Sashe 68
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya fito daga motar Hajia kuma ta zagayo duk suna kallonta da yi mata sannu a tare, dan dukawa ta yi tana yi harda rintse ido
yatsina fuska Risala tayi ta ɗauke kanta tana jin kamar zata yi aman itama dan kyankyami tana duduba jikinta kar aje iska ta dauko aman ta watsa mata a jiki tace "Cussss, wata ƙazama da ita."
Da yanayin kulawa Hajia tace "Dama ba ta lafiya ne ko kuwa abuncin cen ta kama ta yi ta nanaga??"
Abdul da hankalinshi ke kanta ne yace "Ban sani ba Hajia, sannu ko Amina? Taso ga ruwa" Ya sake fada ma Aminatu dake share fuskarta da gumin data fara hadawa, ta mike da kyar ta miko hannu ta amshi ruwan goran da ya dauko ya miko mata, hankalinsa gaba daya a tashe, sai ya nufota kamar zai rikota sai ya ga ta dan kauce dan idannuwan Hajia da kuma su Baba da suka karaso har suka zo summa suna tambayar lafiya?
Abdul ne ya fada mishi a taƙaice, hankalinsa a tashe, sannan yana ta auna abinda ke iya sakata a wannan halin, domin dukkan motsin Amina biye yake da shi sau da kafa
Ya fita sannin abinda ke tare da ita da dukkan hanyoyin da ya dace ace ya bi dan taimaka mata
A gidan Firdausi ta sani, Baba kauratu ta sani, su din da kansu sunne suke sake sakashi a hanyar da mai ciki keda bukata dan samun kwonciyar hankali irin su kwadayinta dai, da yan rigingimmun da na Amina ya zo mata da shi, domin bata laulayi sai na harshe da kuma ciye ciye
Da farko ita din da kanta ta fara damuwa da ciye ciyenta, sai kawai suka hada baki idan ta dan nuna yanzu batada aiki sai ci, sai a nuna mata ai hanjinta ne ya warware dole ta ringa ciye ciye, ai cenjin yannayin kennan
Sai kawai ta hau ta zauna, tunda ba taba yin cikin ta yi ba, bata sani ba ai
Ba zai manta lokacin da ta ce tana son cin abincij nan da ake kira da ABACHA na Yoruba, kafin a samo masa mai yinshi ta yi aman nan
A hankali ya kalli Hajia yace "Ina ga fa kamar dabinon da kika ci ne ya jawo hakan."
Da wani kallo ta bishi ta ce "Ban gane ba? Guba na ci ne? To me ya hada cina da amanta"
Girgiza kai yayi yace "A'a, nufina ko tana so ne, dan na ga tana ta kallo"
Kallon Amina tayi tana mata kallon sama da kasa, aman da ta yi ta kwaye hijabin da ya rufawa dima diman duwawunta asiri , yanzu da ta dan duka suka dan bayana kadan cikin tsalelen lesh din dake kasa wanda aka yiwa dinkin doguwar riga ya kamata sosai dan dinkin kamar cif da cif ne a jikinta tace "Sai ka ce wata dangin mayu? Dan kawai tana so sai ya kaita ga amai."
Murmushi Baba mai Shanu yayi Abdul kuma ya kyaɓe baki ransa na neman bacewa
Baba mai Shanu ya sake duban Amina da kyau, juyawar da Hajia tayi za ta shige cikin Baban bangarensu yasa Alhaji faɗin "Au! Ba za ki bata dabinon ba Hajajjuna?"
Juyowa tayi duk sun tsatsareta da idanu, sai kawai tayi kamar za ta fashe da kuka tace "Saboda Allah me ye haka? Kawai daga ganin abu sai a ce shi ya sakata amai, to idan na bata ta ci ta kara amai sai a ce ni ce kuma ko? Ga dukkan alamu itama yarinyar nan ba wani kaunata take yi ba ake min dole sai na sota"
Girgiza kai Mai Shanu yayi yace " Bafa haka ake nufi ba ke kuwa, Kin manta lokacin da kika taɓa ganin goriba a hannun almajiri daga mun tsaya a bakin danja?"
Ƙura masa idanu tayi irin tana son tunawa, sai kuma tace "E, lafiya?"
Saida ya saci kallon Abdul yace "Da na hana miki saboda a ganina a hannun almajiri yana cin abinsa yaushe zamu tsaya ya baki goriba tsakani da Allah, ba saida kika kwanta asibiti ba?"
Da yanayin rashin fahimta tace "E, sai me to ai a lokacin ni banida lafiya ne"
Shafa wuyanshi yayi da hannunshi mai carbi kamar mai rad'a yace "Sai ya zama dalilin da ya kwantar da ke ne ita ma ya sakata amai ai ur excellency ."
Zazzaro idanu tayi ta kalleshi da kyau, sai kuma ta maida dubanta kan Amina da ka rantse kuɗin aika ta ci tana tsatsare Alhajin da kuma Hajia da idanu, da muryar rawa rawa ta nuno Aminar da yatsa tace"... ke ciki ne da ke?"
A zabure Amina ta muke tsayinta gaba daya tana kwalalo idannuwanta, Risalama ta juyo a zabure gabanta ya yanke ya fadi kamar zai fito ta bakinta
ABDUL kuwa a nutse ya yi taku biyu ya tsaya jikin mota ya zubawa Amina ido zuciyarsa na begen abinda baya kwana da shi bale tashi da shi a zuci
Baba kuwa murmushi ya yi ya sake tsayawa kan kafafuwansa lokaci daya shi da Amina suka yi magana,
Amina ido a waje tana dafa kirjinta ta ce" Wa ni? Aa aa banida komai......m"
Baba kuwa ya ce" Kwarai kuwa shine dai "
A haukace Amina ta juya barin Baba ta ce"
Murmushi ta ringa yi tace "Baba, da gaske nan ɗin anan Auntyna take zaune? Yanzu wannan duk ni kaɗai?"
