← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 83

Sashe 54

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan tarin karfi da yaji ya yi kadan yana cire nauyin da ya tsaye masa a gaban idannuwansa a sanyaye ya ce" Kin san cewa ba kyau tsananta kiyaya ko soyaya ko?, Kuma kin sani wannan hadi na Alkali ne.........a kan haka kin ga irin fushin da Alkali yake yi da ke ko?"

Hajia ta lumshe idannuwanta ta ce " ABDUL, sam ita din ba tsarinka bace, shin ka manta burina ka tsaya a takarar gwamna a sabon zabe ne?, Ka san me ake so a matsayin matar gwamna uwar gida, nifa ba wai wani damuwata Risala ko iyayenta ba, no, ni damuwata kai, ina wannan yarinyar ina amsa kiran sunnan matarka a gaban manyan mutane?"

Murmushi ya yi a hankali ya ce" Ki kwontar da hankalinki, in sha Allah lokaci zai nuna mana komai Hajia"

"Ni so nake ka salameta" hajia ta sake nanatawa, wanda hakan ya sake bashi mamakinta, bai taba sannin haka Hajiarsa take ba gaskiya

Murmushi ya yi bai ce komai ba, har Hajia ta gama saukowa, domin shi ya san hanyoyin sauko da ita koda tana cikin fushi ne, a nan ya yi mata abinda ta fi kauna watau ya tura mata ƴaƴan banki yana fadin" Ina so a koma gida yanzun daga nan.....Hajia, ina mamakin irin yadda har yanzu kike yarda wasu na shiga tsakaninki da Alkali, bayan kin fi kowa sannin wanene shi"

Shiru ne ya biyo baya mai dauke da tunani kala daban daban daga Hajiar har shi din

Cen ta mike tana yi masa salama ta sauka

A lokacin da ta sauko basa nan gaba dayansu dan haka itama bata tsaya nemansu ba ta fice da gagawa ta shige mota aka nufi gidanta da ita

ABDUL kuwa wayoyinsa ya kashe gaba daya ya kwonta dan hutawa

__________________________________

Kwanaki uku da suka biyo baya ABDUL bai kuma komawa dakin Amina da nufin tabata ko kwonciya yin barci tare da ita ba
Hakan da ya yi sai ya samar mata nutsuwa da ragewar faduwar gaba har ta zo ciwonta ya fara yadda zare dan haka ta shiga gasashi sosai har yanzu ya zamto ta saka Baba turo mata Asma'u dan su gama gyaranta sannan tace biyunma su fara zuwa ta yimasu nasu zata iya

A bangaren ABDUL kuwa wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsa da Biyu, a yanzu haka a cikin tractation din cenza masu makaranta yake , ama bai sanar mata ba, domin makarantar tasu gaba daya bata yi masa ba, ba dan tana makarantar gwamnati ba, aa, dan matsalolin da ake fuskanta na irin bambance bambance karara ba tsawatarwa ya saka shi neman takardunsu da komai ya rubuta su a wata babar makaranta ta ƴaƴan manya, yanzu haka lesson da aka ce sai an masu na wata daya kafin su ci gaba da cen din ne ya dan dakattar da su, idan aka dauke su akan mikasu wajen lesson din ne da kayansu na makarantarsu a dawo da su gida, ko a wuce da su gidan gona su sha kiwo da Baba, ko a tafi da su Kampani a sake su, su sha yawo da ciye ciyen kwalam da makulashe ana dubansu ta camera ana gannin mouvement dinsu da komai ciki harda ma'aikaciyar da ta kirayi husaini barawo, sai dai ta ringa binsu da kallo bata da bakin magana, domin a lokacin da ya zo da su sakon da ya bada a fadawa duk wani mai ruwa da tsaki a wajen a matsayin mahaukaci cewa ya kula tikiten karshen shan ruwansa a kampanin ke yawo a kusa da shi, dalilin wannan suka zama yan gata a wajen ma'aikatan, da masu yi dan kar a kore su, da masu yi domin Allah

ABDUL ya tatara du wani abu dake iya zamowa damuwa ya ajiye shi gefe, duda abin damuwar ya kula shigarsa ne yake yi da karfi da yaji koda baya so, ba wai shawararsa yake nema ba, a tsakakanin iyalinsa yakan ji bugun zuciya mai tsanani na yawo da shi
Ya bata fili, ya bata damar da zata yi mu'amalarta da dan kai kawonta yadda take so, idan ya shiga sun hadu da farko takan daure fuska tamau ta nemi rurufe jikinta, shi kuwa sai ya yi mata murmushi ya kireta da AUNTYNA sannan ya tambayeta idan ta tashi lafiya? Hakan ke sakata rakashi da kallo har sai ta tuna wa ta bi da kallo sai ta cire dubanta tana tura lebenta da tunanin yanzu haka da yace mata Aunty ba har zuciyarsa ba.........sosai take so su zauna ta amshi takardarta, ama du idan ya shigo sai ta ji bara dai gobe ta masa zancen har ta cike kwana biyar cif a matsayin mace cikakiyarta a karkashin ikonsa ya zamto yai zata fara gyare gyarenta bayan ta dan yawata a gidan da yamaci tare da Baba sun samu wajen da ya dace ace ta fara din Baba Ta fuskanceta ta ce" AMINA ya dace ki ga ABDUL RA'UF ki sanar masa da maganar nemanki, kafin ki fara, domin yanada yancin sani a yanzu da yake mijinki......"

