← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 83

Sashe 36

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta ta sadda cikin shiga ta blue din Hijab mai tsayi har kasa sosai ta ce" Hajia zan tafi gidan Firdausi ne na dawo dn Allah in ba damuwa?"

Hajia dake murmushin abin nan da mamakin yadda aka yi ya saurareta bai fatataki kowa ba, dan ita fa a shirye take tunda safw jiran ihun sunnanta take yi da balbalin balakin fadan ba'a isa ba, sai ta ji shiru , kuma gashi har yanzu bai dawo ba daga fitarsu juma'a, ita da kanta tana sin fecewa ama har yanzu bata fara fitan ba tukunnan, so take yi sai komai ya idasa lafawa

Hajia ta ce" Kina ji, kina iya tafiya ai ba wani damuwa, ama ba zaki shiga taxi ba saboda Alkali gaskiya, ki je zan yi kiran direba daya ya kasance direbanki ne"

Amina ta yi dan jim, sai kuma ta rage tsayinta kadan ta yi godiya sannan ta juya ta fice

Hajia ta sake rakata da kallon da ta saba na harare harare da kuma haushi haushi a fili ta ce" Allah ya wadaran naka ya lalace, wai Alkali wannan ce zai sa ta juyani ni Hajia Hauwau? A dai daura auren zaka gani"

Tare da Baba Lauratu suka je gidan
Sun tarar da Firdausi tana sharar dan tsurut din balbalin gidan nata da wata tsintsiyar da bata fi a irga tsinken dake daure da yaloluwar leda fara ba

Tana jin muryar Amina ta mike a zabure tana wara idannuwanta hadi da amsa salamar

Da sauri ta daga kafarta dan ta zo da gudu ta rukunkumeta, sai dai amsawar da bayanta ya yi ga daskarariyar yinwar da take ji ya sakata dafe bayanta a hankali ta furta" Wash Allahna "

Da sauri Amina ta karasa tana rikota ta rungumeta a jikinta a hankali tana fadin" Fido? Sannu ki yi a hankali mana"

Firdausi ta yi yar dariya tana ji abin ya lafa mata a tsayen nan ta shiga dariya da murna da son dole sai ta yaye hijabin Aminar tana fadin" Uman biyi kece haka? Uman biyu kanshi kike yi wannan turaran fa? Uman biyu cirw hijabin nan na gani hannayenki bake ji wani santsi hakama jikinki ya dauka? Wayo Allahna farin ciki kasheni zai yi ni kam yau, Uman biyu kin ganki kuwa? Wayo Allahna da ke nake kwana ina tashi, damuwa ta cikan cikina, idannuwana kulun a kan kofar gidan nan, sakata yake sakawa ta baya du idan zai fita wai karma na saki na fita bai san tunda yace Allah ya isa idan na je ba na yi hakuri na biki da Adu'a, Uman biyu kuma da biyu kika tare? Shi mijin naki bai koro su ba! Uman biyu wai dan Allah........."

"Fido wai ba zaki yi shiru ki huta bane?" Amina ta katseta tana ririke hijabinta, dan walahi ita kunya take ji irin yadda jikin nan nata ya dawo, kamar ba jikinta ba, wani irin santsi da yake yi har mamaki take yi, ga wani haske da fatar tata ta dauka har tana neman zarce fuskarta haske, ita kam wannan gyara ya fara damunta , gashi Baba tace bata ga ranar dakatar da gyara ba wai sai ta tare, hahahaa ta tare a ina? In ba rikicin Baba ba?

Firdausi ta dan sasauta din, sai kuma ta sake rungumeta kadan saboda tirtsitsin cikin dake hannata motsin kirki ta fashe da kuka tana fadin" Uman biyu, aka daura aurenki wai babu ni? Innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah idan wani mumunan laifi na aikata ka jabaceni da wannan jarabawa mai tsauri bayan rasuwar mijina mai sona da ta iyayena , Allah ka sasauta min ka yafe min ka bani ikon cinye jarabawar nan, Allah kai ka haliceni kai ka dora min, Allah ka bani ikon cinyewa ya ubangijina"

Baba Lauratun ce ke amsawa, Amina kam janyewa ta yi a hankali ta dauko wata yamutsatsiyar tabarmar firdausin ta shinfida a nan tana kaiwa zaune da kafafuwanta dake cikin safa

Baba Lauratu ce ta ce" Dan bani jakar nan mana?"

Amina ta miko mata jakar da kudin nan yake ciki, Baba ta fice a gidan

A hankali suke hira hannayen junnansu a rike da junna

Amina ta yi iya yinta dan kar ta yi kuka, ta yiwa kanta alkawarin in sha Allah ba zata kuma yiwa dan iskan nan kuka ba, ba Firdausi bace? Tunda ta nuna idan ta fito zata karra zama karin ci da sha da sutura ne a kan Aminar sai ta zauna gata ga shi, haka Allah ya rubuto tata salon kadarar, tana fata ba dare ba rana Allaj ya katse mata wahalar nan da take fama da ita

Dawowar Baba lauratu da leda ta ja gidan ta rufe da sakata ta ajiye ledar ta bude tana ciro dunkula dunkulan kaji gasasu da jus dan kwali da manyan ruwan faro ya saka Firsausin da Amina zarro idannuwa

