← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 83

Sashe 5

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagowa ta yi ta karra daukota da kallo ta watsar, yin turancinta ba shine abinda zai sa ta sasauta mata ba , ta tabata turancin an koye shi ne a boyi boyi ko a titi , watau turancin tsakiyar titi ba na makaranta ba, dan haka ta dubeta ido cikin ido ta ce" Oh kennan kina gane abinda nake fada, ohk ki yi gagawar aiwatar da abinda na fada tun kafin lokacin zuwa sallar oga ya yi ya sameku a wajen nan!"

Amina ta saki hannun Hasan ta matso daf da matar ido cikin ido ta dubeta sosai ta ce" Idan ban aiwatar ba fa?"

Matar ta kalleta da mamaki, ta kalli mutanen da suka dan fara kawo hankalinsu kansu ta dan matsa dan bata so jikinsu ya hadu ta ce" Ke, ki matsa min kadan mana baki san ana fama da cutar covid bane? Idan kika ki kuma sai ki tafi ki barsu a nan na mika su hannun masu horar da barayi!"

Da karfi Amina ta janyo atishawar karya ta maka mata sannan ta ce " Bismillah ki mika mu gaba dayanmu wajen masu horon tunda azalumai ne ku!"

Hankalinta tashe take goge fuskarta da tissu tana fadin maza a kira mata security service!

Jin haka ya kara tunzura Amina ita kuma ta shiga ihun wanda ake gudun ta gannin take son gani, da karfi ta ce" ba kina tsoron kar hankalinsa ya karkato wajenki ba? Shine zaki wulakantamu ki kirayi y'ayana barayi? Na san ke da gani baki san menene yaro ba baki san ciwonsu ba tunda ga dukkan alamu ko mage bakya ciyarwa! Na tabata shi din idan har datijon arziki ne zai maki fadan kira min yayana da sunnan barayi da kika yi!"
A haukace Amina da nake yiwa kallon ko dan yatsana na saka mata a bakinta ba zata taba cizawa ba ta shiga watsar da dukkan abinda hannunta ya kai ta nemi haukacewa a wannan waje har daidai lokacin da secirity biyu suka shigo mata da sauri suka nufota daya ta samu ta damketa sai dai juyin da ta yi da ita ta kubce mata har ta nemi yin taga taga , hakan da suka gani ya daka dayar janyo bindigar teaser dinta ta nemi kashe gaban jikin Amina a lokacin da ta danna zata dora mata shi a lokacin Husain ya gantsa mata cizo a kafarta yana kukan kokowar da ake yi da mamansa , Hasan kuwa yana tsaye wajen mutumen nan da yaren turancin dake harshensa wanda su dukansu sun yi mamakin yaron dama haka yake da turanci a bakinsa yana fadin ya hannasu taba mamansa shima yana daf da fashewa da kukan da idan ya fara ta yiwu yin shirunsa da hakurinsa sai ko zuwa gobe aka danna baban office din da ogan wajen ke ciki da bakonsa da kuma likitansa da ya zo bashi magani domin a yau ranar da ya bi sosai ta bale masa habo har sai da ya yi kiran likitan dole

Docter Mansur , likitansa kuma daya daga cikin abokinsa ne ya ga za'a jonawa yarinyar nan abin nan dake saka mutun yin bori a kasa kamar dan jaki kafin gaba daya jikinsa ya mace har fitsari ake saki fa da sauri yana fadin" stop that immediately!"

Da sauri ta dakata tana kallonsa hadi da dan ja baya domin babu wanda bai san waye shi a wajen ba, da sauri ya dan karaso yana fadin" Subahanalah, me yake faruwa haka a wajen nan , hey boys me yasa kuke kuka? Hey saketa mana, ki saketa menene haka?" Sai kuma ya juya wajen babar mai kula da harkar cctv din ya shiga tambayarta abinda yake faruwa

Kafin ta bashi amsar da zata gamsar da shi Amina dake share idannuwanta da suka cika da kwalla tana tare hijab dinta da aka yaga mata ta dube shi muryarta a shake ta ce" Dan girman Allah ina son gannin mai wajen nan, na yi rantsuwar ganninsa a yau kar kafars ta kamani, idan har ka san inda yake ko kana iya min iso ka taimaka min na ganshi"

Kallonsa Mansur yake yi sannan ya dake kallon yaren dake kuka sunna rike hijabinta , sunnan da suke kiranta da shi Mama ya saka shi sake kallonta kafan sai kuma ya juya wajen da aka yi cirko cirko, a dan hade kadan ya badu umarnin kowa ya koma bakin aikinsa, sai kuma ya dake dubanta a hankali ya ce" Ina fata lafiya? Domin bashi da lafiya ne"

Amina ta hadiyi yawu dake makogwaronta a hankali ta furta" Lafiya lau"

Kofar office din ya nuna mata sannan ya juya wajen ma'aikatan da wace ke son nuna masa bai dace ta shiga haka kanta tsaye ba, bata da damar ganninsa kai tsaye haka bale ba abin kirki ne zai kaita ba , zuwa ne zata yi ta masa rashin kunya may be fiye da haka, sa sauri ya juyo dan idan har maganar cewa rashin kunya ne zata shiga ta yi a office din cen gwara ta zo ta yi wasan kurar da suke yi da kowa a wajen nan ciki kuwa harda shi, domin idan har wata magana marar dadi ta faru a cikin cen daga bakinta bai san me zai faru ba, du inda kake neman dan zafin kai mai tsutsotsin kai idan ka zo kansa ka ja ka tsaya ka dasa aya

