← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 83

Sashe 74

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsa ya yi suka gaisa sosai, ya sake jadadawa , ya bada kwatance tak tak , harda na gidan ubansa , ya sake fadin irin rashin mutuncin mutanen a takaice da kuma tayarwa da ahalinsa hankali da suke son yi

DPO ya yi murmushi ya ce" Wannan aiki ai nawa ne da kaina, zamu zauna da su, idan nan ya isa to, idan bincike ya saka su a uku kuma sai mu maka su kotu, domin sai mun bincike su kaf dinsu, daga ɗan har uban Honorable"

Da wannan suka yi salama

Amina ta saka hannayenta ta talabe habarta, wani tsadaden murmushi ya kubce mata tana kallon yadda Fido ke murmushin itama tana sauke ajiyar zuciya ta mike bayan ta yi godiyar da aka yi mata fadanta ta nufi ciki, cike da gayunta

Hajia ta rakata da ido tana jin wani irin tausayinta a cen kasan zuciyarta

Abinda bata taba yi ba ne ta yi, watau shiga hurumin Amina bayan cikin dake hada su

Tana kallon Amina ta ce"
Sai da ta dan dago yana kallon idannuwansa ta mana masa kisss wanda tsaf a idannuwan Amina sannan ta mike taa nufi ciki firki firki tamkar zata karye biyu
Ita amina Al'ajabinema ke neman kasheta, oh yaren zamani jarabace cike da cikinsu, yanzi wannan yar ita kuma halin da ta saka kanta kennan a rayuwa? Jarabar maza? To Allah ya sanyaya

Zamansa ya gyara yana nuna mata wajen zama dan nesa da shi, a tsare ya ce" Bismillah"

Kujerar ta kalla, tana nesa da shi ainun, sannan ta kalli ta dan kusa da shi
Haka kawai sai ta ga harda rashin adalci a lamarinsa
Ama sai ta kyale shi ta barshi da halinsa ta je ta zauna a kujerar, itama ai gani take ta fi mata alkhairi fiye da kowace

A nutse ta ce" Dama, dama dangane da maganar makaranta ne, jiya twins ke ce min ashe ka cire su a wancen makarantar tasu, ni ban sani ba, kuma har ka saka su wata ta kudi duka ni ban sani ba, shine nace dama zan zo na ganka a kan hakan"

Sai da ta dire aya yana kallonta, shima a hankali ya ce" Eh an yi haka, ashe ban nemi izininki ba Amina, na cire su ne baki yarda ba?"

Idannuwanta ta dago cike da jin wani irin abu marar dadi, tana kallonsa a hankali ta ce" Aa ba haka nake nufi ba fa"

Gannin ya yi shiru ya sakata ci gaba da fadin" Dama na zo mu yi maganar ne, saboda na ji wace makarantar ce suka koma, saboda halin rayuwa idan bata yi mugun tsada ba, kuma na yi godiya"

Yanzunma jin shirun ya yi yawa a dole ta dago idannuwanta dake sade ta zuba masa ido

Sai ta ga ita yake kallo, ama ba da kallon nan na kamar zai cinyeta danya ba, kallo ne normal kawai wanda zaka yiwa irin wani wanda baka sani ba haka

Basarwa ya yi yana kauda kansa ya ce" Allah zai badaa yadda za'a yi in sha Allah"

Amsar tasa a dunkule, kuma yua ja ya tsaya, kamar ya gama maganar yake nufi
Ta dan jima tana cicira maganar, har dai ta rasa abin bilowa a kan maganar sai ta ce" Kuma, Kuma fido yau take ce min an ce ta shirya gobe ta fara zuwa, ta fara tafiya makaranta da kuma koyon girki da.........."

"Amina, abinda ya Kawo ki kennan?" Ya fada yana katseta

Tsuru ta masa da ido

ABDUL ya ce" Idan shine kina iya tafia it's ok"

Sake zuba masa ido ta yi zuciyarta na kunna da tafarfasa, watau ta tafi ta basu waje su dora daga inda suka tsaya ko?

Rai bace ta mike ta juya zata yi tafiyarta tana dana sannin zuwa yi masa godiyar nan, farin cikin da ta tsinta a fuskar kanwarta ya sakata nufo dakinsa, sai gashi yana wulakantata

"Zaki fara awo gobe, dan ya kai wata daya da sati biyu , zaki je wajen Mansur ya hadaki da doctern da zara ringa maki awo in sha Allah" ya fada yana kallonta

Rai bace ta juyo ta ce" Awon me zan je?

A dake ya ce" Awon ajiyar dake tare da ke "

"Ni babu awon da zan je, kuma da kake fadin adadin lokacinsa wani ya fada maka ne?" Ta fada cike da neman a yita ta kare

ABDUL ya tabe bakinsa yana gyara zamansa ya ce" Anya wani ya isa ya fada min bayan ni kadai na diga abina?, Sai dai na fadi ranar da lokacin da tsayin lokacin da ya dauka, Allah dai ya fido shi lafiya"

Kukan da yake ta so ya ganin ne aka fashe da shi, ta nuna kanta, sannan ta nuna shi ta ce" ABDUL, ni kake wulakantawa ko? Ba damuwa Ai damarka ce, ka wulakantani son ranka, ni ga banza ko? Ai na laifi samu ka yi ABDUL, kuma babu inda zani!"

