutuncinta ta kowace hanya, aman daidai gwargwado tana kyautata maka , rayuwar nan kuwa ai kowani bawa da kashinsa a kulle a mararsa ne, na wani ya fi ma wani, yau ita gani take ko me Hajia zata yi daidai da ita ne, ai masu gidan rana take rike da su, wa'inda sunne damuwar da yawa a yau
Da haka sukaiwa Baba lauratu salama suka nufi gidansu a yanzunma ita da useini ne suka rike bokicin shi kuwa sarakin yana tafe yana sake daure fuska kai kace an masa wani laifi ne
Hankalinta kwonce ta idasa bude gidan nasu bayan sun gaisa da mai kantin kofar gidan sannan ta tura da adu'a a bakinta ta shige ta dakata har suka gama shigowa sannan ta mayar ta rufe gidan sosai da makulin ta ciki kafin suka karasa shigewa cikin
Gidan da tsaftarsa kamar yadda ta barshi, sannan komai a kilace yadda ta bari, cikin nutsuwa ta duka a gaban Hasan ta zuba masa ido tana kallon yadda ya zauna a cikin rana yana hararan wani wajen daban, ga zufa dake tsatsafo masa, bayan dan uwansa tuni ya cire takalmin kafarsa ya kilace ya nufi bayi dan yin wanka kamar yadda suka saba
A hankali ta ce" Menene yarona?"
Hasan ya maido dubansa saman fuskarta ya kafeta da ido yana kallonta, cen da ya ga dama ya budi bakinsa ya ce" Mama, me yasa kika cewa Aban baban gida da mai napep din dake kaimu makaranta bayan yace direba ya ringa kaimu? "
Tsuru ta yi da ido tana kallon yaron tare da tunanin amsar da ya dace ta bashi, amsar da ba zai yi mata kallon tana masa karya ba, sannan ba zai riketa da wani abin a zuciyarsa ba, ko ba komai Hasan fa yaro ne wanda zai iya kallon du wani wanda zai tauye jin dadinsa a matsayin wanda baya sonsa, ko wanene kuwa, dan haka itama sai ta zame ta zauna a cikin ranar tana kallon fuskarsa, muryarta a sanyayen ta ce" Fadeel, ranar da kace abokinka ya matsawa byronka, kulun shi sai ya ara yana rubutu da shi, kai ka gaji ya isheka me yasa kace haka?"
Yaron ya sake zuba mata ido yana tuna irin takurawar da Abokin nasa ya masa a aji, da farko shine da kansa yake ara masa dan taimakawa, daga baya sai ya zamto kulun kulun sai ya daukar masa byronsa, bayan shi kadai ne da shi , wani sa'in shi da abinsama aman sai ya jira abokin nasa ya gama anfani da shi kafin ya bashi, dan haka yace" To mama shi kulun kulun sai ya amsar min abina, bayan shima yana iya fada a gida a siya masa , ranar fa budewa ya yi ya hura shi gaba daya byron ya lalace sai da Malamarmu ta cenzan wani, ta bashi wani dan ya shafa min lafiya, aman a wasge garima yace wai na bashi, ni kuma na kiya!"
Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" To me yasa zaka kiya bayan abokinka ne?"
Da mamaki yake kallonta ya ce" To kuma shikenan kulun sai ya amshe min ? Ni kuma fa?"
Amina ta dan dage kafadunta ta ce" Ka gani Hasan, to kamar haka ne na hasaso a kan maganar motar da Baban baban gida yace a ringa kaiku school, sai nace da ace tawa ce sai ina kaiku kulun kulun, idan na zo na saka rai da motar zan zamto bani da wani anfani har na saba kulun kulun ana kaiku, idan direban ya gaji ya daina kuma yaya zan yi? Wa zai dawo kai min ku ba tare da kun yi lati ba? Shi yasa nake kaiku ina dawo da ku".......
Fadeel ya ce" Aman Mama, a gidan na baban gida motocin ai ba daya bane, ki dauko daya mana ki koya ki ringa kaimu?".........
"Aman Fadeel kana so kace min na je na dauko motarsu na ringa maku anfani da shi bayan ba ni na siya ba?" Ta fada tana sake kallonsa tare da auna irin yadda yake daukan maganar a saukake ba tare da ta rikita tunaninsa na yaro kamarsa ba, duda Hasan din nata yana da shekara takwas ne aman wasu abubuwan idan ya yi zaka dauka ya rufe goma ko ya haura ne, domin shiru shirun da yake yawan yi a yawancin lokuta yakan auna abubuwan dake zagaye da shi ne, dan uwansa ne mai zuba surutu ko ba ma'ana
Hasan ya girgiza kansa sai kuma ya ce" To ke yaushe zaki sayi taki Mama?"
Wannan karron har wani dan murmushi ya subuce mata tana kallonsa da manyan idannuwanta ta sake wara hannayenta tana tunanin in ba yarinta ba yau rigimar Hasan a kan mota ne yake yi? Ta ce" Zan siya idan Allah ya hore min , na ringa saka ka a ciki ina yawatawa da kai da izinin ubangiji, wai Jaririna kana adu'ar da nace ka ringa yi kai da dan uwanka kuwa?"