← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 83

Sashe 15

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Datijantaka da ilimi da salatin annabi da ya yiwa harshensa kawaya ya saka shi tausasa lafuzansa sosai hadi da iya kiyaye harshensa ya ce" Dama mun zo ne dan mun san a yanzu a duniya babu wanda ya kaika kusanci da ita, kuma babu wanda ya isa ya yanke hukunci ba tare da ya tuntubeka ba, Alhamdulilah tunda har ba zaka iya rikewa ba ni zan riketa, har Allah ya fitar mata da mijin ta yi aure, ko bayan raina na san iyalina zata rike min!"

Malan Liman ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa, ai ko ni nan zan rike Baiwar Allah mai baban sunna, ka duba ka ga yau a masalaci irin taimakon da suka tara dan ance an tafi asibiti da ita, yanzu haka ana amsar kudin mai dari mai dubu kowa na bado talafi da kuma alkawarin za'a hadu a saka ido sosai dan a kama azalumin dake son karya mana haki a ido, ai in sha Allah yarinyar ba zata tabe ba, sai ta zauna a gidanka Elhaj idan Allah ya fitar mata da miji sai a daura mata aurenta ta yi tafiyarta gidanta"

Da aka ce ko yaya ka yi da jaki sai ya ci kasa haka ne, kamar wanda wannan bawan Allahn yake gudun abin alkhairi da rahamar ubangijinsa, shin bai san falalar shafa kan maraya kadai bane a rayuwarsa bale kyautata masa da cireshi a kunci uwa uba ciyar da shi? Shi dai koda ya sani to fa shedan ya yi galaba a kansa a wannan lokacin da lada ke binsa yana zundumawa a guje tamkar mai gudun fanfalaki, a takarkare ya warware wani nadin na arzikin yana nuna hali ma rashin arziki ya ce" Ban taushi numfashinku ba, ba zaku gane abinda ni na gane dangane da yarinyar nan ba, kamar yadda ta fita daga gidan nan dan ta raina rikona da ikona ta gwamace zama a gidan ubanta haka zata koma yanzuma ta ci gana da zaman a cen! Walahi ba zan barta ta je gidan kowa ta zauna ba! Ba da yawuna ba, idan kuwa wata iyakar tawa zata nuna min bismillah sai na ga idan ta samu mijin wanda zai daura mata shi! Ai ta gani da kanwarta ta min rashin da'a yadda muka kwashe da ita!, Itama bata fi karfin hakan ba, babu abinda ya shafeni da barikinta ko kudinta, idan ta bijire min in na kama tsine mata sai ta bi duniya wa bilahilazi!, Alkawarina ne wanann!, Gwarama ta gyara halayarta ta koma ta kama mutuncinta ta zauna ko ta samu mashinshini, idan har ta bar gidan nan da nufin zama wani wajen sai dai idan da auren wani a kanta ne!"

Daga Liman har Baba Mai shanu ido waje suke kallonsa
Baba bai san lokacin da ya ce da Malan dan iya" Aman Malan me yarinyar nan ta yi maka da kiyaya hala? Ko dai kiyayar ta mahaifinta ce ke shirin shafarta?"

Malan Dan iya har huci yake yi ya cire kansa gefe, irin wannan karron iko a hannunsa yake din nan , zai gwadawa Amina bata isa ba, ita din ba kowa bace , idan tana tunanin ta kai wani mataki ne dan tana da gida banzar bazara ce ita! Ya ce" Ba maganar gaba ranka shi dade, ai na yi rantsuwa ne sai dai idan da auren wani zata je gidansa ta zauna!"

" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yanzu fisabililahi Malan wannan din ina anfaninsa? Idan fa bata fa maneman a yanzu? Shin baka gane cewa ana so a yaga mutuncin yarinyar nan bane ko me? Wani irin uba ne kai? Anya zaka so a yiwa ƴaƴan cikinka?" Liman ya fada da jimami yana kallon Dan iya

Dan iya ya tabe baki ya ce" Liman ba zaka gane ba, mu mutanen karkara munada namu ka'idojin da ba'a takewa, a shekarun fa ta tara kadai laifi ne a kauye, tana yawo waje waje , bata zauna ba, baka san yaron mai garin garinmu sai da ya fito aurenta ba? Mahaifinsa ne da kanda yace aa wannan din ai ta tsufa sai dai ya nemi wata, wannan abu ya min ciwo a rayuwata, kwata kwata bata da sa'ar rayuwa ne!, Da yanzu ta malaki shanu uku ko hudu nata na kanta!, Sai karyar bokon tsiya, wannan din itace maganata, yarinyar nan ba zata je ko'ina ba ta koma ta zauna, wani mutuncin kuma? Kai ni fa dai na rantse bata da shi , kai baka ga rawar kanta ya yi yawa ba?"

