Sashe 48
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
RISALA ta tsare shi da ido bayan ta kamo hannunsa ta ce" Kishina ne ya saka ka hanna ni tafia?"
Sai da ya zubawa fuskarta ido mai dauke da kwaliya da su gashin ido, kwaliya kai mai kyau din nan , a hankali ya gyada kansa yana tunanin kwaliyar nan ai ta yi yawa fisabililahi
Murmushi ta yi tana komawa kusa da shi ta ce" Dama na sani, sai da na fadawa Mama ta daina fushi na tabata da dalilinka mai karfi, gashi kuwa da dalilin"
Murmushi ya yi shima, domin ko ba komai ya ji dadin da ta dauki maganar da mahinmanci
A nutse ya ce" Zuwa na yi na ganki, na yi maki oyoyo sannan na maki sai da safe"
'Sai da safe?' ta ayanna a kasan zuciyarta, tana kallonsa ta ga ya mike yana dube dubensa ya sake juyowa ya ce" Hop komai lfy baki da bukatar wani abu?"
Da mamaki ta ce" Sai da safe?"
Juyowa ya yi ya fuskanceta ya ce" Eh "
Da mamaki ta sake dubansa ta ce" U said sai da safe, safe? Hakan na nufin zaka je part dinka ka yi sleep ? Ko kana nufin na taso mu tafi sai da safe na dawo nan?"
Ita da kanta da ta yi furucin sai da ta ji wani iri, ama kuma abinda take hange ya fi mata wannan jin nauyin a zuciyarta
ABDUL ya dan lumshe idannuwansa yana jin wani iri a furucinta, duda ya san gaskiya ta fada kuma ƙarin haske take so a furucinta, ama sai ya ga zuwan kai tsaye ai na namiji ne, a duniyar hausa
Dan sake matsota ya yi kadan ya zauna yana fuskantarta ya ce" Oh sorry, kin san a hukunce dole sai na yiwa UWAR GIDANKI sati kafin na yi maki ko?"
"Uwar gidana?" Risala ta fada idannuwanta na kankancewa
Abudl ya sake fuskantarta ya gyada kansa ya ce" Eh, yar uwarki, yayarki, ko kin manta ne?"
Gaban Risala na dukan tara tara, ranta na neman jagulewa ta sake dubansa ta ce" ABDUL, wannan wace irin magana ce? Kana magana kamar wanda ya tare da matar cen?, I said uwar gidana, yar uwata....kamar wata wace take da isa da takama a wajenka wace kuka yi auren soyaya da ita irina?"
ABDUL ya dafe habarsa dan magangannun sai ya ga kamar ba wani ilimi a cikinsu gaskiya
A hankalinsa ya ce" Risala, tanada daraja mana, ba magana ce ta na yi auren soyaya da ita ko akasin hakan, tunda har igiyar aurena ya rataya a wuyanta ai tanada daraja, nd maganar tarewa kuwa ai inaga sirri ce ko?"
Risala yanzun kirjinta ya fara dokawa da karfin da har gaban goshinta ke dokawa, a yamutse ta ce" Please, please ka yi shiru..... Please ka rufa min asiri ka yi shiru da maganar nana haka ......kar ka saka na tsorata da furucinka mana?......................, Na san an aura maka ita ama darajarta bata kai tawa ba, domin ni kake so ita kuma hadaku aka yi....., Nd maganar tarewa wannan ai inaga ba wani maganar da zan iya fahimta a cikinta tunda an jima da daura maku aure, kuma bayan wannan idanma maganar wace ta fara zuwa ne ka tambaya mun rigayesu zuwa gidan nan, wai bama wannan ba kamar wata budurwar yarinya zaka ce idan ka yi mata sati? Wani irin sati matar gotai gotai da yaranta da komai?"
"Risala, are u okey?" ABDUL ya fada a hankali yana kallon Risala da mamakinta
Risala ta kamo hannayensa tana mai tabatar masa lalle a cikin hayacinta take
Hakan ya saka shi fuskantarta ya ce" Am, RISALA, kina ji? Ina so ki kiyaye dukkan abinda zai shafi irin magangannun nan idan har bai shafe ki ba, sam bana tunanin zan lamunci haka ta fara fitowa daga kowace daga cikinku, maganar daura aure hakane ama bata tare ba sai a jiya"
Risalas da jikinta ke neman daukan zafi da wani irin yamutsa da ske yi mata a cen cikin kanta kamar zata haukace ta ce" No, no, ba jiya bane yau ne , kuma yau dinma na rigayeta"
ABDUL ya sauke numfashe ya ce" Jiya ta tare, ban san me kuke kira da tarewa ba, wanda na sani nake maki bayani a kai, kuma ta dauki karfin fara yin kwanakinta ne dan ba a rana daya aka daura aurenku ba, kin ga idan har hukunci zamu bi bisa adalci kwanakinta ne muka fara.....so ki yi hakuri koma menene abinda yan kwanaki ne zasu shige na dawo?"
