← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 83

Sashe 51

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryarta a sanyaye ta ce" Ka fada mata ina gidan Uma, ka barta ta zo Elhaji ba damuwa"

Tana gama wayar ta katse ta zurawa waje daya ido still jikinta na yi mata wani irin yam yam yam kamar ana bin jikin nata daya bayan daya ana zukar jinnin jikinta
*NZL PAGE3️⃣1️⃣*

Da wani ihun kukan ta sake fadin" ABDUL, ka kirayeta uwar gidana, yar uwata, yayata.....kana son nuna min cewa ne kana sonta itama bayan an fada min grandfather dinka ne ya aura maka ita, an kuma fada min ita din ko wacece?, An fada min har ta haihu? Zaka kai mata kwanakina ne dan cin zali har sati daya dan ta asirceka ko me? Tunda dai kowa ya san ga yarenta nan a kan me zaka wulakanta ni? Waye bai sheda cewa na rigayeta zuwa gidan nan ama sai a bata kwanakin da suke nawa?!, Abdul uwar gidan banza uwar gidan wofi bayan nice amarya koda auren so ka yi da ita ka fi dokina ?, Abdullllllllllllllllllllllllllllllllll kisa kake so na yi? Wayo Allahna, wayo Allah................." Ta karashe da kukanta, sai kuma ta zabura ta rarumo wayarta ta shiga dokawa nahaifiyarta waya

A irin wannan lokacin maman nata kanta tana dakin mahaifinta sunna hirar dare kira ya shigo wayarta na Risala

Tana dagawa Risala ta shiga labarta mata duka yadda suka yi tana sheka kuka

Mahaifiyarta ta shaka iya shaka, rai bace ta ce" Tun ba'a je ko'ina ba kin ga ilar zurfafawa da namiji soyaya ko? Ba laifi yana iya yin abinda ya ga dama tinda an asisrceshi an nashi ya ci a waina, ama ba zan taba lamuntar wannan wulakancin ba, in sha Allah zamu zo a zauna gobe da safe a kan maganar nan, ina hadin bazawara da budurwa? Kuma mu ina ruwanmu da maganar wai itace uwar gida bayan kin rigayeta shiga gidan?, Ai walahi ba zan lamunta ba tsaf ya dawo dakinki idan ya maki sati ke mai darajar a tare da ke sai ya koma mata ya yi mata kwana uku irin na zawarawa irinta, in bandama cin zali ina hadinki da naa wata bagidajiya.....? No ba zan dauki haka ba, ki kwontar da hankalinki in sha Allah goben zamu zo gidan , saima na faraa biyawa na dauko kakarsa mu wuce dan ba zai yiwu ba walahi, a kan haka sai na amshi takardar sakinki!"

Sosi ta hau take zage zage har ta kwontarwa da y'ar hankalinta sannan ta juya ta fuskanci Mahaifin Risalar da yake fadin" Meye kuma daga zuwa yau yau har ta fara kawo kararsa, kin ga ki yiwa yarnan tsawa fa, na kula so take yi ta saka ni a cikin jin kunya , yaushema har zata fara an yi mata an yi mata, aa ni fa bana son irin haka nan gaskiya, ki kwabi yarki ko zata zauna a gidan miji kar ta kaso auren ko sari bai yi ba!"

Mahaifiyar Risala ta mike tana fadin" ai kuwa elhaji sai fai ka shiryawa jin kunya, domin ba zan taba yarda a cutar min ya ba a banza a wofi, shi yasa bana yarda da siyayar dangi dan idab danka ya yiwa yarana na tsaya tsayin daka na hukuntaka daidai da laifinka, danginama ban dagawa kafa ba a kan y'ayana bale jikan yar talakawa? Ai Walahi ba zai yiwu ba".....

Yana kallonta ta shige ciki sai mita take yi da rantse rantsen ba zata sabu ba bindig a ruwa, ta yaya za'a ba ƙatuwar mace kwanan y'arta, ko amarci basu fara da miji ba
Kai ya kada ya yi kwonciyarsa bai bita ba, abu daya ne ya sani idan takamarta ita karyar kudi hajia Hauwau ta dameta ta shanye, kuma a kan jikanta sai ka ga rashin wayonta, bata hada jikanta da kowa fa a rayuwa , ita nan har so ne take nunawa ya? Ta bi a hankali dan yana guje mata garajenta ya hadasa mata husumar da ta fi karfinta, domin lalle ita din yar mai kudi ce, ama ta kasa ganewa gaba da gabanta, su kam
sun yi biyaya

___________________________________

Dakin yaren ya fara zarcewa bayan ya rufe falon da ky yana mamakin Uman biyu da shiririta ta kwonta ne bata rurufe ko'ina ba?

A hankali ya bude dakin ya shiga da salama kasa kasa dan ya tabata warhaka ai sun yi barci

Turus ya yi yana zuba masu ido su uku a saman gadon Uman biyu ta bararaje abinta a daman gadon yaran nan du ta takurasu ta matse masu waje har kamar zata tunkudo Husaini kasa tunda tsakiyarsu ta shige abinta

Habarsa ya kama da hannu biyu, irin idan abu ya bashi mamaki ko haushi da yakan yi dan nuna girman mamakinsa ko jin haushinsa a abun yana kallonta a hankali ya ce" Bata jin magana fa yarinyar nan ko kadan"

Kai ya girgiza ya shige bayi ya duba an kashe dukan abinda zai iya zamowa damuwa wa barcinsu, ya dawo falon, a nan ya ga kaskon turaren wuta da hayaki kadan kadan na dan tashi irin ya cinye din nan saura dan kadan ne a ciki

Ido ya zubawa kaskon yana tunanin anya wannan aikin aikin daya daga cikin ma'aikatan familly dinsu ne? A formation da ake basu na kula da gida idan suka saka turaren wuta sukan tsaya ne har ya gama waje sannan su dauke su tafi da shi
Sake juyowa ya yi ya dake kallon wajen AMINA
Dan kankance idannuwansa ya yi a kanta , sai kuma ya karra tabe bakinsa ya dauke ya fitar ya kashe ya yarda mata kasko a cen ya dawowarsa

Adu'a ya shiga yiwa yaren a hankali yana dafa kansu daya bayan daya har ya gama sannan ya sake kallonta da mamakin nauyi barci ne haka ko dai summa ta yi?

