← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 83

Sashe 24

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hasan din ya wani maka masa harara yana cicijewa ya ce" Ka kuma ce min karya sai na fala maka marin mutuwa a gidan nan, sa'anka ne ni wai? Baka wani kin karba ba, na farkonma kana mika hannu kana kallona ne kace Mama ta hanna, shi kuma yace ai Mama amarya ce bata son rigima ba zata yi maka fada ba, sai kawai ka amshe ka kama ci ko wanke ledar ba zaka yi ba, kai dai ka ji kunya!"

Baba Rabi'u na dariyar fadan biyu da baya karewa ya ce" Kun ga, yanzu dai ku je wajen Inna tana baya tana kiranku inaga ko me zata ce maku?, Ku je cen daga nan sai ku buga ball kun ji?"

Da sauri Husaini ya fara juyawa, Hasan kuwa mamansa yake ta kallo , gannin tunda suka shigo bata dago ta kalle su ba sai ya ji ya kasa motsawa

A hankali ABDUL RA'UF ya dan sake gyara tsayuwarsa yana karantar yaron

Har Hasan din ya juya ya dan fara tafia, sai kuma ya ga ya juyo ya dawo daa hanzari ya duka kusa da mamansa ya saka tafukan hannayensa biyu yana dago fuskarta

Abinda ke jikin fuskar nata ya sinsina sai kuma ya yi murmushi ya kalli Baba Rabi'u ya ce" Har gabana ya fadi na zata kuka take yi"

Baban kansa sai da ya ji abin a zuciyarsa, yaro ne fa karami Hasan, ama irin yaran nan masu nacin uwa
Dukkan motsinta a jikinsa a ransa, a bayane zaka ga shi din mai bata kariya ne duda karancin shekarunsa, dan uwansa kuwa a bayane zaka fahimci mai bukatar a bashi kariya ne a dukkan al'amarinsa

A hankali ta dafe hannunsa muryarta cen ciki ta ce" Fadeel tafi mana"

Sake tsura mata ido ya yi, sosai ya so fasa zuwan, sai dai daure fuslar da ta yi ya saka shi mikewa ya tafi yana waigenta

Babanma sake mikewa ya yi yana jadada mata kalmar biyayya da hakuri, in sha Allah zata ga ribar abin

Ita dai bata ce da baba ufan ba har ya fice a gidan shima
Ta jima tana kallon waje daya, sai kuma ta mike tana dingisa kafarta da ta yi tsami ta nemi nufar dakin da aka bata dan ta harhada komatsanta ta san inda dare ya mata tun yau, ba da ita ba wannan rigima, ita? Ina ba da ita ba!

"Ke zo nan" ya fada a kausashe yana saukowa gaba dayansa ya nufi babar kujerar dake falon

Wani wawan birki ta ja ta ci, ta juyo a haukace cikinta na curewa waje daya

Daga sama har kasa ta debo dubansa ta sauke masa kafin ta yatsina fuska ta juya da nufin tafiyarta

A kausashe yana tsatsareta da kakausan kallo, muryarsa na kausasa ya sake fadin" KE ZO NAN NA CE!"

"Ba ke sunna na ba malan, sunnana AMINA!" Amina ta fada bayan ta juyo ta dafe kugu da hannunta na dama zuciyarta na tafarfasa tana sake kallonsa yadda ya wani hakimce

Hannunsa ya watsa irin du dayan nan , da idannuwansa ya yi mata nuni da wajen da yake nufin ta zo ta zauna

Sosai ta zo yin tafiyarta, sai dai wani tunani da ta yi cewa ta yiwu ya sawake mata ta kama gabanta ya sakata dawowa ta zauna, ama ba a wajen da ya nuna matan ba tana kafe waje daya da ido

Sai da ya sake kare binta da kallo yana ta nazartarta, yannayinta, girman fitsararta ( bai san a kansa kadai abin ke tashi ba ), sai kuma ya kada kai a rarabe ya ce" Kin san bana ra'ayin haka , gana daya hadin bai yi maching ba ko?"

Amina ta juyo tana kallonsa, kallo daya ta masa ta dauke idannuwanta tana fadin ' Ni da kaina abin ya kasa zaunar min a cikin kwakwaluwana, wannan wani irin gaurayen abinda basa kamanceceniya ne?"

"Ko?" Ya fada yana dan dage girarakinsa biyu

"of course, menene ke damun Baba fisabililahi da zai tashi ya dauki kannin bayana ya bani a matsayin miji?" Ta fada wannan karron tana kureshi da manyan idannuwanta
Wani irin haushi idannuwansa ke bata, irin kallon kasa kasan nan kamar tsohon kwarto ke bata haushi, bayan shi din bai tafasa bama bale ya kone, irin yadda yake yin kallonsa ke matukar kume mata zuciya da wuya, haka ta yi ta babatun magana a office dinsa ta zatama kurma ne ashe wai yana ji dan tsogon wulakanci da yarinya, ai sai ka yi fito na fito ka rama abinda na fada maka kau?

