← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 83

Sashe 23

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka barni na yi, ka barni na tuna mata ita din mutun ce kamar kowa, bakin ai ita ta gayato su dan a hadu a taro ni, na haukace ko? Ita ta harhado su dan a yi min magana zan tafka sabo ko? Ai bakin makusantanta ne da nawa, idan summa sun haukace sai na gani, idan tunani take yi saukin halin da na dauka na zubar da komai nake rayuwa da ita dan samun sukunin zuciya tsoro ne ko dan ta fi karfina ne ta farka, Son ka barni a gaban bakin nata na tuna mata bata isa ba ta hanna wani abu a kan wannan, na daura maka aure zaka zauna da matar ko ta ki ko ta so, kuma sai matarka ta aminta zaka dauko ta biyun da take fada, maganar siyasa kar Allah ya sa su hau in dai son zuciya suka saka a gaba!, Hauwau kema zan iya haramta maki zumunci da kawayen nan dake mance abin rufa dan su zo su yi zigi a kan aikim lada da gyaran rayuwar wani, ki saurareni da kyau Hauwau, nace zan iya haramta mu'amalarki fa Uma, idan har ta fini a wajenki kuma sai ki bita, ki bita Hauwau!"
Baba Mai shanu fada yake yi tun karfinsa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, gaba daya hakuri ake bashi ana fatan ya yi shiru ama ya gagara, zuciyar Aliyun Umar Farukun a kusa take yau, yau a kai kan gaba ya amaye abinda ya girgiza kowa, da yawaa yanzu suke kuka na tsorata da tashin hankali, ya jima rabonsa da rigima irin haka, ya dauki girmansa da hannu biyu ya zubar da komai tunda ya rasa dansa kwalin kwal da matarsa, ya daina saka hancinsa a wajen da ba'a saka shi ba, yana aiki ne dan ubangijinsa ba dan wani ba, yana kyautata mata ne da zuciya daya dan burinsa ya mace a hannunta ta yi masa takaba a gobe kiyama ta zamto uwar gidansa a aljannah idan Allah ya aminta, sai gashi lamarinta na kulafircin mulki na son haifar mata da ɗa ba ido, a fadansa da ya furta furtaciya fa? Wace koda da kome da kunya fa? Da sun dawo kowa ya yi dana sani, ABDUL RA'UF gannin abin zai zarce misali ya saka shi shiga kafadunsa ya rike shi da kyau ya shiga tafia da shi a hankali ya nufi sama da shi kasa kasa sosai yana fadin" Ka yi ta hailala, ka maye gurbin maganar da ambaton Allah, ka daina maganar haka, ka bar maganar haka"

Sosai kirjinsa ke dokawa, bai taba tunanin da girmansa zai ga irin haka ba sai yau, tun ana yara ba'a yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ta zo masa da sabon lamari a cikin rayuwarsa, wannan wace irin masifa ce? Tun jiya zuwa yau ta hannawa kanta kwonciyar hankali saboda abinda yake daidai da kuma alkhairi? Shi ba gori ya yi mata ba, ba kuma wulakanci ba, ya daki abin da karfi ne dan harta masu ririketan su gane bai zo da wasa ba a kan lamarin nan!

Zaunar da shi ya yi a bakin gadonsa, a hankali ya dora masa kafafuwansa a samn bed din ya cire masa sabon takalmin da ya dandasha na amarci, sannan ya cire masa safarsa harda hularsa ya kai komai ma'adaninsa ya dawo ya janyo kujera ya zauna ya zuba masa ido yana kallonsa

A hankali fushin ya fara sauka, har ya dawo yana ajiyar zuciya carbinsa a hannunsa yana ja

Kasa kasa ya ce" Na kira Mansur ne?"

Baba Mai Shanu ya bude idannuwansa ya sauke a kansa, shi yama zata ya fice ashe bai fita ba, tausayinsa ya ji ya kama shi a cen kasan zuciyarsa, ya sani sarai shima a cikin wani hali yake mai girman gaske, sai dai kamar yadda ya kasance mai saka bukatar wasu a gaba da taa, damuwar wani a gaba da tasa damuwar halaya kamara wani mai manyan shekaru ya sa ya dane nasa balin da ya sa zai masa ne a lokacin da ya fuskanci ya dace ya yi masan, a yanzu da ya ga yana fada ya cinye ya kawo shi dakinsa

Kai ya girgiza a hankali yana bin shadar dake jikinsa da kallo irin jan man da ta yi

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike ya rage karfin ACn sannan ya dannan yadda zai ringa yin sama da kasa kar ya kafe waje daya , ya dawo ya sake gyara masa kafafuwansa yana ta dan matsa kafafuwan dan so yake ya gane idan sunna da kumburi ko basu tasa ba

A hankali ya rufa masa bargonsa sannan ya mike da nufin barin dakin

Muryarsa ciki ciki, dan har ta shake ya ce" ABDUL RA'UF"

ABDUL RA'UF ya dakata, ya juyo ya dawo yana kallonsa da sauraronsa

A sanyaye ya ce" Kar ka aikata aikin dana sani, kar ka saketa ko me zaka tarda ka ji?"

