Sashe 10
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido Amina ta tsura mata, zuciyarta cike da damuwar wannan lamari, yanzun kayan miyarma ya salwantar mata da siyarwa? Ashe dole ta lalace har haka, dama da yar sana'ar ake samu ana kaiwa mai dan dadi baka, ta rasa ta inda zata bullowa al'amarin kanwar tata, ta ce ta je ta yi dinki ta koyi sana'ar dogaro da kai ya kafa kai da kasa ya kiya, ta nuna mata ta gwada siyar da awara ya kiya, ta ringa sana'ar kitso da gyara jiki domin itama ta iya nanma ya kiya, komai bawan Allahn nan idan an kawo na karuwar Firdausin sai ya kiya....wai sai ace kishi ne ke damunsa, wannan wani irin kishi ne bakin kishi? Yanzun dai ba'a kai ƴaƴan cikinta da ta haifa ba, ya yi masu katangar karfe wai hasan da husaini shekara shida shida a duniya yace sun zama samari su daina shigo masa gida, yanzu haka wannan rashin nutsuwar ta tabata tsoro take yi kar ya dawo ya tarda su a soron gidan da ta dakatar da su cewa tana zuwa, yaran kansu a yanzu idan ba ita ta kawo masu maganar Firdausin ba sun daina yi mata maganarta, shin yaya zai yi da haki da girman soyaya irin ta uwa da ƴaƴanta? Sam basa shiri a duniya , zata iya shiga gidansa ta fita yana nan basu gaisa ba, domin har akoy ranar da ya zageta ido da ido yace tana yawon banza ta ki fitar da miji baya son mu'amalarsu da matarsa, ita kuma tace sai ya dauki wuka ya yanka hannun matar ya tsiyaye jinninta dake gudu a jikinta ya cenza da wani, a ranar har ashariya ta kusa yanka masa dan bacin rai sai da Firdausin ta yi ta kuka da bataa hakuri ta hakura ta yi tafiyarta
Amina ta sauke gauron numfashi ta ce"ki zauna waje daya mu yi magana, tsoro kike ji kar ya dawo ya tardo biyu a soro?"
Firdausi ta zauna din tana jan numfashi ta ce" Aunty ai idan ya tardo sun ban san yaya zamu kwashe bane, kin sanshi da kulafirci da daukaka gaba da rigima"
" Y'ayanki? Fido bakya missing dinsu? Bakya jin kamar zaki haukace dan rashinsu a gefenki? Bakya jin rashin dacewar hukuncinsa ? Ba zaki iya dakatar da shi ki nuna masa martabarsu da darajarsu ba? Shin bakya gudun shiga hakinsu?" Amina ta fada a sanyaye har idannuwanta na neman cika da kwala
A hankali Firdausi ta dora kanta a kafadar Aminar kuka na kwace mata
A kasa kasa sosai take kukan tana mai sake dora kanta a gefen kafadarta ta ce" Nakan wuni, na kwana da tunaninku, da matsananciyar kewarku baki daya, Aunty ina son su sosai fa, walahi ina son su, rikicin cenjin Rayuwar da na samu ne ke makani a kasa, Aunty bana iya tsalake maganarsa ko yi masa jayaya, ina ji ina gani ya haramtawa y'ayana shigowa gidansa bayan musulunci ya yi nuni ne idan D'a namiji ya balaga kana iya ware masa wajensa da sauran yayanka mata sannan ka saka ido sosai a kansu baki daya, shi din ko dan ba shi ya haifi nawa bane yake ki? Marayu ne.....yau da bani da ke yaya zan yi a rayuwa?"
Sosai fushin dake zuciyar Amina yake narkewa yana komawa tarin tausayi da jinkai na yar uwarta
A hankali ta ci gaba da dan bubuga bayanta a sanyaye ta ce" *KI YI MASA LADABI*, na tabata babu abinda yake dawamame a duniya dadi ko wahala, watarana zai cenza halayarsa ko Allah ya canza maki da wanda ya fi shi zama alkhairi"
A hankali take amsata, Amina ta saka mata dubu biyun a hannunta ta ce" Ki adana wannan, du ranar da baki samu abinci ba ki yi kokari ki siya ki ci, in sha Allah zan dawo "
A hankali Firdausi ta amsa ta mike ta boye tun tana zaunen sannan Amina ta tashi ta fito daga dan tsakuraren dakin Firdausin tana yi mata salama
A hankali Firdausi ta ce" Aunty, dan Allah ki ce da su ina gaishe su, Allah ya yi masu albarka, ki ce masu kulun kulun ina yi masu addu'a sosai"
Murmushi sosai Amina ta yi mata a sanyaye ta furta" Allah ya saka da alkhairi, zan sanar masu in sha Allah"
Da wannan suka yi mata salama, basu hadu da mijinta ba sai a lokacin da suke tsayar da mai adaidaita sahu, ido cikin ido suka kalli junna da ita, ama sai ya cire kai tamkar ya ga wata abokiyar gabarsa
Itama Aminar bata gaisheshi ko ta nuna ta sanshi ba, domin ta sani ne idan ta yi masa gaisuwarma da kyar ya amsa, koda ya amsa a kayade take zai ce da ita "Lafiya" yana cire kai, gaba yake yi da ita , yana jifanta cewa ta ki yin aure ta zauna zaman banza har tana neman tsofewa ta fake da nufin bata samu miji ba, to wa zai fito ya dauki ya'yan wani ya rike sannan ya kwashi sauran karti? Wannan kalamai nasa suka saka ta daina gannin mutuncinsa, dama mutuncin nasa kadan ne take gani domin mutun mai irin halayar mijin Fido sam baya cikin tsarin wanda zata iya yin zaman minti uku da shi a waje daya ba a rayuwa
Firdausi dake gida zaune bayan tafiyar yar uwarta ta yi shiru ta zubawa waje daya ido zuciyarta cike da tunanin rayuwa da aune aune da sake sake ta yi firgigita tana mikewa tsaye da sauri sanadiyar jin rufe gidan mijinta ta hanyar saka sakata da komai sannan ya shigo gidan fuskarsa a hade sosai yana karewa ko'ina kallo da son gane abinda yake zargi
Gannin bai fahimci komai ba ya fuskanceta fuskar nan a hade tana masa sannu da zuwa hadi da miko masa ruwan da ta ja a rijiya ta tanadar masa tunda ta gama dafa dukan taliya yar murdi ta adana
Ruwan ya bi da tsinanen kallo ya sake dubanta fuskar nan a hade ya ce" Na tabatama ta zo gidan nan , domin na hadu da ita a bakin layi, abinda nake son sani shine ina fata bata shigo min gidana da kartin maza ba, kuma baki dauki ruwan gidana tsaftatace kika bata ba?"