Baba mai Shanu tunda ya rufe baki da hannunsa yana kallon larkararen rashin ilimi da shirme ya kasa furta koda A ne, yana kallon yadda Malan ke iya kokarinsa dan ya dawo da Dan iya hanya, ama abin ya gagara, du inda ya bila sai ya bile, irin girman zumunci yake nuna masa da irin alkawarin Allah a kan wanda ya yanke zumunci, ama sai ya zile ya nuna masa ai yarinya ta lalace ba za'a iya talafa mata ba, Liman har zufa yake yi, gardama da mai lafiya ce da ita, domin ba za'a kirayeshi da jahili ba yana da nasa sannin daidai gwargwado!,

A sanyaye Baba Mai shanu ya ce" Ka yi shiru abinka Liman, ba fa zai saurareka ba"

Sai kuma ya fuskanci Dan iya ya ce" Shin yaushe ka yanke aurar da ita? Ina nufin zaka iya bata koda kwana uku ne ta dan saku daga wannan tashin hankalin a gidana? Idan ya so ni zan dawo maka nan da kaina da maganar aurenta, domin nima alkawari na daukarwa kaina ta gama zama a gidan nan ita kadai!"

Dan iya kallon Baba mai Shanu yake yi, so yake ya kara kafewa ya kara zilewa, sai dai gaba daya mutumen yanzu da ya zo masa a tausashe sai ya kasa yi masa musu

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai ka isa da ni Elhaji, ba damuwa tana iya daukar har sati daya ta huta din, duda na san karya ne bata da wata damuwa, ama bayan nan idan bata samu mijin ba ta tatara ta koma rayuwar ta da, ba zata hanna kowa zaman lafiya da gidansa ba"

Malan Liman gyada kai yake yi yana karra kallon mutumen, Baba Mai Shanu kuwa harda godiya da nunin ya gode da akai masa wannan alfarmar

Ai kam kamar ya sani, alkhairin aka yi masa mai tsoka, yan dubu dubu sababi dal kafin su tafi, sunna daukan hanya shima ya dauki tasa hanyar ya nufi kasuwa dan ya yi sare sare, ba zai yarda ba matarsa ta ga kudin nan ta rabashi da su da jarabar lalurar yara!

Mai Shanu ya jima a wajen su Malan Liman sunna tatauna maganar nan, karshe suka rabu bisa shawara daya tak, wace ta yiwa Malan liman dadi har cikin zuciyarsa, ya kuma dauki alkawarin daukan kwana uku yana fadawa Allaj da sake neman zabin Allah a kan lamarin

Koda ya koma gida wajen hutunsa ya je ya dauki alkur'aninsa ya shiga tilawa, dan sosai zuciyarsa ta tabu da wannan lamari, hankalinsa ya tashi sosai da wannan abu, tausayin kansa ke lulube shi, da tunanin abinda dan Adam ya zama
Baima koma saman hajia baba ba, bai sani ba dan rikewar kafar nan harda su docter ya zo ya dubata tana ta zubawa jikan shagwaba a waya ya mata alkawarin zuwa ya dubata shima, danma tafia ce ta fado masa wace dole shi da kansa zai je, a kan maganar taki ce da yake son buda kampaninsa na kansa dan ya fara fitar da takinsa yana siyarwa sannan yana anfana shima waa kansa

Sarai Baba ya lura maganar da ya mata kan ta ja yarinyar a jiki bata yi, hasalima tunda ta yi wunin dayaa bata fita ba a na biyin shi da kansa da ya sauko bai sameta a gidan ba,
Bai nuna damuwarsa ba ya kama hannun biyu suka wuce da kansa ya masu rakiya makaranta sannan ya bada damar idan baba Lauratu ta zo a barta ta shigo wajen Amina dan ta fada cewar a jiyama ta zo bata samu shiga ba, da wannan Amina ta wuni tare da baba dake karra tausarta da nuna mata hakan ya fi mata alkhairi, kuma da ta ji baba ya mata shiru a kan tafiyarta gidan yayan mahaifinta itama ta yi shirun kawai, ta tabata zai waiwayeta ko me ya yanke, sosai ta yi mata nasiha cewa ta yiwa matar gidan biyaya, ko menene ta tabata idan har bata taka dokarta ba ba zata wulakantata ba, kuma fa ba laifi tana da dan mutunci fa, kawai sun kalubalanceta ne

Ita dai dadin da ta ji na gannin Babar ne, sosai suka wuni sunna shan hirarsu har yama ta yi baba ta mata salama zata tafi, a nan ne ta roki alfarmar ta biya ta sanarwa Firdausi, tace mata ba sai tace zata zo ba dan ta san ba barinta mijinta zai yi ba, ta fada mata babu abinda ya sameta, zata zo da kanta daga ta samu sararin hakan

A wannan ranarma idonta idon Hajia bai hadu ba, Hajiar fa tamkar babu mutun a gidan haka ta mayar da ita, bata damu da lekata ba, bata damu da ita ta lekota ta gaisheta ba, takan fita dan ta gaishetan ama bata taba cin sa'ar haduwa da ita ba, yaranta kuwa sun zama sai hange, to sai hange mana sukan tare da Baba sai dai ta ringa jiyo dariyarsu da guje gujensu, karshema wani gem ya sa aka kafa masu tafkeke ya sa ana koya masu idan suka fito daga karatun islamiya yana zauna yana shan dariyar saurin fushin Hasan da kuma saurin kulan Hisaini, kamaninsu daya ama halayarsu sun sha bamban sosai, irin nutsuwar da yake kara ji da shawarar da ya yanke a zuciyarsa ya sa yale karra shirin hakan a ransa
Chapter 15 · 0% Book details