← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 83

Sashe 7

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kujera yar tsuguno ta mika mata tana mata murmushi ta koma ta ci gaba da toya wainar matar Mai shanu domin ta gama tashi tuni ta zuba a kwanon nan ta kilace

Murmushi Innar Sauda ta yi tana fadin" Oh Amina ke kam jinninki ya hadu da mai gidan abanku, bayan kasa ta birni idoma bai yada ke ba, da ba dan Baba Mai shanu ya tsufa sosai ba ai da aurenki ya yi ya cencaneki sosai, ama yanzun idanma ya aureki anya zai iya da ke?"

Amina ta dan katse zuba kulin ta kalleta da dan mamaki, sai kuma ta yi murmushi bata ce da ita kanzil ba ta ci gaba da zuba kulin wainar

Haushi ne ya kamata a ranta tana ayana ' shegiya mai shegen taurin kan tsiya, maganarma ba zata yi min ba dan bakin hali!'

Murmushi ta yi a bayane ta ce" Um, maza? Maza? Kin ga tunda na gama sallah na zo na tsaya nake jira ki gama ki bude dan na shigo na amshi wainar naj sadaka na ba yar nan, ki duba ki ga abanta a jiya naira ashirin daya da ya banu tun safe bai kuma waiwayarmu ba, wannan lamari na maza da me ya yi kama? Namiji ba kama gida, ba fara'a idan ya shigo gida bamu isa mu yi wata walwalar ba sai idan ya fice, shi kulun a babu yake, ko so yake na je wani wajen na samo mana ne?"

Amina ta zuba masu wainar isashiya ta miko mata harda miyar da ta sha kayan hadi na gargajiya sai kanshi take a hankali ta ce" Allah shi kyauta"

Maman sauda ta amsa tana ajiyewa gabansu da yin godiya ta ce" Ke kika san Allah shi kyauta, wai shine harda yin budurwa a cen bayan layi, ai nace ba damuwa ta kula shi idan har ya kawota sai mu ci idonmu baki daya"

Amina ta yi murmushi tana idasa zubawa a kwanon Matar mai shanu ta kilace shima sannan ta zauna tana gadin miyar har ta daidaita ta zuba masu isashiya a dayan kwanon ta hade komai a cikin kwondon da take mika masu ta zubawa biyu suka zauna sunna karyawa sannan ta shige wanka

Da ta fito ta shige ciki ta cenza tufafinta cikin shigar riga da sket na atampa ta zurmuka katon hijab dinta mai ruwan kasa har kasa mai hannuwa ta daka dan kwali sannan ta dake fitowa jin ana salama

Ummu salma ce ta zo tambayar gyaran amarya , nan suka yi magana suka gama ta tafi harda bada rabin kudin
Innar sauda kam kallonta kawai take yi, gata dai baka ce ita ama ko ita ta fita kyan gani, ita da kanta tana matukar kaunar kalar fatar Amina, ga shegen nutsuwa da dan uban miskilanci du yadda ka so ka daki cikinta ba zaka samu abin fada ba sai dai ka gaji ka hakura,

Tare suka fito daga gidan na Amina ta rufe komai suka yi gaba neman abin hawan da zai mikasu gidan mai Shanu, da kallo ta raka su har suka bacewa ganninta, Tsaki ta ja a fili a ranta kuwa tana ayana' Yarinya karama ba miji ba komai aman ta gaje komai na anguwa, idan gyaran jiki ne ita, kitso ita, komai ita, kowa mutunci yake da ita! To walahi baki isa ki shiga gidana ba ki hanna min zaman lafiya da kwonciyar hankali da rawar gaban hantsi a gidana!'

A hankali ta mikawa mai adaidaitar kudinsa tana kallon kofar baban get din da aka wangale ba'a rufe ba

A nutse suke tafe yarenta na rike da wasu kayan itama tana rike da wasu suka wuce baban get din sula gaisa sosai da mai gadi sannan suka dauki bangaren Baba Mai Shanu

Wani irin ja ta yi ta tsaya a lokacin da idannuwanta suka sauka a fuskar yaron nan na jiya wanda aka wulakantata a kampaninsa ta kai kara ya mayar da ita yar iska dan rainin wayo ya fito daga cikin wata galeliyar mota ya ja ya tsaya yaba karewa gidan kallo jikinsa sanye da dakakiyar shada ruwan sararin samaniya sai haska ido take fuskarsa daure yana kallon wani gayen dake masa hira yana ta nunawa yana dariya ama shi sai binsa da kallon nan na raini yake yi baya bashi amsa

Mutuwar tsayen da ta yi na yan sekwani ne da sauri ta juya da nufin komawa

Husain ya kalleta ya ce" Mama ina zamu je?"

