← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 83

Sashe 20

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai a tsaye take tana dauraron Baba har ta gama maganarta, haka kawai sai ta ji fargabarta na neman karuwa a kan tunanin abinda ya da suka zo nan, tana jin dadin yannayin wajen sosai, ama jiki sukuku ta karasa ta karra dukawa tana sake gaishe shi

Mai Shanu yana murmushi ya ce" Uman biyu rabonki da ki min waina tun ta ranar juma'a, yanzun kikan ki yi min wainarma , bayan ni din ina son waina sosai"

Murmushi take yi kasa kasa ta ce" A yi hakuri baba zan yi mai yawa , har sai kace ka koshi "

Shima dariyar ya yi yana sake gyara zamansa ya ce" Yauwa, dangane da maganar wajen uncle dinki ne, yau kwaba uku kennan da na je na same shi ni da Malan Liman "

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ta kai zaune zuciyarta na saka mata abubuwa kala daban daban, baban fargabarta kardai yayan mahaifin nata ya yarda ta koma gidansa, shin yaya makomar rayuwar biyu? Tsoro da fargaba irin ta uwa ke darsuwa a zuciyarta, tunaninta ya kafe ya tsaya a kan murmushi da dariyarsu da ta barsu sunna yi yanzu, idanfa ta koma kuka a gobe?

Baba Mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya bayan ya hada abunda ya dace ta sani, ko ba komai ba zai saki baki ya yi ta yi mata bayanin abinda babanta ya fada ba, koda tana yarinya ba zata taba jin dadi ba, sam bai ga anfanin aikata hakan ba
Dan haka ya ce" Sharadinsa daya ne tak a kan maganar zamanki a wani wajen, shine ya kasance kuna daure da auren wani a kanki , ki tare a dakin mutumen"

Yanzun kam da sauri ta dago ta kalli Baba, dara daran idannuwanta masu dogayen gashin ido take ta kiftawa tana kallon Baba, sai kuma ta sake sada kanta

Baba na hankalce da dukkan yannayinta ya ce" Harma ya bamu adadin kwanakin da ya diba bisa adalcinsa cewa nan da sati daya tak, watau nan da kwana hudu, Amina idan baki manta ba na yi ramtsuwar cewa ba zaki koma gidan nan ba, ban sani ba ko ni zan yi ta yin azumin kafara? Ko kina da tsayaye ne?"

"Tsayaye?" Ta fada a hankali still tana kikifta ido tana kallon Baba

Baba ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa tsayaye, wanda kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura, wanda ke zuwa wajenki kika ji kin aminta da son aurensa"

Gaba daya sai ta afka a duniyar tunani, Aure? Ita? Nan da kwana hudu? Mutanen da suke tsayen da alamun sunna sonta biyu ta sani a duniya, Aban saudat da kuma Muktar, su din nan su ra sani a sanninta, sai dai bata karasa tunanin nan ba baba ya ce" Lauratu ta min maganar manema aurenki biyu, tun a washe garin da rigimar nan ta faru, Malan Liman ne da kansa ya tuntube su, su dukansu sunna da ra'ayin hakan, sai dai shi daya lokaci ya kure masa duda an nuna ba yanzu tarewa ba, dayan kuwa mahaifiyarsa ce ta yi karan tsaye kan lamarin, bayansu akoy wani ne?"

Yanzun kam da hannayenta take dan watsawa, naman gaban goshinta na cakudewa a birkice ta ce" Aa, dama, dama su kadai ne suka ce, suka ce zasu aureni koda da biyuna, suka ce sunna son biyu, bayansu babu kowa"

Dan murmushi ya subucewa baba, domin ko a yanzu baba cewa ta yi ba sai ya ji ra'ayin ko tana da wani ba kawai abinda ya yanke a zartar, shine yace da ita lalalala, ko daya ba zai so ace tana son wani ya katse hakan ba, ya fi so ace bata son kowa idan ya so su shirya kansu a gidansu

A tausashe ya dubeta ya ce " Amina, idan babu, shin kin yarda ni na zaba maki miji, mai nagarta, wanda zai kula da maraicinki, ya rike yan biyunki, da ke kanki? Ina nufin zaki amince ki yi min biyaya kuwa? Idan har bakya jin zaki iya yin hakan ba zan ga laifinki ba, zan je na fara daukan azumin rantsuwar tun gobe, na san zan jure, ulcern tawa ai zata yi hakuri na yi ibada kar tsoho ya mutu ya je da bashi a kansa"

Idannuwanta da suka cika da kwallah ta zuba masa, nazartarsa take yi , karara ta ga lalle da gaske yake, magangannun Baba suka fado zuciyarta, tsoro da fargaba suka shigeta, ta yi shiru ta rasa amsar badawa, hankalinta ya ringa neman karra tashi har sai da Baban ya kuma budar bakinsa a sanyaye ya ce" Amina, shin zaki iya yi min biyaya kuwa?"