Kai Firdausi ta sada, zuciyarta na dokawa sosai, ciwon magangannunsa na ratsa zuciyarta, ita din ba mutun mai fitina bace, du irin sanyin Amina ta dameta ta shanye, ama duda haka wani lokacin sai ta ji tamkar asararen zama take yi da mai gidanta, sam bai san darajarta ba, bata tunanin gabar da yake yi da danginta dangin nata ya tsana, ta fi tunanin matsalar a kanta ne, itace damuwarsa, itace abikiyar gabarsa, takan yi tunanin da ace tafiyarsu bata dauki salon tsarce tsarcen yawu da tashin zuciya ba, da ta nema masa sauki itama ta samawa kanta , wani lokacin tana yin biyayar ne dan tsoro da tsoron Allah ba dan tana ji a ranta ya cencenci ta masa biyayar ba!
A sanyaya ta ce" Sun zo, ama bata shigo da biyu ba, kuma ko ruwan gidanka ban bata ba"
Daga haka ta juya ta shige cikin daki ta dauki carbinta ta zauna gefen gadonta ta shiga hailala da salatin annabi, domin shine kadai abinda take lazumta ta ji sauki a zuciyarta dangane da zamanta da mai gidanta
Baki ya tabe ya daura alwallah yana ta mita da fadace fadacen shi da ya isa da gidansa da Amina ta daina shigo masa gida!
Ita dai daga wannan bata ce masa ufan ba, sai da dare ya tsala ya sake biyota saman jigatacen gadonta ya yi mata turmusar da baya tsalake rana, kulun fa wannan sai ya biya shi baya tsalaken rana, da yinwa ko ciki koshe, da yardarta ko babu yardarta , idan ya tashi zuwa zai zo ne babu dan aike zai turmusa da dukkan karfinsa ya mike ya barta da wahalarta!
Bayan kwana biyu
Kasancewar amaryar gidan aunty Rukaya yarinya ce mai dan haske sai take yi mata gyaran hadin kurkum da zuma, sai kuma hadin dilkar tubawa tsumamiya wace a kwana na biyun nan da ta fara yi mata aikin fatar yarinyar har wani kyali take yi tsabar gyaran na kamata (gaba daya hadin zai zo da zarar na rufe free page)
Yau gashin kanta ta raba gida hudu ta yi hadin gyaran gashi kamar haka : Nescafé, Kwai, madara, man shanu: ta kwaba shi sosai ta ringa bi daya bayan daya tana shafa mata har ya gama hade kan ta sakata saka leda sannan ta daura dan kwalinta a sama da zumar ba za'a wanke ba sai nan da kwana biyu domin yarinyar na fashin sallah ne, ta sake jadada mata kar ta damu da karnin kwan, idan bata kunce bama ba zata ji ba, domin turaran wutar da take yi mata kadai ya isa ya hanna karnin ya dameta
Kamar yadda ta saba tataka mata , hakan ce ta faru yauma har kan kwanar gidansu sannan ta ja ta tsaya tana hangenta har ta shige gidansu
Juyowa ta yi da zumar komawa gida, da sauri ta ja baya kadan tana kallon Muctar mai kanti dake tsaye daf da ita sosai
Hade fuskarta ta yi kadan domin ta tsorata sosai bata san da mutun kusa da ita har haka ba tana sake dan matsawa hadi da fadin" Aa, Malan muctar kaine tsaye kusana har haka?"
Muctar ya yi murmushi yana kallonta gannin tana sake jan kasan hijan dinta tana kokarin rufe fuskarta ya ce" Ba dole na ringa dakon hanyar fitowarko ba tunda na je zance sau uku kina kin fitowa? Amina shin kin dauka da wasa nake ne ko ba zaki iya auren talaka irina ba?"