Daburcewa ta so yi sai kuma ta juyo gannin Baba direba ya taho da dan sauri hannunsa rike da wata jaka ya wuce su fuuuuuuuu yana sauri gaisuwarma sama sama ya iya yi mata ita

A hankali ta ce" Baba ko dai yau Baban baya nan?"

Baba direba ya ce" Yana nan yana ciki fa, jikansa ne ya zo yau ai ba kanta ki taho mana"

"JIKANSA?" ta furta a saman lebenta, ta taho?
Ta sake tambayar kanta,

Abinsa ya faru a jiya ya dawo mata sak sak , irin abinda ya faru ya dawo mata, kwarai riketa da kokowar da take yi a kan idannuwansa ya koma ta kuma bishi ta dora daga inda ta tsaya

A hankali ta rike kwondon da kyau a lokacin da ta ga ya juyo barin fa suke da nufin shigewa ciki

Dan kallon second daya takk ya maka masu mai shige da harara ya dauke kansa ya shiga tatakawa ya shige ciki

Da ido ta raka shi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce"
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️

*NA*

*SAJIDA NIGER*

Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida

Wannan Novel na kudi ne ba free bane

Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER

Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai

Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka

*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*

*Page 0️⃣5️⃣*

Da ido ta raka shi, kasa kasa ta ja tsakin jin haushi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce " Kumu je mu ba Saliss gayacen ya kai sakon Baba, yau bakine da shi ba zamu shiga mu dame shi ba"

Gaba daya yaren basu so hakan ba, bama kamar Hasan, du miskilamcinsa da rashin son mutanensa sunna shiri sosai da Baba, koda yake baban ne datijo mai datako da iya mu'amalantar mutane kala daban daban, yakan zauna da Hasan ne da irin mood din da ya zo masa, idan yan hirar ne su taba kadan ana nasarwa, idan yan a zauna a kalli junnan ne sao su wuni a haka bai ce masa ufan ba, to shi da ya zauna da jikansama suka yi zaman lafiya bale hasan jariri, ga dai jikan nasa a yanzu ya kawo mizalin da ya dace ace ya ajiye iyali shima ya yi nasa gidan da mace zata dora tukunya ta masa sannu da zuwa idan ya dawo daga nema, ama sai gidan ba macen a ciki, shi gana dayama tale takensu da kakarsa ba wani dada yardarsa da kasa suka yi ba, ya dai zuba ido ne yana kallonsu

Gaba daya sakon ta ba daya daga cikin yaren dake aiki a gidan wato Saliss suka yi tafiyarsu tare da yaren

Salis ya nufi baban falon Mai Shanu ya yi salama sannan ya ja ya tsaya daga kofa, domin ya san yau madame na wajen ba zai so ya shige kansa tsaye ba ya samu matsala

Mai Shanu dake zaune cikin sasaukar shiga ta hausa , lalausan yadi kansa sanye da hula ya sake waigowa kofar yana fadin" An amsa salama malan Salisu ka ja ka tsaya ka shigo mana?"

Salis ya daga labule ya shiga da salama a bakinsa a karro na biyu ya karasa direcy gaban Mai Shanu yana kokarin dukawa da kayan dan ajiyewa wata murya mai cike da nutsuwa, furuci kasa kasa sosai, cike da cikaken aji da wayewa ta furta" Ka kai dining mana kar ka ajiye a nan"

Mai Shanu ya dubeta sai kuma ya kalli Salis ya ce" Aa ya ajiye min a nan, wannan kamar kanshin Wainar maman biyu?"

Salis ya ajiye din kansa a kasa sosai ya karra nutsuwa ya ce" Eh itace ta ajiye ta koma tace zata mika biyu makaranta ne"

Dan jim ya yi sai kuma ya gyada kansa yana furta" ALLAH ya anfana, ya saka da alkhairi, ya yi mata albarka"

Salis ya ringa amsawa sannan ya mike ya tafi

Bayan fitarsa da kamar minti biyar Hajia ta kuma dagowa ta kalli mijinta a karro na hudu tun bayan maganar da ta yi ya take ko kallo bata ishe shi ba, ya wani kama yiwa yarinyar dake aikata aikin nan da kudin da yake tura mata godiya kamar wace ke ciyar da shi sadaka! Kanta ta cire ta maida kan Jikanta, abin kaunarta , farin cikin zuciyarta , abin alfaharinta taba cire gilas din karin ganninta hadi da ajiye jaridar hannunta ta ce" Cencenta ce ke nemanka ido rufe , ba kai bane ke nemanta *ABDUL RA'UF!*"

Sau daya ya dago daga rubutun da yake yi a wani litafi ya sauke dubansa a kanta, sai kuma ya dauke dubansa ya maida cikin litafin ya sake dasa alkalaminsa ya dora daga inda ya tsaya
Chapter 7 · 0% Book details