← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 83

Sashe 70

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi ya shigo din yana fadin" Kai kai kai masha Allah, uman biyu wai kwonci tashi yau Rabi'u ya aurar da jikarsa mai sunnan Kulu, ni kam a da idan yar ta zo gaisheni sai ni kadai na ringa yunani, sai na samu kaina da tunanin oh sunna zannen mutun, to Uman biyu zanen mutun mana yarinyar nan baki ganta ba yar tsakure da ita yar kadan, ama akoy iya kwaliya da daukan wanka fa iya tafia , wani lokacin sai ka yi zatonma yar faransa ce"

Maman Biyu dake sauraronsa tana binsa da kallo har ya nemi waje ya zauna yana zuba sam bata gane ma maganar wa yake yi ba, ita abinda ke ranta yana ranta ne

Baba ya idasa zama yana fadin" Ya zuljalalu wal'ikram"

Dubansa ya maida wajen Amina ya ce" Uman biyu yau fa inada shekara Saba'in da kwanaki a sama, tsufa kam ya zo, Alhamdulilah, Allah dai ya sa mu yi tsufa mai alkhairi mai tatare da abin alkhairi sannan ya sa mu cika da kyau da imani"

Amina ta bude bakinta a hankali ta ce" Amen Baba"

Dabinon dake ajiye ya mika hannu ya dauko ya bude shi sosai yana kallonta ya ce" Maman biyu amshi ki ci dabinon mana"

Amina ta kalli dabinon, haushinsa da son cinsa na mata yawo a zuciyarta

A hankali ta girgiza kai tana son sadda kanta

Baba ya ce" Ba kyau ai mayar da hannun kyauta Baya, amshi yar albarka maza amshi, bara na dauki biyu nika na dandana, irin dabinon nan irin dadinsa, gashi bashida ila shi dabino ko kadan "

Tana kallonsa ya ciri biyun ya fara ci

Jiki a mace ta rarafa ta amsa ta koma ta zauna ta bude ta shiga ci
Ci take yi har tana lumshe idannuwanta, shi kuma Baba yana kallonta yana murmushi har ta kai koshi, domin yanada yawa a nanage yake, ga ruwa gefe na goran da ABDUL ya bata ajiye ta dauka ta kora tana jin yanzu kam batada wata matsala a duniyar da ta wuce maganar ciki,

Murmushi Baba ya yi zuciyarsa cike da farin ciki ya sake mayar da dubansa kanta bayan ta gama shan ruwan tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa domin cikinta ya cika ba laifi ya ce" Su Uman biyu sai kike dubi tsabar idannuwan kakar gwamna kika nuna bakya son jikanta da dan tayin shalelen da na tabata idan har kakar geamna ta yi tsayin rai sai kun ga kauna gannin idannuwanku tsakaninta da dan jikanta, shine nake shan dariya, oh dan fari kam sai shi"

A hankali ta fara shashekar kuka tana jan hijabinta ta kai wajen fuskarta tana sharewa

Tsakani da Allah wata irin kunyar baban ce ta kamata wace a dazu bata jita ba
Maganarsa ta doketa fiye da tunaninsa

A hankali tana shashekar kukan ta ce" Baba, ni fa ba wai cewa na yi na tsani kowa ba fa baba, kai ai ka sani Baba"

Baba ya gyada kansa yana fadin" Na sani sosai Aminar Gwagwo, nima ai na san zakiji kunya , to ama kuma abinda na gaza ganewa ta menece kunyar?"

"BABA Abdul kanina ne fa......" Ta fada tana rushewa da kuka

Baba ya kama bakinsa a hankali ya ce" Toh fa, haba ni kam nace kukan nan da kika samu Uman biyu ba kalau ba, ashe dai na gane, To Allah ya baki hakuri share hawayen mu yi magana kin ji?"

Kai ta gyada tana share hawayen tana sauke ajiyar zuciya

Baba ya sauke ajiyar zuciyar shima, yanzu kuma sai kalar damuwa ta bayana a fuskarsa

A tausashe ya ce" Shin dama bakya son hadin nan kika yarda na yi? Ko wani abu yake maki na cin zali ne ban sani ba?"

Amina ta rasa amsar da ta dace ta bashi, kanta a sade ta samu kanta da gyada kai da kuma girgizawa lokaci daya, irin amsar da mutun zai rasa me kake nufi, watau ita kanta a cikin rudun amsar dake zuciyarta take

Baba ya karra tausasawa ya ce" Amina, ba zaki iya zama da Aban Biyu bane? So kike ya sawake maki ne?"

Haba, kofa itace yar fari a wajen iyayenta ta dan halaci
A duniyar kaf bayan rasuwar iyayenta Baba shine wanda ya fara talafata, sai Baba Lauratu, sai daidaikun datijan anguwarsu
Mutumen da bai kyamaceta ba, bai nuna mata bambamci dan tana talaka ba, karshe yake cin abin hannunta da take jan ruwan rijiya ta girka masa, ya zo ya hada aure da ita da gudan jinninsa kwalin kwal wadda itace zata fadi girma da soyayar yaron a zukatan kakaninsa, idan ta bude baki a karro ba biyu ta yi wata wautar da kanta zata ba kanta amsar abinda ya dace da ita

A yanzu haka abinda yake faruwa tsakaninta da bawon Allahn cen ma gidan cen zata ce a maza da ta sani babu wanda ya kaishi kima a idannuwanta
Kawai ita dai bambancin shekarun nan ne baban damuwarta , bayansu batada wata damuwa da shi

