← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 83

Sashe 27

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ya tausasa muryarsa aa tunaninsa, sannan ya yi iya yinsa dan gannin bai wulakanta lamarinta ba, cikin nutsatsun lafuza ya ce" RISALAH, da ni, da ke, da dukan wanda yake tare da mu bamu isa mu zanawa kanmu komai ba, munada ra'ayinmu da muke iya nunawa da karfin ikon da muke da shi a hannayenmu, a tunaninmu!, Bamu san komai da gobenmu ba, gaibunmu ne, ki kasance iyalina ko akasinsa ban taba zama da ke na maki alkawarin zan aureki na rayu da ke ke kadai ba, wannan kuma damata ce, ni a yanzu bani da isashiyar lafiyar da zan iya bi maki komai daki daki...................."

Ya dan dakata yana kallon reaction dinta da son sake fashe masa da kuka, a hankali ya ce" Hey, hei RISALAH saurareni plz..........."

Kanta ta langwabe tana kallonsa , dan murmushi ya yi mata a hankali ya ce" I love u too "

Kanta ta karra langwabewa sosai tana kallonsa da son gaskata maganarsa

A tausashe ya sakar mata da murmushin da ya sakata lumshe idannuwanta da jin tamkar zata dira ta fada masa ta rukunkume shi dan kauna da soyaya, yakan jima bai furta mata kalmar soyaya ba, yawancin lokuta idan ta furta masa yakan ce da ita "ME TOO", Du idan yace da ita I Love u takan adana maganar a kuryar dakin zuciyarta ( kar wanda ya ga laifinta, so ne fa, so ne mai tsanani, wadda na tabata babu wace batada wanda zuciyarta ke yiwa irinsa, sai dai wata ta iya danne shi, danne shin da hanna shi falasa baki dayansa shine alkhairi, domin zamanin namu ne ya zo da kalar gigitarwa!)

A hankali yana kallonta shima ya ce" Zaki yi hakuri ki je gidan har na zo?"

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta waiga barin da Mansur ke zaune ta ga gefe daya yake kallo bayaa ko kallonsu, shi yasa mutumen ke birgeta, kuma Allah yana gani a duniya shine mai taimakon soyayarta da ABDUL, domin wani lokacin ABDUL kan cireta kwata kwata a rayuwarsa, idan ta kama Mansur da kuka sai ya shirya su, ita kam da yau zata ga yarinyar nan da aka ce an aurawa mijinta da sai ta shake wuyanta ta kasheta , sai dai itama a kashetan!

A hankali ta daga masa kanta, dan ta san tunda yace zai zo din, to fa zai zo din ne, kuma ta san idan har ta saukar da kanta kasa suka yi magana to fa tabas zai saki yarinyar nan, dan itama ta san yana sonta

Mikewa ta yi tana jan hijabinta da kyau stiilll tana kallonsa

A sanyaye ya ce"
*NZL PAGE1️⃣7️⃣*

Ya dan karra kamar minti goma yana sake amsar kalaman soyaya har ya ji kansa ya fara daukan caji sannan ya mike da niyar tafiya

Kamar yadda ya saba baya zuwa gidan bai bar kyauta tautunci mai saka farin ciki ba hakan ne yauma, ya ajiye chek ba dan sunna cikin rashi ba ko wani abin, ya sabarwa kansa irin haka ba dan a so shi dan hakan ba, sai dan ya kasance mai yin kyauta a kowani hali, ba iya su yake yiwa irin hakan ba, nasun dai na zuwa ne da karrin jadada mutuncinsa

Har bakin mota ta rako shi, bayan ya bude ya shiga baya ya zauna ya waigo barin da take tsaye tana murmushi
Murmushin ya yi mata a hankali ya ce" Kin tabata kin daina maganar shagon ki?"

Sai da ta yi dan tsai, sai kuma ta gyada masa kai da sauri, dan ta san ko menene mahaifiyarta da ta fi kowa tsayawa kan maganar neman na kai ta kuma aikata haka da dalilinta, ta tabata ko menene zata samu gamsuwa idan ta koma yanzu, dan haka ta amsa shi da kwarai hakan ne

Murmushi ya yi a hankali ya furta" Good night an mata"

Itama murmushin ta yi ta ce" I love you My Man"

Sai da ya lumshe ido da kalar nasa salon sannan ya furta" Me too"

Daga haka ta ja baya kadan suka tayar da motar suka fice da mota uku cif masu kudi na garari, yana tafe da yan rakiya ne dan ya tabata zasu cika dare a yawo yau, domin daga nan kauye suka nufa da daren nan kuma a cen zasu kwana

Tana tsaye sai da suka bacewa ganninta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya tana murmushi, sai kuma ta cire hijab din tun daga tsakiyar gidan ta shiga dan gudu gudu ta shige falonsu
Hango mahaifiyarta zaune da chek din da ya ajiye a gefenta ya sakata karasawa da gudu ta rungume maman nata ta baya tanaa daria ta ce" Thank you mama, thank you love, ni na san zaki so shi, ni na san babu wanda zai ki ABDUL dina Mama, ni na saj zaki so shi watarana"

Uwar ta yi murmushi tana janyota ta gabanta kamar wata yarinya karama ta ce" Ba tsanar Abdul dinki na yi ba baby, wasu halayarsa na iko na tsana!"