Murmushi Baba ta sakar mata tace "Ke kaɗai Firdausi, ai ina ga ma idan bai miki ba za'a iya canza miki."
Murmushi ta ƙara saki tana sauke numfashi a hankali, gyara tsayuwa Babar tayi tace "Bari na je na samo miki abinci, ina zuwa."
Da kallo ta bi Babar tana sake duban iya ƙofar ɗakin kawai, ba jimawa Baba ta dawo da abinci ta aje a gefenta ta taimaka mata ta zauna da kyau sannan ta zuba mata ta ci ta ƙoshi saboda Babar na sake nuna mata mahimmancin ƙoshin na ta a halin da take ciki, tana gamawa ta ɗauke kwanukan za ta fita tace "To yanzu ki kwanta ki huta, haka aka bani umarni."
Jinjina kai tayi da farin ciki tace "To Baba, nagode sosai."
Juyawa tayi ta fita ta sake rufo mata dakin ita kuma ta gyara ta kwanta tana lumshe idanu don neman bacci ido rufe.
_________________
Daga yanayin zaman nashi zaka san lallai yana girmama na sama da shi, ƙara gyara zama yayi yana murmushi yace "To shiyasa na ce bari na kiraka na ji, dan na ga shirun yayi yawa, ita tana zaune haka kuma ko sau ɗaya ban ga ka zo ko dubata ba."
Shiru yayi kanshi sadde ƙasa yana mamatsa tafukan hannayenshi da suka ɗauki sanyin acn mota daya fito daga ciki, kamar ba zaiyi magana ba saboda lokacin da ya ɗauka bai ce komai ba yana nazari kan lamarin na Risalah da mamanta, sam ya salewa lamarinta tunda ta masa wannan terere, a ganinshi sam bai cancanci ta masa haka ba, hakan ma da ta yi ba birgewa ba ce, ita ba ta fi ƴar uwarta sanin zafin jikinta ba, yadda ya je mata haka ya je wa ƴar uwarta, amma sai da ta sanar da duniya abunda ya faru, daga ƙarshe mamanta ta zo ta wani kwasheta suka bar gidan, to me zai musu? Ya dinga zaryar zuwa ganinta yana rawar jiki a kanta? Sam hakan baya daga cikin tsarinshi.
Ɗan siririn numfashi ya sauke kafin cikin nutsuwa yace "Abba ni ban san da zuwanta gida ba, ban ce a tafi da ita ba, shiyasa ma ban zo ba."
Kallo mai ɗauke da mamaki ya bishi da shi jin abinda ya ce, sai ya ji kunya na son rufeshi na abinda matar tasa ta aikata, sam bai ɗauka ta ɗauko Risala dan ra'ayinta bane, hakan yasa shi ɗan sadda kanshi yace" Ah to shikenan ai, ina ga tunda ta ji sauƙi ma zaka iya tafiya tare da ita ko?"
Shiru yayi na wasu daƙiƙu da tunanin shin ya tafi da itan ne? Samun gamsashiyar amincewa yasa shi jinjina kai alamar to amma bai ce komai ba, tahi yayi ya shiga ɗakin matar tashi inda anan Risala ta fi zamanta tunda ta zo gidan.
Yana shiga ya sameta zauna kan gado tana daddana waya fuskarta cike da damuwar shareta da Abdul yayi, mayar da dubanshi yayi kan Mamanta data fito daga banɗakin kanta ɗaure da ƙaramin towel.
Dantse leɓenshi na ƙasa kawai yayi ya sake duban Risala da ƙarar ƙofar ne yasa ta kallonshi tace "Abba sannu da zuwa."
Fuskarshi a haɗe ba alamar wasa yace "Tashi ki shirya ki bi mijinki yana nan falona."
Rarako idanu tayk da mamakin dama Abdul ya zo gidan nan ne? Shi ne bata sani ba, Mamanta kuma a sukwano ta nufoshi tana aje towel ɗin tace "A'a! Ban gane ba Abban Risla, ya za ka ce kawai ta tashi ta b..."
Irin arnen kallon daya jefo mata yasa ta ɗauke kanta tana harareen bango, Risala ya sake kallo a tsawace yace "Malama zaki tashi?"
Da sauri ta shiga kiciniyar saukowa daga kan gadon ta zuro ƙafafunta ƙasa, wajen kayanta ta nufa da Mamanta ta aje mata a nan ta zaro dogon hijabi ta saka akan dogon wandon dake jikinta da ƙaramar riga, jakar kayan nata ta ɗauka da sauri ta kama hanyar fita.
Ta cika iya cika tamkar za ta fashe tsabar hassala, saida Risala ta bar ɗakin sannan ta sake kallonshi da yanayin ɓacin rai tace "Abban Risla, a gaskiya ni baka kyauta min ba, ya za ka wani ɗauketa ka miƙa masa haka kamar wata yar tsana? Yaron nan kwanan Risala nawa amma ko sau ɗaya bai zo ya dubamu ba, shine daga zuwanshi za ka ce ta je kawai, kenan ma an bashi dama ya sake wulaƙantata?"
A matuƙar tsawace cike da ɓacin rai yace" Ya wulaƙantatan, ke yanzu dama ba shi ne ya ce ki ɗaukota ba shine kika taho da ita nan? Anya kuwa kina nemawa kanki mutumci da daraja a wajen mijin ƴarki? Me ye ya faru? Kasheta yayi ne da san an ɗaukota nan? Haka kawai ki dinga ja wa mutane zagi."