Walahi, ita ba mashayiyar abin maye bace, ama a yanzu sai ta ringa jin ana yi mata mugun kida a cen cikin kanta kamar wace ta saba busawa bata busa ba
Kasa maganar da ta yi ya saka shi mikewa bayan ya mana mata pk a goshi ya fice yana janyo mata kofar, domin kansa shima har ya kwashi ciwon , dama ya wuni da abinsa ya nufi bangarensa dan yin wanka yana tunanin ba zai juri yawon dakunnansu ba, idan komai ya lafa na maganar bakunta zai dora dokar du wace keda shi ita zata zo turaka ( wo wo wo malan, wai kai yaya haka? Mufa sakinmu muke jira me kake jira da mu ne)
ABDUL na fita RISALA ta silale kasa daga saman bed din tanaa kunce daurin kanta ta warware shi sosai tana cusa hannayenta a cikin kitson tana yamutsawa da kardi ta kama jela guda ta ringa ja har sai da kan ya kama sara mata da wani irin karfi sai kuma ta dakata tana kallon waje daya ta ce" ABDUL, ABDUL, kana nufin dakin wancen matar zaka je ka kwana? ABDUL kana nufin dakin wancen matar zaka tafi? Me ma'anar ta tare? Me husarka ke nufi? .....Abdul!" Ta fada da karaji tana sake damkar gaban rigarta da kanta da hannunta ta sake fadin" ABDUL, don't tell me abinda ta fada cewa ta yiwu cikinka ne a jikinta dazu da irin tafiyar da take yi da komai cewa ka sadu da wannan matar?"
Da karfi ta daki abin gadon da hannunta ta ce" ABDUL!, ABDUL!, Kar ka ce min burina da rike kaina da na yi dan darenmu ya zamto unik,na kasance ta farkonka kai har ka ba wata wannan darajar ba ni ba?"
Da wani ihun kuka ta sake fadin
*NZL PAGE3️⃣3️⃣*
Da kyar ta iya tashi ta shiga wanka jikinta a mace, babu karfi ko daya, damuwar dake ciciyar kirjinta ta kore komai, dama da kyar ta iya rintsa idannuwanta zuciyarta cike da mamakin ALKALI, yanzu alkali yana sane ance masa ta fita bata da kafiya zata je asibiti, ama shine babu abinda ya dame shi? Alkali har ta kwana a wani wajen bai nemeta ba? Tana gannin kiraye kirayen ABDUL ta ki dagawa , dan ta fara lura wannan abin harda yardarsa yake faruwa, ta fara yarda cewa ABDUL ne ke bada dama ana wulakantata
Suturar da ta fito da ita ta cenza , watau doguwar bak'ar abaya mai shegen kyau ta dauki mayafinta ta yafa sannan ta bude jakarta ta hannu ta shiga fesa turare tana tunanin abinda ya dace ta aikata
Batama san ta inda ya dace ace ta fara ba, ama ko menene zata fuskanceshi, ta yi kuka a jiya ta huce, a yanzu lokaci ne da ya dace ta fuskanci damuwarta
Karfe tara na yi da yan mintunna ta fito sakamakon kiranta da Hajia Uma ta zo ta yi cewar ta yi baki
Zama ta yi kamar yadda ta saba a kimtse, zama mai birgewa, kafafuwanta a hade, abayarta ta dan bazu kadan ta bi jikinta masha Allah, kanshin jikinta kuwa ya hade ko'ina domin tana fitowa kanshin turaran Channel gangariyarsa ya baje ko'ina ya hade ko'ina ya doke kowane da aka yi anfani da shi a wajen
Da kyar Hajia ta iya jurewa bayan Maman Risalar ta gaisheta ta amsa mata sannan ta sake hade bakinta da fuskarta tana kallon TV
Hajia Uma ta yi murmushi, domin ta kula kawar tata fa ta karra kankaro wulakanci, dan haka itace ta fara yin magana tana duban Maman Risala ta ce" Hajia ki yi mata bayani mana?"
Maman Risalar ta tabe bakinta kadan tana kallon yayarta da ta mintsineta, domin dama itace tace sai sun zo sun dauki wace ta isa da shi su je gidan ta ce" Hajia, dama jiya ne Risala ta yi kirana tana kuka take fada mun yadda suka yi da ABDUL, cewa wai sai ya yiwa yarinyar nan sati daya kamar wata budurwa wai ai itace uwar gida tunda an rigayi daura aurenta kafin ya yiwa Risala nata kwanakin, bayan a jiyan da kika ce a kai Risala ko wankan kirki bata yi ba aka kaita, shine kuma haka zai biyo baya?"
Hajia ta sasauta gilashin idannuwanta na karin karfin ganni tana kallon Maman Risala
Ita abin mamaki ya fara bata, sai kuma ta samu kanta da jin haushin lamarin
Da basarwa ta ce" Kina nufin, auren da aka daura yau kwana uku cif, ta tare jiya a jiyan ta fara kawo karar mijinta?"
maman Risala da yayarta suka kalli junna, sai yayar tata ta yi gagawar fadin" Aa hajia ba haka take nufi ba"
Hajia ta fuskanceta dan ta kuka itace uwar maganar ta ce" Yaya take nufi kennan?"
Mama Risala ta dubeta ta ce" Hajia, ya dace a yanzu idan akoy wani abu da ya shiga tsakani mu mayar da shi gefe mu fuskanci abinda ya dace ace mun fuskanta"
Hajia ta yi murmushi tana sauke kafarta dake saman dayar ta fuskanceta sosai, a hankalinta ta ce" Ke da kina tunanin akoy wani abu da zan rike a tsakanina fa ke Hajia?, No, bama ke ba, ko wanda ya girme maki ba zan iya hakan da shi ba.....dama cewa na yi than.........abinda kika ce kin shirya ni na jima a kai......"
Ta saje duban jus din da mai aikin Hajia Uma ta ajiye a gabanta da cofin kwalba mai kyau ta dauke kanta ta sake dubanta ta ce" Idan dabi'arta ce, ya dace ki kwabeta ,domin mijinta ne ai , kuma yanzu suka fara rayuwar, a duka lamarin itace a baya , ya dace ta daina kawo maki kararsa, bayan wannanma ai na wani abu zaki yi masa ba ko?"