Risalah ta ce" Mama, ki masa uzuri da maganar ikonsa, yana da damar yi mama, ki masa uzuri, ni kam ikonsa na daya daga cikin abinda ke karra sakani sonsa a zuciyata Mama "

Baki ta tabe ta dauki takardar ta sake duba kudin,
Kafadunta ta dan daga, ba maganar godiya ko nunawa yar ya yi bajintar da ta isa a gode masa, dama bata koya mata haka ba, ko duniya zai bata bata koyaa mata gannin wani abin a zo a gani ne, yau ta fara kama kudi ne? Yanzunma hakan take a dan takaice da isa da basarwa da nuna kudin har wani abu ne ta ce" Za'a karra injinnan gyaran jiki a saloon dinki da kudin nan"

Tsare uwar ta yi da kallo ta ce" Saloon kuma? Inace kin ce an daina?"

Da mamaki ta kalleta ta ce" An daina? Why za'a daina?"

RISALAH ta ce" Mama yanzu fa kika cewa ABDUL an daina ?"

Yatsina fuska ta yi ta ce" A daina? Kina bani mamaki Risalah!"

Da wani mamakin ta budi baki zata sake yin magana uwar ta daga mata hannu ta ce" Look, ki ci gaba da nuna masa abinda nace muna kai a kawo a daura auren, kafin a daura auren ki tare kanwarku zatana zuwa saloon din ta kula da shi, idan kika zauna a gidanki kika mayar da ABDUL mutun ya zamto ba zai iya rayuwa ba sai da ke sai ki koma bakin aikinki ki nemi kudi Hajiata, idan baki da shi ko a cikin yan uwanki kece koma baya bale a duniya!, Ki rage kulafirci da shirme a kan da namiji!"

Tana gama fada ta mike ta haye da takardar kudin, ita kuma ta rakata da kallo
Sosai hudubar ta shigeta, da kyau kuma ta rike a ranta cewa dan ta yiwa Abdul karya dan ta samu cinma burinta ba laifi bane!, Haka kuma kudin nan da ya ajiye bata bishi da kalmar godiya ko Addu'a ba, daga naa wayar ta dauka kawai ta shiga tura masa kalaman soyayar da ta san da wahala ya mata replay ko ya bata amsa a takaice kamar haka" Thanx "
Ama bata damu ba, ta san yana sonta, shi kawai ka barshi da nauyin bakinsa ( uhum hajiata ana yiwa wace bata isa bane nauyin baki walahi!)

Yana zuwa gidan kakanin nasa sai da ya kusan minti goma sha biyar da ma'aikatan gidan sunna dan zantawa, bale mazan, matan da Hajia babar ma'aikaciyar gidan kawai suka zanta

Sai da ya gamsu da komai sannan ya shige ciki

Tunda ya shigo ya ga wayam ya samu kansa da sakin murmushi da tunanin kennan ba'a shirya ba tunda ba'a zaune a falo kallon dare kamar yadda aka saba

Juyawa ya yi ya nufi hanyar hawa ba tare da ya kallo bangaren dakinta ba , kai ko a kansa hakan bai shigo ba sam

Muryar Farid dake rusa kuka ya saka shi dan saurarawa da fara hawa ya yi tsai da tunanin kukan yaro kuma?

Har zai sake hawa ya jiyo magana kamar haka "Wayo Allahna na shiga uku, Mama idan kika zane shi hala nima zaki zane ni? Mama dan Allah kar ki zane mu , ni jikina ruwa yake yi ya yi ta ciwo shi yasa bana son duka!"

Muryarta ya tsinkayo tana fadin" Malan yi min tsittt da bakinka ko na farfasa maka jiki, kai Hasan zo nan na ce, yau zan ga uwar taurin kai da rashin ji a gidan nan, ba dai kulun a kan haka zamuna yin fada da kai ba? To yau jikinka ne zai fada maka!"

A hankali ya saurara ko zai ji muryar wanda ya tabbata wannan yaron ne mai zuciyar nan, watau wanda ya birge shi a ranar da suka watsa masu ruwan kwata,
Sai dai jin shiru ya saka shi dan juyowa a hankali ya sauko kafarsa daya ya kara saurarawa

Jin karan saukar bulala da fasa ihun Husaini ya saka shi karra sauka da dan sauri ya karasa bakin kofar ya dan saurara yana son jin da gaske dukan yaron ne take yi ko me?

A lokacin ne ya ji muryarta a hankali tana fadin" Ba zaka fahimtar da ni ubanda kake aikatawa a ajin ba ko Hasan? Watau ba zaka yi magana ba sai dai na kasheka ko?, To yau ni da kai a ga wanda ya fasa, kai kuwa Husaini idan bakinka bai min shiru ba sai na fafasa maka shi a wajen nan"

"Wayo Allahna na kyale, Mama na kyale, Mama ki barshi haka kin ga baya wasa baya yin komai a ajin, nima ban san me yasa yake zuwa na buta ba mamanmu"

Sake jin saukar bulala da karanta a kam wanda yake tunanin ake duka ya saka shi dora hannunsa a saman abin budewar a hankali ya bude kofar sannan ya dan guara tsayuwarsa ya leka dubansa dan so yake ya fahimci abinda yake faruwa, haka kawai yake son daina jin saukar bulalar kamar wani wanda abin ya shafe shi
Chapter 27 · 0% Book details