← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 83

Sashe 72

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta karaso mai ba fulawowin da aka shushuka ruwa ya gaisheta sannan ya tambayeta shin ya amso ky ne?

Samun kanta ta yi da zubawa wajen ido,da tambayar kanta shin a amso mata ky din ne?

Zuciyarta na zumudin a amso, wata na gargadinta

A hankali ta girgiza kai ta juya tana sake maimaita sunnan wajen a cikin zuciyarta ta koma cen bangarensu

Tun daga nesa ta hango Risala ta yiwa wata cencadediyar budurwa rakiya, hakan ya sa ta dan rage tafiyarta gar suka gama matar ta shige motarta ta tafi, ita kuma ta juya ta nufi nata bangaren

A hankali ta dauke dubanta a kanta, dan da farko ido ta dan zuba mata sannan ta shige bangarenta

Sai bayan magariba Baba ta tafi, watau sai da ta yi jira ABDUL ya dawo ta samu ganninsa da kanta ta sanar masa komai, domin ita kam ba za'a yi haka da ita ba walahi, yadda yaron nan ke mutuntasu ba zata kasance cikin shiritar Amina ba

Ai kuwa, halayansa na girma ne ya gabatar
A yadda ya dauki abin da irin yadda ya yi maganar sai da ta ji kamar ta fasa kukan dadi

Bayan sun gama maganar duka kaf abinda za'a yi wanda sai da kyar ya yarfa aka dan rage ya fuskanci Baba a nutse ya ce" Baba, dama a kan maganar Firdausin nake son mu zauna da ke, sai gashi yau kin zo"

Baba ta gyara zamanta a saman kujerar falonsa da ya yi ya yi da kyar ta zauna , domin da farko a kasa ta so zama gannin yana sama, ama firr ya nuna shima ai kasan zai sauka idan har ta sauka

A hankali ya ce " Kasancewar ba takaba bace take yi, tana da damar fita, shine nake son sannin a fannin makarantar boko da ta islamiya a daidai ina ta tsaya? Domin ina so ta je ta ci gaba da karatu dan ta karra warwarewa ta manta komai"

Sai da idannuwan Baba suka cika da kwallah, harda tarin jin kunyarsa tana sake sada kanta kamar shine baban , itace karamar ta ce" Oh, Elhaji da wanna
Tsuru ta masa kukan na daukewa cik, itace Abdul ke wulakantawa haka? Jama'a ga mari ga tsinka jaka? A guje ta juya tana sake fashewa da wani kukan Bilhaki, wanda ya saka shi dan mikewa kadan yana kallonta har ta bacewa ganninsa ta shige bangarenta

Labulen ya saki ya dawo a ransa yana Adu'a kamar haka ' Ya Allah, ka kare min ita da abinda ke cikinta, sam bata bi a hankali , gudu fa take yi da cikina a jikinta"

Amina naa shiga falonta ta karasa wajen Fido ta fada jikinta tana kukanta hadi da neman yin burgima

A rikic Firdausi ke tareta dan kar ta jima kanta ciwo tana fadin" Aunty, subahanalah aunty lafiya?"

Amina na kuka ta ce" wai ni ce zai ringa kora?, Nice zai ce na je awo ko ya ringa aunani a gida?, Nice zai ringa wukakantawa dan ya rungumin wanncen abar kamar karauki tana tafe frikyau firkyau kamar diban raba? Duwawu a shafe kamar bayan plat sai wasu shangalalun hannaye kamar kanlemun fara cici kashi?"

Firdausi ta kwalalo idannuwanta cike da alj'ajhabin wannan ba'a layayiya ta ce" Awo na me aunty? Aunty, wayo Allahna aunty ko dai ciki ne da ke?"

Cak ta tsayar da kukan tana zarro idannuwanta tana kallon Fido ta ce" Ciki kuma?"

Firdausi ta kureta da kallon itama ta ce" Eh mana aunty, na ji kina cewa an ce ku je awo, kowani abu ne za'a auna? A sanina ciki ne ake zuwa awonsa asibiti ko?"

Amina ta sake hade fuska ta ce" ciki kike min fata ne ke?"

Firdausi ta sake zubawa karfin Hali irin Na Amina ido,kafin ta ce" Aa, Aunty ana zancenma? Ai baban farin cikina da na twins a duniyar nan ki bamu baby, baki ji yadda muke fatan gannin haka ba"

Amina ta shiga tureta daga jikinta tana silalewa kasa ta ce" Ta yiwuma bakinku ne ya kamani, ta yiwuma kunne kuka min fatan nan abin nan ya sameni, shikenan na shiga uku kin sani Fido, ciki ne na kanina a jikina Fido"

Firdausi ta shiga tafa hannu ta kwashi kururuwar da ta saka Amina yin wuki wuki tana kallonta

Salati take tana salamewa da sanarwa ubangijinta, a rikicen da gangan ta ce" Wannan da ace su Uma da rai har sai sun sakaki a ukun da gaske, mijin naki kike wani cewa kannenki? Yo ko kin bashi shekarun haihuwarsa tunda ya zama mijin ki ai komai ya kare, Kunya? Abin kunya? Halal din? Allah ya rabamu da abin kunya, kuma walahi kinga awo ko? Tsaf zamu je awo gobe, ni nan zan rakaki abinda yace shi za'a yi gaskiya, kuma a dai ringa tunawa da mutuwa, idan ta zo a hali irin haka ai an shiga uku , me za'a amsa a gaban Allah? Mace marar yiwa miji biyaya ake sak, kuma dai ai an yi islamiya an san makoma, ko shi yasa kwana biyu ba ruwanki da kowa kike ta masifa? Mu kam abin dadi ya same mu sai sallah da sanarwa ubangiji walahi aunty , haba dai ai godiyar Allah ya dace ba wai a nuna rashin gldiya ba"

Har baki Amina ta kama da mahaukacin Mamakin Fido ta ce " Ke, kin ci kaniyarki,na ce kin cikaniyarki kin ji? To sai ki kaini asibitin na gani!"