Da haushi haushi ta juyar da kanta tana son jan tsaki, domin har ta hade labanta ta basu kalar turowa kamar za'a saka ribom tana shirin bude su kadan dan iskar da zata samu hanyar shiga ta tsakankanin hakoranta dake cije ta samu hanyar shigewa ta bada amon tsakin ta ci ya ce" Kin san tsaki raini ne, bai dace ka yiwa danka bama shi ko AMINA?"

innalilahi wa inna ilaihi rajune, yaron da ya dace ya kireta da aunty ne yau ta yi faduwar tasar da wannan raini mai zafi ke shiga tsakaninsu? Shin me ta yiwa Baba ne? Du datijan dake zagaye da shi ya gaza dauko daya ya bata sai jinjirin da bai wuce goyo ba? , Shagwababen gaban kaka wanda a kansa kakarsa sai ta tada duniya? Uhum, dama Hajia ta kwontar da hankalinta, da ta daina daga hankalinta a kan abinda ba zai kai gobe ba!

A kausashe tana mikewa tsaye ta dube shi ta ce" Ka san a kan mutuncina babu abinda ba zan iya yi ba, kudinka ko masu tsaronka ba su zasu hanna na rama ba idan na ga za'a wulakanta min girmana ba!, So kawai mu mutunta junna kowa ya tashi da mutuncinsa, ni dai ka san na girmeka nesa ba kusa ba, rashin sanni ne ya biyo ta nan da mu, yanzu da aka sani farar takarda sai ta sameni a ciki, bana son sa in sa da kai, domin ba mutunci bane ka gane ai!"
Irin ta yayaba maganar nan, tana jira a yayaba mata ko ta samu ta sake amayar da takaicinta ta huce, sai ya karra tafka mata abin haushin nan ya sake yi mata shiru kuma yana kallonta

Walahi kamar zata fadi ta saka ihun kula ta kama bori daga nan har bakin titi
Wayo Allahna wulakancin dan Adam, dan tana talaka? Dan tana marainiya za'a yiwa haka?

Juyawa ta yi da karfi karfinta ta nufi ciki, sai kuma ta dawo wuuuuuu ta warci dan kwalinta da ya fadi a kasa ta yafawa kafadunta ta sake hararar gefen da yake zaune ta kuma wucewa cikin dakin nata

Murmushi ya yi ya maida kansa baya yana lalubar wayarsa dan ya kirayi direbansa ya zo ya kaishi gida ya yi wanka ya cire kayan maikon nan ko zai dawo cikin hayacinsa, ji yake abin na kama wuyanda sosai walahi, to ita du mayukan duniya ta rasa na shafawa sai wannan?

Kai ya sake girgizawa kasa kasa ya furta" Yarinta kennan, kanwar hauka, Allah ya sa kar na karya y'ar mutane kafin na salameta" ( na shiga uku ni sajidede)

Amina na shigewa dakin ta ja kofar ta rufe da karfi sannan ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta ta silale a jikin kofar a hankali kuka mai daci na neman kubce mata ta ji wata zazafar dankwasa ta sauka a dandin kanta

Da sauri ta dago gefen da ta ji abin zuciyarta na yankewa da faduwa da tunanin ko biyota ya yi ta rufe dakin da shi? Harda fargabar ko shine ya rafka mata dankwasar nan? To abu da yaro babu abinda ba za'a gani ba, sai ta ga Baba Lauratunta tsaye a kanta tana yi mata harare irin na fil'azal , harare na usulin kwararru a fannin juyar da ido bakin dake cikinsa ya bace bat farinsa ya tsaya yana mata mar mar mar

"Ke yanzu in banda mayar da kai shashasha da neman fitina yarinyar nsn tunda na shafa maki abin nan kika bace min da azuminki a bakinki sai yanzu zaki shigo? Ina kika je kika zauna sai yanzu zan ganki ta nan? Ni me kike son mayar da kanki ne Amina? Gyaran nan inace ke kika koya min kin fini sannin yaya ake yinsa, shine zaki dauki kafa ki je cikin mutane a haka? Kin ganki kuwa? Kin ga da abinda kike kama? Daga ina kike ne?" Baba lauratu da ta biyo ta hanyar nan dan ta katse balin Aminar, domin abubuwan da duka faru babu wanda bata gani ba, karshema da ta ga rigimar ta koma tsakaninta da Sarkin samarin ne ta yi wuf ta shige daki dan ta san daga cen nan zata biyo, domin ta sani ne babu wanda zai risinawa dan uwansa a yanzu

Amina dake dafe da kanta ta wani langwabe kai hawaye na ziraro mata ta ce" Aya, da kin san abinda na jiyo da sai kin yi takaicin bata naira dari ukunki wajen siyo madarar nan kika hada abin nan kila shafa min, da kin san abin kunyar da ya tunkaroni da kin tayani kuka Baba"
Chapter 24 · 0% Book details