Wannan magana ta tsaye mata a kahon zuci har yanzu da take kan murjewa Asma'u gyaran da ta yi mata tana tunawa

Sunma gamawa ta rako Asma'u har bakin get, daidai an wangale get din motoci har biyar suka shigo

Daga ita har Asmaun raka motocin suka yi da ido har suka kulewa ganninsu , Asma'u ta gyada kai tana yi mata salama ta tafi

A sanyaye Amina ke nufar Bangarenta ba tare da ta kalli kowa ba

A hankali tafiyar taya ta fara yin nauyi sakamakon jin kamar ana kallonta

Da dabara ta dago dubanta ta sauke a wajen da ta fi kyautata zaton a nan ne ake kallon nata

Tsaye yake kikam Hannayensa duka biyu zube cikin aljihun wandonsa yana kallonta da kallon da ya saka gaba daya ta tsargu da kanta

A hankali ta cire idannuwanta daga kansa ta sake daga kafarta ta yi taku biyu ta ji ta kasa yin na uku, a dole ta sake dakatawa ta juyo gaba dayanta ta tsaya tana kallonsan itama
Rabonsu da su yi irin kallon nan gaskiya har ta manta

A hankali ta nufo inda yake tsayen, hakan ya saka shi dan sake waigawa dan gannin idan umarnin da ya ba garadansa sun tafin ko sunna nan, sannan ya sake zubawa Uman biyu ido har ta karaso inda yake tsaye ta ja ta tsaya tana harde hannayenta biyu a saman doguwar rigarta wace ta dan lafe kadan a jikinta ta dan bi shap din jikinta kadan ta matukar kayatar da halitar jikinta
Kanta ta dan langwabe ciki ciki ta ce" Hi"

Fuskarta ya zubawa ido da yadda ta yin, kamar in Husaini na son abu yake yin haka, Hasan dama shi halayansa kamar na wani baba ne

A hankali ya dan matso kusa da ita, ta yadda sosai ya sake kerewa tsayinta yana kallonta cem ciki ya ce" Yanzu fa kin girma......ina hijab dinki?"

Idannuwa ta wara, sai kuma ta kausasasu tana kallonsa ta ce" Me yasa idan kana yiwa manya magana baka tausasawa?"

Murmushin gefen baki ya yi kadan ya zuba mata tsaurarun idannuwansa a kanta a hankali ya ce" Kin tabata kin warke?"

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi......, A hankali ta dan cire idannuwanta a cikin nasa kasa kasa ta ce" Hala murna kake ji dan ka ci zalina?"

Kansa ya girgiza yana kallon yadda ta turo bakin ita a doke amsa take so

Baki ta karra turowa tana kawar da kanta ta ce" Baba Lauratu ce tace nace maka wai, wai ina yin sana'ar gyaran amare, zasunna zuwa nan ina yi masu kafin mu tashi daga nan"

Baki ya tabe ya ce" Tashi zamu yi daga nan din Aunty?"

Har sai da ta kama habarta ta ce" Kai, harda kai kuma?"

Ya dage kafadunsa irin ya sani?, Sai kuma ya ce" Ba damuwa, ama idan muka zauna na ji million nawa ake baki dan wahakar dukawa da darzar fatar wata?????, In ya min.....idan bai min ba gaskiya aaaaaa......."

Idannuwanta ta kankance ta ce" ABDUL me kake nufi?"

Sai da ya kausasa nasa idannuwan ya ce" Abinda kika ji AMINA"

muhamadu rasululahi Sallallahu alaihi Wasallam, tana kallonsa har ya bacewa ganninta, gaba daya ya yi tafiyarsa, ita da za'a tambayeta waye fitsarare a cikin fitsararun zamani da ta fadi cewa ABDUL ne dan gidan Baba Mai Shanu walahi, idan ya kama sunnanta kirat har gabanta faduwa yake yi, inda dalili jama'a? Ana ce mata aunty da mutuncinta da komai ta zo zamanin da kannin bayanta zayana ce mata wai AMINA? AMINA fa? Ko su iyayenta ce mata suke mai sunnan Ina, dan mahaifinta har ya rasu ce mata yake yi Innata, shin shi ABDUL bai san sunnan Maman abansu ta ci bane hala?

(Ah to....tambayeshi dai)

Juyowa ta yi sai cika fuska take yi suka yi ido hudu da Risala dake tsaye wajen tagar bangarenta ta yaye tana kallon Aminar da wani mugun kallo tamkar zata kasheta da mari

Kanta ta dauke ta tataka ta nufi bangarenta, sai ga Biyu an dawo da su sunna ta maganar result din da Hasan ya samu yau da malaminsu dake masu lesson ya masu exercise

Da gudu Husaini ya kawowa uwar a lokacin da take bude bangarenta ya mika mata, sam basu lura da fitowar Risala da doso wajensu da ta yi yana fadin" MAMA, Mama albishirinki, dubi result din Hasan, dama Dady yace idan ya maida hankali zai siya mana tap da kuma babur irin na yara muna tukawa a gida , yau Dady sai ya yi dariya idan ya ga result din nan"

"Wanene dadynku?" Risala ta fada da mamaki tana kallon Husaini yadda yake dira ya karra kiba fatarsa ta karra murjewa bul bul da shi sak irin ya'yan gayu
Chapter 54 · 0% Book details