Baba ta mikawa kowace nata itama ta ja daya ta ce" Yau ai juma'a ce, bismilarmu"
Amina bata san lokacin da ta fashe da dariya ba domin yadda Babar ta yago kazar nan kamar sunna gaba da junna ne
Itama Firdausin dariyar take yi, nan da nan yawunta ya tsinke tana kallon lazar da tsoron tabata
To sai ta ji tsoro mana, ita rabonta da ta gantama ba ta manta ba, sai irin wani lokacin idan tsuntsaye suka dan sauka dan kama wani abin su ci su yi tafiyarsu dan kuwa ko na anguwa masu kiwo basa samun shigowa dan gidan a rufe yake kulun

Ci suke sunna santi da dariya, Baba zuciyarta ta yi mata fesss tana kallon yan marayun da dariyar da suka samu
A ranta take adu'ar Allah ya datar da su da farin cikin nan, ta san dadi ko wuya ba masu tabata bane har karshen rayuwa, wata rana dole a ji dadin, wata ranar kuwa a sha wuya, sai dai tana dakin ranar da zata ga farin ciki mai sunna farin ciki a fuskokin marayun nan

Amina da ta koshi da wuri tana kora jus din nan mai shegen sanyi da dadi ta ce" Kai, anya akoy abinda ya kai kaza da yaji dadagage dadi kuwa?"

Fisdausi dake hannu baka hannu kwarya baiwar Allah kamar zata tsinke yan yatsunta ta girgiza kai tana fadin" A duniya? Aa babu gaskiya"

Baba ta yi dariya tana fadin" Akoy mana, miyar taushe ta sha dadawar batsi yara ta fi komai dadi"

Aminarma ta yi dariya ta ce" Haka fa babanmu ke fadi Allah ya masa rahama, yace babu abinda zai dauke masa hankali da irin girke girken mai sunnana, watau mamansa"

Firdausi ta kora ruwan ta yi shiru tana jin wata zufa mai sanyi n tsatsago mata sai gyatsa mai nutsuwa ta bi baya a hankali ta ce" Wayo Allahna, dadi zai kasheni, Allah ka sa mutu k raba auren Auntyna"

A dan zabure Ameena ta kalleta zata yi magana Baba lauratu ta amsa da ameen, sai kuma ta ce" Bama kya tambayar biyu?"

Firdausi ta yi murmushi tana fadin" ƴaƴan mamansu ni mamakin da na yi yau babu su a rakiyar kamar wutsiya du inda ta bi sunna lake da ita"

Baba ta wani karkace tana share zufa hadi da yin murmushi ta ce" Sun tafi masalaci da babansu ne ai"

Da mamaki Amina ta kalli Baba, waye baban nasu? Kai ita gaskiya ba'a kyauta mata a duniyar nan kwata kwata!

Baba ce ta hsde sauran ta mika ma Firdausi ta ce" Kauda a kasan gado inda bera ba zai ja ba ki boye idan ya fita salar asuba ki janyo ki kauda sauran ki zuba a masai "

Yadda ta yin ya karra basu dariya, irin karma ya ji koda kanshinta ne

Murmushi ta yi a ranta tana ayana' Kaya, ai na rabaki da talaka mai zuciyar fir'auna, shi bama zai saki ransa ya cin ba in dai daga hannun Amina ya fito, a fili zan ajiye dan na tabata masu fada masa ta zo zasu fada masa, ni kuwa yau cikina a cike ai ko wace wace kawai!'

Sake gididige watannin cikin suka yi, kafin su mike su yi mata salama

Ji ta yi kamar zata dane su su tafi da ita, tana jikin kofar tana saurare har motar ta tafi ta koma cike da farin ciki ta idasa tatararta ta sake zubawa dubu goman nan ido ta yi wani murmushin hadi da godewa Allah da ya bata Amina a rayuwa
Ta tabbata da kudin nan zata jima tana cin abinci, idan ya fita sai ta yi kiran yar gidan maman husnah ta bata ta amso mata abin tabawa su ci tare ta yi daidaya ta huta abinta.....................

Talaka bawan Allah, shi baban burinsa ya ci ya cika cikinsa koda babu dadi, sannan ya samu kwonciyar hankali komai kankantarsa.....Allah ka karra rufa mana asiri duniya da kuyama, sannan ka kara ba ba mai bamu😍😍😍😍😍😍🤣
*NZL PAGE2️⃣3️⃣*

Kalaman da ta fara jifan aminar ta su ya saka Hasan dake samn gado yana daga kafafuwansa tashi zaune ya zuba mata ido

Rai bace ta nunawa Amina hannu ta ce" Abinda nake so da ke shine, idan ya kawo kayan nan kar ki saki ki bude, ki bari idan aka kai wadincen din zan saka a kawo maki su ki bata nata, wa'inda yace a baki ba naki bane nata ne, kar ki saki ki kaini bango yarinyar nan!"

A sanyaye Amina ke kallonta tana son fahimfar inda kalamanta suka nufa, domin ita dai bata san da maganar wai za'a karra mata lefe ba, wadinnanma da ko anfani bata fara da su ba dan gani take yi sun fi karfinta bale wasu?

A hankali Hajia ta dafe gaban goshinta tana mai fashewa da kuka ta ce" Wannan wace irin masifa ce?, Da na san zan riski ranar nan da na shirya mata, ama ki me kike tunanin kin tanada ki zubar dan walahi na shirya maki tsaf zan yake ki da dukkan karfina!, Amina ki..........".........

Maganarta ce ta katse a lokacin da ta kai dubanta kan hannun da ya rike mata hannu

Fuskar yaron har wani huci take fitarwa ya rike hannunta taf ya zubawa fuskarya ido

Hannunta ta janye da sauri tana sake kallonsa

Hasan haka kirjinsa ke sama yana kasa,
Chapter 36 · 0% Book details