Sai dai ya makaro, bayanta kawai ya gani d ƴaƴanta dake biye da ita sun kutsa cikin office din
Juyowa ya yi dafe da gaban goshinsa ya rasa abinda zai ce, sai dai ba zai bar wajen ba sai ya ga abinda zai faru dan baya so a samu matsala ya barsu da rigimarsa su kadai

Da karfi ta bude wajen sannan ta kutsa kanta da salamar da ta zamto tarbiyar bakinta ta shiga baza ido dan ta ga abinda ta shigo nema watau mai wajen

A hankali ya dago lumsasun idannuwansa ya sauke saman kanta da ƴaƴanta dake ta faman rike gefe da gefen hijabinta, tunda ya mike dan takawa bakin da ya yi da sauri ya dawo sanadiyar ihun kukanta, kansa tunda ya sarra yake tare hancinsa dan yana gudun wani habon ya same shi

Wayar da yake yi bai katse ba haka kuma bai daina kallonta ba da yarenta dake kallonsa suma

Da haushi ta sake kureshi da kallon raini, a ganninta idannba wulakanci irin na y'ayan masu kudi ba ta yaya za'a maka salama kana kallon mutane ka kasa koda amsa amincin da aka nema maka a wajen ubangijinka? Baki ta tabe ta ce" Ban san ko kana jin hausa ba fan saurayi? Ama dan Allah mahaifinka ko mai gidanka nake son gani, watau mai kampanin nan! "

Kallon da yake mata da kuma dan juyar da kansa da ya yi ya waiwaiga hagu da damansa ya sakata bi itama da kallo, sai ta sake dubansa ta shiga tunanin ko kurma ne?

Da wani bacin ran ta budi baki ta ce" Bawan Allah shin kai kurma ne? Ko kana daya daga cikin masu wulakanta mutun a wannan kampani? Koda yake kasancewarka a wannan kujerar ta yiwu kai din makusanci ne ga mai kampanin, ka fada masa cewa Allah ya halice shi, shi ya halice mu, ka fada masa cewa babu wanda ya san gobe sai Allah, idan da sanninsa ake wulakanci a karkashinsa Allah ya saka min wulakantani da aka yi har aka zagar min y'ayana!, Idan ba da sanninsa ake yi ba ya gagauta yin bincike ya tace ya rauraye! Wadannan din y'ayana ne! Yayana ne ! Ba bara.........."

Idannuwanta ta rintse sai kuma ta bude ta dora da fadin" Ba barayi bane su, ina kafa kafa da abina, ina kuma fadawa Allah, yau koda sun iya hali irin na bera idan har an san ciwon haihuwa za'a kiyayi zaginsu da shi, idan kuma an san gobe ta Allah ce za'a kiyayi aibatasu da laifinsu na yanzu, domin laifin wani na iya kasancewa laifinsa na gobe!, Bai san me zai zama gobe ba, idan har shi din magidanci ne da ya san menene haihuwa to fa zai kiyaye ya saka tsari a tafiyarsa.....ka fada masa ni din uwa ce da hawayena ke zuba na ciwon wulakantamin y'ayana da aka yi, na san kai baka haifa ba bale ka sani dan girman Allah sak...................................."

Dif ta dauke wuta a lokacin da ya mike daga cikin kujerar da ya lume ya tura kafafuwansa cen kasan tabel din office din , ashe irin zaman nan ne ya yi wanda ake tura kaffafuwa karkashin table a dafe kujerar, zama ne na masu tsayi ba gajeru ba gaskiya, shi yasa sam bata gane tsayinsa ba har sai da ya mike a yanzu

Idan har ya mata magana a iffice din nan to fa takardun dake zube saman table dinma sun masa

Wajen wayar tafi da gidanka ya nufa ya daga ya karra a kunnensa dannan ya shiga dadana numbobin da yake sin kira

Cen kasan makoshinsa ya iya furta" EH " sannan ya ajiye ya kuma juyowa ya jinginar da bayansa jikin garun ya sake fuskantarta yana sauraronta

Shiru ne ya dauki wajen, sosai shiru ana kallon kallo

Kasa kasa Husain ya ce" Mama mu tafi kar ya zane mu "

Hasan dake masa kallon da yake masu ne ya sake jan hijabinta yana fadin" Mama lets go please"

Lebenta ta dantse cike da takaici, ta fa gane ba kurma bane tsagwaron wulakanci ne irin na yaren zamani, idan zata rantse ba zata yi kafara ba ta tabata wannan din ta girme shi nesa ba kusa ba, rashin kunya baya karewa a duniya!
Juyawar ta yi, ba dan komai ba sai dan ta san ko menene uban gidansa ya jita!, Ta bar wajen ne dan ta kare mutuncinta, abinda ya so faruwa dazun ba zata so ya tabata a kanta a gaban ƴaƴanta ba, abin nan ta ji hirarsa a wajen yan school dinsu, tabas a dazu ta tsorata da ta ga za'a dasa mata shi

Gana take sunna biye da ita har suka idasa sauka

Bata tsaya ta kula kowa ba sula nemi ficewa a baban filin kampanin har an fara kiraye kirayen sallar magariba
Chapter 5 · 0% Book details