Fuskar tsogon yake kallo da daraja tamkar ta mahaifinsa
*Saki, ko me zai tarda,* yake ta maidawa zuciyarsa
Wai dama auren da wannan yarinyar ne aka daura masa?
Ya sake tambayar zuciyarsa

A hankali ya sakarwa tsogon tatausan murmushi, dan ya kwontar masa da hankali sannan ya juya ya sake ficewa

Ja ya yi daga sama ya harde hannayensa yana hangen dan karamin meeting din da ake yi a falon

Maganar kakansa cikin fadansa ne ta fado masa a rai , inda yake cewa wace yake nema din bai is ya aura ba sai wace ya aura masa ta yarda
Murmushi ya samu kansa da saki a saman lebensa
Oh ahalinsa na shagalinsu
Watau su a duniya kowane idan ya tashi yakan yi abinda yake birgeshi ne da rayuwarsa, ba ruwansu da nasa ra'ayin ko nasa burin, babu ruwansu da bin nasa tsarin

Wani murmushin ya kuma yi yana gannin yadda abokin Baba ke masu fada hadi da nasiha, a haka jama'ar da hajia ta gayato ke dan raragewa domin da yawa dama da abin hawansu, wa'inda basu zo da abin hawan ba kuwa mota na jiransu

Ji kake yi tsitt Hajia babu rigima da koke koke, gaba daya kamar an yi ruwa an kafe ta yi shiru kamar bata wajen
Kawayen natama wasu tunda baba ya mike suka fece, sun san hali da zaki ya yi barci ne suke neman yin wasa da gashinsa
Dayar dai itace ta tsaya, watau Uma, itama gaba daya jikinta ya yi mugun sanyi kamar an zare mata laka

Umarnin da Baba Rabi'u ya bada kan ta raka Hajia dakinta ta dawo ta tafi gidanta ya saka suka mike Uma na rike da ita suka shiga haurawa

A hankali ya ce da Hajia, dan ya san wacece ita, shirunta ba yana nufin ta dauka daga abinda ta hau bane, yana nufin tana kaunar mijinta ta kuma dan waye shi, yana nufin komai abinta idan ta taboshi takan yi laushi, ya san wacece ita a kak kafiya a abinda ta yi niya, dan haka ya ce" Hauwau, dan Allah kar ki yi abinda zai daga hankalinki ta kowace fuska, ki rike hakan a matsayin kadara da abinda Allah ya hukunta, ki bar yaran nan su shirya kansu, idanma da maganar aurensa ku barni da shi Aliyun idan komai ya lafa zan tado masa fa maganar tunda ai ya san da ita, tsohuwar magana ce, da ba dan shi din Abdallah din da kansa ya nemi da a dakata ba ai da an jima da yi, dan haka ku kiyaye kun ji?"

Ita dai kai ta gyada masa, idannuwanta suka sake sauka a kan Amina da kanta ke hade da gwuiwarta , babu wanda ya ji muryarta ko ya gane abinda take ciki, tunda Baba ya fara fada da ta yiwa kanta haka bata kuma dagowa ba, a yanzu haka babu wanda ya san halin da take ciki,

Kai ta dauke suka idasa haurawa

Kasancewar hankalinsu a gaba basu lura da tsayuwarsa a barin dakin Baba Mai Shanu ba suka yi bangaren Hajiar

A hankali ya sake juyowa yana hangen Baba Rabi'u da kuma yarinyar nan

Kai ya sake girgizawa ya dago hannunsa dake maiko maiko da warin Man ja ya zubawa ido

Page 1 bayan free🥰🥰🥰🥰
*NZL PAGE1️⃣4️⃣*

'shin su basu damu da nawa ra'ayin bane? Basu gane an kawo lokacin da namiji ko mace take da damar rairaya da tankada dan su dauki abokin rayuwar da suka gamsu zasu iya rayuwa fa shi duk rintsi duk wuya ba?, Shin yaya Baba yake tunanin shi ABDUL RA'UF UMAR FARUK ALIYU UMAR FARUK zai iya gabatar da rayuwar da mace zata bashi dama kafin ya dauki wata macen idan har yana ra'ayin hakan? Yaya suke tunanin shi din nan zai iya wata rayuwa da fitsarariyar nan?, Ganninta na farko da ya yi ana dambe da ita a wajen aikinsa ga yarenta masu kuka, na biyu da harare ta bi shi bai san me ya yi ba, na uku sun tsaya a bakin titi da kato yama zata mijinta ne Lukman ya watsa mata ruwa sakamakon tare hanyar da suka yi ga gefen hagu dinsu babar mota ce da ta shigo titin sosai, shigarsu ruwan ya zama wajibi ne ama ta kama masifa bata ko jin ta gaji harda jefa dutsi da yin Allah ya isa, sai yanzu da ta kwala masa kai uwa birgin bulo, ta cakumar masha riga da kazanta a hannunta karshema wai shi ta daga hannu ko zata yi menene ? Allah masani,itace aka daura masa?, Tabdijan'
Dan kara saukowa yake yi yana sake kallon Baba Rabi'u da ya dage yake magana ba ko hutawa, har ya gama yana shirin tashi biyu suka shigo , Husaini yana aikin da ya saba, watau ciye ciye, hasan kuwa hannunsa daya a cikin aljihun shadarsa, dayan kuwa na reto kadan suka nufo wajen Mamansu dake zaune Husaini na fadin" Mama tsaya ki ji, tun kafin ya fada maki karya, na ranste da Allah bani ya yi, nace bana so, bana so ya dage ,karshema yace mai mayar da hannun kyauta baya dan wuta ne, sai kawai na amsa, kafin na kawo miki ne dai na dan bude na taba kadan, kai Hasan tsakaninka da Allah ba haka aka yi ba?"
Chapter 23 · 0% Book details