Baba ya sake tausasawa gannin ta lume a tunani ya ce" Idan har wannan din shine burinki, ki sani, ni Uba nake a wajenki, da farko zan fara baki shawarar ki je ki yi nazari, ki yi dogon nazari na rayuwa, ki sani koda kin rabu da Abdallah ba zaki koma gidan cen ba wannan alkawarina ne, ni zan zame maki gata a gidan duniya har na bar duniya, kar ki yi tunani a kan kaka naka yi ta rayuwa , ina nufin ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhali, da dukkan hutun da ya dace........tunanin da zaki yi shine na mutuncinki, abinda yake cikinki, yayanki dake kiransa Aba, uwa uba shi din da kansa Amina......., Ki yi tunani a kansa da kansa kin ji? Ki auna ki gani, shin wannan mutun ya cencenci zama da ke? Na san ke ba jahila bace, ba zaki yi riko da karfi dan kar ace ba, ki saki maganar kar ace, ki gyara Amina............. Kar ki manta komai girman abinda ke tare da na farin cikin da kike sama masa wata na iya bashi, haka kuma wannan baban abin dake tare da ke mai daraja mai mahimmanci kina iya rage kimarsa a zuciyar mahaifinsa............., Idan har kika yi tunanin nan kika yanke hukuncin ba zaki iya zama da shi ba, in sha Allah zan sama maki nutsuwar zuciya kin ji?"

Amina da kanta ke kasa bata iya yin kwakwaran motsi ba tana sauraron Baba

Baba ya sake maimaita cewa " Uman biyu kina jina kuwa ?"

A hankali ta gyada kanta tana sake sauke ajiyar zuciya

Baba ya ce" Zaki je ki yi nazari a hankali ko?"

Kai ta gyada tana sake sada kanta

Baba ya yi murmushi ya ce" Masha Allah, ki cire damuwar komai a ranki kin ji? Zamanin nan da shegema am daina boyewa bale dan Abdul? Ai ni nan in fada maki shagali kawai da kakar Gwamna, na tabata yau idan ta fara sadaka harda ni"

A hankali Amina ta samu kanta da yin murmushi, domin irin yadda Baban ya yi dole ya saka ka darawa

Dan shiru ne ya biyo baya, a lokacin Hajia ta sauko daga sama da waya a kunnenta tana amsawa ta nufo falon ta karasa kusa da Baba ta zauna wayar a kunnenta dai tana amsa abinta

Baba kasa kasa ya ce" Ai in fada maki inaga harda party zamu sha"

Amina ta sake sada kanta gabanta na faduwa, tsoro ya cikata, tana ji kamar zata tashi sama dan tsoro ta tsere

Hajia na gama wayar ta sake Bin Amina da kallo sannan ta kalli Baba ta ce" Ita kuma me yasa bata bi mijinta ba?"

Baba ya yi murmushi ya ce" Zantawa muke yi, kin san yar dakina ce , zancen sirri muke yi ai"

Hajia ta tabe bakinta tana sake kallon kafafuwan Amina dake nanade ta ce" Ki mike kafafuwanki , ki daina dogon zama a haka, kuma kin ga miyar bikin nan da magi da komai kika tashi kika ci, ki daina haka yana da ila wa mai ciki kin ji?"

Cike da kunya da tsoro Amina taa gyada kanta tana sake sinne kan nata

Hajia ta dubi Baba ta ce" Kun gama sirrin ne Alkali?"

Baba ya dubi Amina ya ce" Uman biyu, mun gamaa sirrin ?"

Da sauri ta gyada kanta

Baba ya ce" To bakua marmarim waina, ko dambu, ko kauco, ko tafasa, ko agwaluma, ko rake dai da sauransu? Ko madasho bakya son ci?, Idan kina son daya ki fada sai Kakar Gwamna ta maki ko a siyo maki kin ji?"

Da mamakin Baba da neman rigima ta kafe shi da ido, tana jira ta ji saukar masifar matarsa kan yace wai ta mata abu ta ci? Sai ta ji shiru, asalima itama kallonta take kamar mai jiran amsarta

A sanyaye ta ce" Bana son komai Baba "

HAJIA ta dauki wayarta ta yi kiran Baba direba

Minti kalilan ya shigo, ta dauki kudi ta bashi tace" Ka kaita gidanta, wannan idan ta ga wani abin a hanya ka siya mata yadda zai isheta, Ke tashi ku tafi gida mana yama na karra yi"

Cicibawa ta yi ta mike tana kallon dabinonta da ya rage ta kasa dauka har sai da Baba ya ce da Baba direba ya daukar mata yana murmushi suka fice

A cikin motarma kanta a hade da jikin madubin motar ta lumshe idannuwanta tana jin maganar direba sai tambayarta yake yi me za'a siya? Ama ta kasa bashi amsa har ya gaji da yawatawa da ita ya kaita gidan

Tana fitowa daga mota Twins dake buga balll suka nufota da gudu sunna murnar dawowarta

Hasan ya ce" Mama, kin ga wai ball dim da dady ya siya mana? Mama dady dinmu yana sonmu, muma muna sonshi Mama"

A zabure ta kalle shi, Husaini ya katse mata kallon yana fadin" Bakiga fadan da ya yiwa prncipal din makarantarmu ranar da kb yace wai mu kamar shegu bamuda uba ne? Yace mata laifinsu ne da basa tsawatarwa yara har yaro ya iya fadawa dan uwansa haka sunna kallo, daga nan ai ya ciremu a makarantar yace shine ubanmu!"

Numfashinta ta ringa ji yana mata sama da kasa

A hankali ta ce" A makaranta ya cire ku?"
Chapter 70 · 0% Book details