Ta mike ta wuce ciki tana fafa tamkar zata ari baki

Firdausi kuwa ta yi tsit sai da ta shige ta mako kofar sannan ta mike tana dariya hadi da zagayawa tana sake godewa Allah

Karshema dakinta ta wuce ta shiga duba abinda zata saka na fitar da zata fara yi a gobe, har Allah Allah take yi goben ta yi, a jiyama har yar dariya Yaya ABDUL ya bata da ya yi maganar ida, wace idar kuma ita da ta yi jinnin haihuwa? Ai an wuce wajen kawai kowa ya yi ta kansa, ita dai yanzun zata maida hankali ne ta gina kanta da taimakon ahalinta, namiji kuwa sun yi hannun riga da shi, ai an gwada tunda ba riba an hakura

Wainar Baba ce ta raba dan Amina fushi take yi, Baba kuwa ta tsaya a kanta da jan ido ta ja rantsuwar gobe da sasafe maza a shirya a je maganar miji , idan ba haka ba ai ta san ana mutuwa kuma ba'a yafewa kowa ba!

Kukanta ta sha, kuka da biyu, dayan abinda ke mata ciwo wai ita ABDUL ya kora, dayan kuwa na zuwa awo ne

Da kyar ta yi barci, haka kuma safiya na yi Firdausi ta tasheta, lahadi ne ama da yake clinik ce, kuma ya san da zuwansu haka ta shirya rai bace suka tafi asibitin ta su Mansur

A asibitin sunna karasawa Muhammat ya fita ya shiga ciki

Jim kadan ya fito tare da Mansur din da waya a kunnensa yana magana yana tsaye gefe guda

Muhammat ya daka hannunsa ya bude gefen da Fido ke zaune yana fadin" Bismillah kanwata ku fito "

Firdausi dake karra tausar Amina tana yi mata maganar ta daina to hade ran ta fito da dan gudu sakamakon daga hannun da Amina ta yi tana cik alwashin sauke mata biyar a kumatunta

Birki ta ja tana kallon barin da MANSUR ke tsaye ta ce" Ina kwana?, Zata fito yanzu in sha Allah"

A hankali Mansur ya dauke dubansa daga kanta yana maidawa kasa, dan haka kawai ya ji haka ya dace ya yi , sai kuma ya dago da murmushi yana jin furucin ABDUL dake Fadin" Mansur, ka ga idan docter ba zata dawo yanzu ta duba min mata ba kawai ka sakata a office dinka kai ka fita ka tafi wani office din ni na zo na aunata, kar ka bari wani kato ya mata tambayoyin da bai bata ajiya ba, ka ga rantama a bace yake, inaga ba zasu wanye lafiya ba fa?, Docter ita ta san yadda ta vi da ita wancen karronma , kawai ka nemota zai fi"

Docter Mansur na murmushi ya ce" Ka ga wasa fa nake maka tun jiya na sanar mata, yau bama ta aiki ama tuni ta zo tana office dina , su ladai take jira ta tarda mujinta da ƴaƴanta park"

Ajiyar zuciya ya sauke mai dan dumi ya datse kiran yana dan sosa kansa a hankali da jin haushin nemansa da fitinar da Mansur ke yi, shi kuwa sai ya wani manta komai ya biye masa su yi ta yi kamar wasu yara ƙanana
Koda yake gaskiya ba zai iya lamuncewa a yiwa iyalinsa dala dala ba! To ai bama kyau hakan a adinance

Sun ga likitar, sosai suka zanta cikin hikima da iya aiki,
Abinda docter ta fuskanta ya sakata fara dauko strategi na sakawa Amina cikin nan a ranta, ko tace na bayana mata tsantsar kaunar da take yiwa cikin ama takw dannewa dan wani dalili nata, domin uwa ba zata taba kin cikin dake jikinta ba ko a wani irin hali, sai dai wasu lokutan wani tashin hankalin kan dane soyayar , idan ya yi mugun karfi harma yakan rinjayi soyyayar, sai wani gyara na Allah

Hotunnan da ta ringa hasko mata na yayan larabawa da turawa cikin kyan kama da kyan shiga, da yayan hausawa cikin kyan shiga da yannayi na farin ciki, da tarin kaunar dake idannuwan iyayen ta ringa kallo har suka gama bayan ta tabatar batada wata matsala na laulayi da ya wuce cin abinci da barci, ta karra mata nasiha sosai a kan yadda zata kula da kanta sannan ta fada mata ainahin lokacin da zata fara awo mai sunna awo, ama kafin nan ko me ta ji marar dadi to fa ta dawo ko ta yi kiranta ta sanar mata bama sai Sir ya sani ba, sunna iya yin magana a tsakaninsu

Sosai ta sakata ta saki jikinta da ita suka cenza number sannan suka fito ta rakata Ofice din Docter Mansur domin Fido na cen zaune tana jiranta
Chapter 72 · 0% Book details