ABDUL yana kallon fuskarta da kukan da ba hawaye ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" Ai ba damuwa idan baki je ba ni sai na aunaki a gida,sai an jima Amina"

Tsuru ta masa kukanta na daukewa, jama'a ga mari ha tsinka jaka? Itace ke gannin haka a wajen ABDUL dan ya gama da ita?
A guje ta juya ta fice a dakinta tana sakin kukanta bilhaki
Turus Amina ta yi, ta juyo a kufule tana kallon Baba ta ce" Ke kuma yaushe kika fara kaunar turare haka? Inace du turaren da nake hadawa sai kice aa bakya son turare kinada cutar turare, idan kika shaka yana hadasa maki ciwon hanci da wuya?"

Baba ta karkace zamanta tana kantsar goronta ta ce" An yi haka, sai dai ai turarenma sunna ya kama, wannan nata ai inaga ba na kasar nan bane"

Yanzuma da haushi haushin da ita sam bata san ya kai cen ba ta ce" Du turare dai turare ne, Allah na tuba ai ba'a kai turarukan Madina ba, ni kuma da su nake aiki , da su nake hada turarukana, ko menene dai na Madina ya fi kyau da karko da komai, kuma sai maganar kwaliya kyau kyau kyau ai Allah na tuba du kyanta idan ta ga wata sai dai ta ja gefe ta yi shiru!, Kuma ai farin ne ta fi mutane ba dai kyau ba walahi!, Fari kuwa a me? Ai fari banza ne ni nan Amina na fada!" Harda buga kirji da sake kallon Baba irin tana jira ta ji ta bakintan nan

Firdausi tamkar zata saki fitsari a zaune yanda take mutsu mutsu da kafarta dariya na tukarta, a dole ta shiga tarin dole dan kar ta fashe da dariyar ta shiga uku

Baba kuwa ta sake gyara zama ta ce" haƙa ne kuma, ama fari ai karshen kennan, wani fa cewa yake yana son fara ko maya ce, kuma ni banma ga me yasa abin ke bata maki rai ba, bayan ba layin abinda ya shafeki bane uman biyu, sai na ga kamar fada ne muke yi a kan maganar ABDUL "

Turus ta sake yi tana kallon Baba

Sai kawai ta cire kai ta kama kofar dakin yarenta ta shige a fusace

Tana mako kofar Firdausi ta kama ciki tana kakaba dariya har fadowa take yi daga saman kujera

Babama dariya take yi bilhaki ta ce" Walahi idan ta tarar da su sunna rashin ji zasu ci kakansu a dakin cen"

Firdausi na dariya ta ce" gwarama su ci kakan nasu yaren cen sai ita, kim ga wai yadda Hasan ke cika yana batsewa, ni kuwa na gaura masa mari , shegen yaro kai ba dan kowa ba sai shegen hobara?"

Baba ta ce" Kin ga, ki rufawa kanki asiri da dukan ƴaƴan nan walahi a kansu sai mamansu ta zaneki tsaf idan ya so in me za'ai mata a yi mata"

Firdausi ta ce" Na ga kat, dan walahi da ya je ya rukunkumeta harda tara hawaye a idannuwanta ta min kaca kaca tace aa bata son wasan duka in daina dukansu, in masu nasiha in masu addu'a ya isa, fadama ba'a yarda na yi ba"

Baba ta ce" Kadan daga soyayarta da ƴaƴan nan, Allah dai ya biyata sannan ya shiryeta, dan baki ga yadda maganarta ke cenza yannayin mijinta ba, muna magana da karsashinsa da na kamanta hirarta nan take yannayi na rashin jin dadin mu'amalarsu ya bayana a tatare da shi, na tabata abinda ke zuciyarsa dangane da ita mai girma ne, bana so wannan firgitaciyar y'ar ta kwace komai, Uman biyu kuwa na shirme"

Firdausi ta sauke ajiyar zuciya mai zafi, ta ce" Baba, walahi tana sonsa, rikicinta ne ya fi komai karfi a cikin lamarin, ama ai wannan hanya da ya dauko zamu gani ita ko shi wanda zai saki ya nemi sulhu"

Baba ta amsata ta mike tana mata salama dan so take ta yi ta je ta gayaci makota su tayata aikin nan tun yau a rarage

Yauma hakan ta kasance, sai da dare ya tsala ya shigo ya samu Firdausi na karatun Alkur'ani mai girma

Ya zauna suka gaisa sosai, ya karra yi mata nasiha da rarashi a kan lamarin rayuwa, sanann suka tatauna a kan lamarin abinda suka tatauna da Baba
Sosai Firsausi ta ringa kuka tana sake dukawa tana yi masa godiya, har sai da ya nuna bacin ransa ya fara fada sannan ta share hawayenta ta shige kamar yadda ya umarceta

Tana shiga bayi ta wuce ta dauro alwallah ta haye saman salaya ta shiga Adu'a a kan wannan mutumi da yayarta da dukan alkhairin dake tare da su

Shi kuma abinda ya saba ya yi, yaransa ya yiwa adu'a sosai sannan ya karasa kofarta ya tura a hankali ya shiga

A hankali ya karasa bakin gadon ya tsuguna yana kallonta

Kumatunta yake kallo da ajiyar zuciyar dake masa nuni kamar ranta a bace ta kwonta

A hankali ya dora hannunsaa saman mararta ya shafa yana dan sakin murmushi

A hankali ya kai bakinsa ya manna mata kisss mai zafi a wajen sannan ya dago ya sake zubawa fuskarta ido da gashin kanta dake waje wanda ke wal wal wal wal na hasken duhunsa da kyansa
Chapter 74 · 0% Book details