Hannayensa ya saka bayan ya tatare hannun jalabiyar tasa a hankali ya saka a hamatar Amina ya yi mata dagowa irin ta yara sannan ya talabi bayanta ya cicibota gaba dayanta ya mike tsaye da ita a hannunsa

Ido ya sake zarrowa gannin bata farka ba,
Kai ya gyada ya juya a hankali ya fito da niyar mayar da ita dakinta sannan ya dawo ya rufewa yaren dakinsu

A hankali yake tafe da ita yana sake wara dubansa a kan fuskarta domin har wani dan lilo lilo take tana murmushi ga dukkan alamu mafarki take yi ko kuwa idannuwanta biyu neman fitina take yi da shi

A daidai zai shige da ita dakinta ya gwara mata kai da garun wajen, hakan ya saka Amina bude idannuwabta da sauri jin an kwala mata dutsi tana barcin

Ido hudun da suka shi da shi ya sakata sakin ihu ta kubto ta dirmiyo kasa , sai kuma ta saka wani ihun tana kokarin mikewa da dan wara kafa domin ai dinkine a kasanta jama'a

Tsayuwa Abdul ya yi yana binta da kallo tana dan kai kawo tana yarfe hannu yana tanbayar kansa hala dinkin da yawa ne akai mata? Ko kuma an bar mata abin zare na sukarta a wajen?

"Yanzu ni zaka dauka? Ni Amina? Wai kamar wata kanwarka? Mema ya dawo da kai dan girman Allah? Me yasa kake shiga harkata ne ni? Me na yi maka kuma yanzzzzzzzzzzzz"
Gannin yana matsowa kusanta maganarta ta dauke tana zaro ido tana kallonsa

Hannunta ya kama ya nufi bakin gadon da ita ya zaunar da ita yana kallonta cen ciki ya ce" Ina zuwa"

Juyawa ya yi ya fice, hakan ya sa Amina kokarin tashi dan ta rufe dakinta da ky ta zo ta yi tunanin yadda ya dace ta yi da wannan yaron, domin bafa zata yarda ya ringa raina mata wayau ba da girmanta!

Dawowarsa da rufewar kofarta da ky da ya yi ya sakata komawa ta zauna a saman gadon tana zarro ido tana kallonsa

Fitilar dakin ya kashe sannan ya kunna ta kusanta mai hasken ja mai ragagen haske

Yana yi yana fadin" Ki kiyaye barin abin turaren wuta kuma ki yi barci kin ji? Ita wuta batada kadan, kuma aikinta mai girma Ne Amina"

Amina dake binsa da kanta kamar zai karye dan son gannin me yake nufi da ya kama sunnanta gatsau sai da ta ji wani iri, ace kanninka na kama sunnanka fisabililali?
Da gunguni ta shiga fadin" Ko wa'inda suka girmeka Aunty suke ce min, dan ka dauki karfe ka wani ja dare kamar daren mutuwa shikenan sai ka nemi raina wanda ya girmeka?"

A lokacin ABDUL ya gama dube dubensa ya karaso inda take zaunen ya duka kasa hannayensa a saman katifar, hakan ya sa ta ja baya tana son hantsilawa hadi da fadin" Kai wai meye haka?"

Da sauri ya rike kafafuwan nata daria na son kwace masa, shi walahi har yanzu ya kasa yarda bata wuce wata sha bakwai haka ba, wannan shiririta haka?

A hankali ya ce" Me kika ce?"

Amina dake hadiyar yawu da sauri da sauri ta ce" Me zaka min dan Allah?"

ABDUL ya yi dan murmushi ya ce" Ba komai fa, cewa na yi me kika ce?"

Amina ta ringa dauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Cewa na yi wai da, ka ga tunda na girme maka da yawa na ce min aunty , wa'inda na girma haka ka fahimta?"

Kai ya gyada , a hankali ya ce" Nima na ringa ce maki Aunty ne?"

Amina aka wani mane baki aka gyada kai, ita ga Aunty

Murmushi ya yi ya ce" To Auntyna"

Amina ta dan tsatsareshi da ido dan sai ta ji kamar da gatse ya kireta auntyn

A hankali ya shiga dage doguwar rigar barcin nata, a gigice ta daka hannunta tana rike nasa taba kallonsa bakinta har yana hadewa ta ce " ABDUL , menene haka kake shirin yi? Me zaka min? ABDUL ka tashi daga kusana kuma ka daina tabani , ka ga lokaci nake jira ka bani takardata ko? Dan Allah ka barni haka ya isa"

Kansa ya dago a cikin ragagen hasken yana kallon yadda du ta rikice, tsoro na dawainiya da ita karara

A hankali ya ce" Ba komai ba fa zan yi maki"
Chapter 51 · 0% Book details