So take ta tambaye shi waye zai zaba mata? Ko baba direba ne? Ko mai ba shukoki ruwa ne? Ko Usman dan albarka ne? So take ta ji ko wanene, ama girman kunya irin ta cikakiyar budurwa ya danne curiosity dinta, kanta na kallon kasa a hankali ta daga kanta, sai kuma ta bude muryarta bakinta na rawa ta ce" Baba, zai, zai kular min da biyu? Kar kar ya min irin na mijin mamansu, kar sai ka daura auren yace ba zai rike yayan wani ba"

Tausayinta zallah ya kama baba, ya kuma yi mata murmushi ya ce" Bari ki ji, bi izinillah zai rike biyu, ke da da hali harta tarkardunsu sai sun koma da sunnansa a kai, ni nan bani da haufi a kan haka, burina dama ki amince, domin na yanke hukuncin a gobe da yama zan daura aurenki bisa wasu abubuwa da suka bilo da take dokata da wace nake tunanin na isa da ita ta yi, ta manta cewa itace a kasana, *ITACE ZATA YI MIN LADABIHHH!*, dan tsufa ya kama ni, sannan na kasance mai son bata damarta na dan Adam mai daraja, har take son wulakantani da yi min bazawar sirri a kan abinda yake *MALAKINS?*, inada iko da dukkan *BAIWAR* da Allah ya bamu, bata san na fi mai rike da bulalar iko ba!, Tashi ki je Uman biyu, bana son kuka ko damuwa, ki shige dakinki ki yi alwallah ki fadawa Allah, yau Lauratu a wajenki zata kwana, Allah ya maki albarka"

Idan ta iya budar baki tace ufan to fa takalmintama da ta saka a jirge ta nufi motar ya yi godiya ko ya yi magana, tunda suka shiga motar kuwa kanta a sade yake bata iya dagowa ba har suka karasa ta kuma ficewa ta nufi falon

Tana budewa ta ga wasu mata biyu zaune sunna zantawa
Ido hudu suka yi da junna, hakan ya sa ta duka har kasa ta gaishe su sannan ta mike ta nufi ciki

Tana nan zaune Baba ta iso itama dakin ta zauna ta fuskanceta ta shiga tambayarta yaya maganar gyaran jiki?

Da mamaki ta kalli babar, gyaran jiki? Wani irin gyaran jiki? Na me? Lallema baba ta iya hade hade a rayuwa

Bata ce mata komai ba, dan ta san ta gama sannin komai, abinda ta so ta ji wanene a cikin ma'aikatan gidan? Dan a yanzuma da ta fito ta ga baba direba sai kallonta yake yi yana murmushi, ko dai shine? Ama ba zata iya tambayar ko babar ba, kunyarta take ji walahi

Alwallar ta dauro ta dawo ta shiga gabatar da sallar magariba , a kan salayar bata tashi ba har aka yi isha'i, kai na takaice a nan harta abincinta nan ya iskota ta dan tsakura ta rufe shi ta ajiye gefe domin burinta ta dauki azumi goben! Ko menene ke shirin tarban rayuwarta Allah ya sa alkhairi ne, ta kasa gaskatawa, ashe itama zata yi aure? Aure fa? Gobe gobe? Shikenan shi babanta bashi da ta cewa kennan? Idanma waye a bata? Anya Baba dan iya zai iya bada y'arsa haka?

Cire komai ta yi a ranta ta ci gaba da adu'arta

Masu jiran Baba kuwa kowa sai kama wajen kwonciya ya yi ya kwonta, domin bai shigo gidan bama bale su hadu da shi

___________________________________

Washe gari

Jirgin karfe tara ya sauka da shi a kasarsa ta haihuwa
Yana samun ntwrk din kasarsa ya shiga kiran numbar baba da layinsa na gida

Abin mamaki tana yin ringin aka daga, kuma muryar baban ce

A tausashe baba ya ce" Ga dukkan alamu ka sauka Baban mutun?"

Abdul Ra'uf ya sauke ajiyar zuciya jin muryarsa ram ya ce" What happened with u? Shin me yake faruwa ne? Ina Hajia?"

Baba ya ce " Tana gida"

Abdul Ra'uf ya ce" Kai kuma kana ina?"

Baba ya ce" Yanzun dai na fito daga kasuwa ni da Malan Liman siyan goro, mu hadu a gidan dan nima cen na nufa ai"

Yana gama fada ya katse kiran yana ta adu'ar da Liman ya karra bashi har suka karaso gida

Gannin motocin Abdul Ra'uf din ya tabatar masa cewa ya karaso, lalle ya zaku ya ga kakarsa yar rigima

Murmushi ya yi yana gyara babar rigarsa dake baza kanshin misk hannunsa rike wayarsa da kuma carbinsa ya doshi falon kansa tsaye

Yana shiga mutanen da ya gani sai da bin ya so bashi dariya, haka kuma irin yadda ake nuna jimamin ba'a ganshi ba ya sake bashi dariya, kamar ya bace din nan?

Shi dai da mutunci ya gaishe su, sannan ya karasa wajen abokinsa da ya sake zuwa da sasafe dan jin idan ya dawo gidan

Hannunda ya kama yana fadin" Mu je saman mana Elhaji, na san Abdullahi ya karaso ko?"

Du yadfa suka so dan fara dannarsa kowa sai ya yi shiru suka haura saman
Chapter 20 · 0% Book details