← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 83

Sashe 8

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gefen da mijinta yake ta sake kallo, wannan karron abin ya taso mata daga cen kasan zuciyarta tana kallonsa ta ce" Ama ai sai ka yi masa magana ko Alkali?"

Wainar da ya ciro ya dangwala miyar taushen ya sake kaiwa bakinsa, domin tuni ya fara karyawa da ita ya juyo inda take zaunen,
Walwalin da take yi abin birgewa ne, ita din mace ce mai kwaliya, sam fatarta bata samun hutun rashin gyara, tun tana da jan sawunta da ya daukota ita din mai kwaliya ce, har yanzu da ta kawo shekaru hamsin da hudu a duniya ba zai ce ga wata macen da ta kaita iya saka kwali ba a idannuwansa, yyarintarta yake ganni ainun, a kanta ya gane bak'ar fata aba ce mai daraja da mahinmancin da ko ta zo tsufa idan da gyara sai shekaru sun yi mugun ja take nunawa, ita din ba farar mace bace, ama irin yadda ta iya daukan ado da gyara da ba kalar fatarta daraja ko farar fatar na mangarinta
Da yawa masu shekarunta sun koma sun jabge, wasu tsabar lalaci da son jiki sun fake da sun tsufa ko kunshi sun daina yi, ama ita din wannan tasan da a yanzu shi tsufan ya masa zuwan gaske ita a danya sharat yake ganninta, baban damuwarsa idan ya kwonta dama shine ya bar wannan abokiyar rayuwa tasa mai wasu halayan da yake gannin hagu a tare da ita, giyar mulki , kaunar siyasa ba yau ba suka yiwa jinninta billin da ita da kanta bata fahimta ba!, Gatanan dai a zaune a kan siyasa sai ku haura sam ku fado wuyan kowa ya karye a huta, a yanzu haka rigimar da take kokarin janyowa a tsakaninta da jikan nata da ta san mutun ne mai zaune da ra'ayin kansa, wanda ya ki jinnin wani ya nemi yin iko da shi, shi yasa ya zama mutun mai ikon kansa da kansa ta hanyar kasancewa bos din kansa yake *NEMAN NA KANSA* da karfinsa da kuma guminsa ba tare da ya jira wani ya masa ba ko ya yi jira an bashi damar yi ba, shi din mutun ne da ya ki jinnin a ja shi a kasa a kan komai, shi yasa yake nema da karfinsa da kuma lokacinsa, wannan miskilin jikan nata take so ya tashi ya nemi takarar gwamnan garin nan, tana so ta bara masa wajen da take nema a cewarta aljihunta bashi da nauyin yin farfagandi, kuma bata da matasa a damarta , shine take so shi ya motsa ya bude aljihun wandonsa ya yi zuba na kudi sannan ya riko matasan dake tare da shi su hau wannan tsani mai nauyi da hatsarin gaske, dan kawai wannan din shine *Burinta!*

Sai da ya taune ya hadiye ya yi dan murmushi yana fadin" Watau yarinyar nan Allah ya kara mata lafiya, a kulun abinda ke bani mamaki da wainarta bata konewa, bata yin yami, bata cika siga, idan kuwa ta rangada mata miyar taushe sai na ji du duniya babu miyar da ta kaita dadi, mahaifiyarta ta mata horon arziki, ita kam ta huta idan ta yi aure ba zasu samu matsala da miji ba wajen girki, mu kuma maza dama a kware wajen girkin kadaima ya wadatar"

Wani irin tukuki ke turnikar zuciyarta tana kallonsa, lalle ta yarda bashi da kiyar kama mata a kan maganar nan, bayan ta san yaron na girmama maganarsa koda da salon wasa ya yita?

Mikewa ta yi ta dauki jaridarya da gilas dinta ta maida a idannuwanta ta juya ta nufi ciki cikin takun nutsuwarta ba da fuuuuuu ba dan ranta ya baci, no, da salo irin na wayayiyar macen da ta gane idan ranta ya bace gwara ta yi shiru da ta daga muryarta ya zamto an samu mumunan furuci daga tsadafen bakinta ba!

Da ido du suka rakata, sai kuma suka yi ido hudu shi da kakansa

Goshinsa ya tatare sosai yana kallon kakan nasa
, Dubansa ya maida wajen agogon dake bango ya duba ya sake juyowa wajen da yake ya ce" Sai yanzu kake karyawa bayan kana fama da ulcer?"

Fuskarsa ya yatsina ya ce" Ka san kuwa tunda safe nake jin yinwar, har mafarkin wainar nan na yi, yau maman biyu ta yi rana shi yasa"

Takardar ya mayar gefe gaba daya yana fuskantarsa , sai da ya gama ayana abinda zai fada masa a zuciyarsa sannan ya ce" Bana so,......"

Ya yi shiru jin saukowa daga sama ya maida dubansa yana kallo, kakarsa ce ta fito cikin tsadaden shiri da abayarta mai walwali ga kanshinta dake sanar da zuwanta tun kafin ta iso
Karasa saukowa ta yi daya daga cikin yan aikinta na biye da ita rike da jakarta ta tsaya tana kallon table din ta ce" Ki tatare breakfast din cen, a yi masa na rana, kar a cika mai sannan kar a saka masa magi da yaji a ciki, a dafa masa cuscus da miyar lambu......nd a tabatar an saka turaren wuta a ko'ina idan ya gama cin abincin"

Cike da ladabi take amsata , sai da ta tabatar da cewa ta gane komai sannan ta sake juyowa barin da suke zaune
Idannuwanta suka sarke da na jikanta, tarin damuwar dake tatare da ita ya fara karanta, sai kuma juyawar da ta yi ta wuce ba tare da ta ce da su komai na, uwa uba ko tambayar izinin fita bata yi ba a wajen mijinta ta kada ta yi tafiyarta ya saka shi rakata da kallo, sai kuma ya dawo da maganar da ya fara ya ce" Bana son kana zama har wannan lokacin baka karya ba, Waina, waina waina, na yi na yi na kawo ma'aikatan da suka kware wajen sarrafa waina su ringa sarafa maka ka kiya"

Sosai jikan nasa ke saka shi a hali na kwonciyar hankali da farin ciki, uwa uba idan ya ga yana magana a kan abinda ya shafi lafiyarsa ko kwonciyar hankalinsa, tamkar wanda ya take shekara hamsin a duniya, rashin hayaniyarsa da tauna hharshensa wajen magana da matukar son girmansa na sakashi manta shekarunsa a duniya
Murmushi ya yi masa ya ce" Babu mai wainar da zata fi Maman biyu iyawa a duniya, bayan wannan na yarda da tsaftarta ne ai"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ja bakinsa ya yi shiru yana kallon abincin da kuma irin cin fa kakansa ke yi

Mai Shanu ya ce" A zuba maka ne?"

A hankali ya girgiza kansa harda yatsina fuska, kwarai shi din mai matukar son abincin gargajiya ne, ama ba zai taba iya cin wanda bai yarda da shi ba!

" Me yasa ba zaka yi mata biyaya ba ka shiga farfagandin da take da bukata?" Mai Shanu ya fada a tausashe bayan ya wanke hannunsa , ama bai sha ruwa ba , domin idan ya ci abinci baya shan ruwa a lokacin sanadiyar ulcer dinsa

Yatsarsa ta tsakiya yake dannawa a hankali har sai da ta bada kara sau biyu sannan ya juyo gefensa a hankali ya ce" Saboda da na rintse ido ban ji ba dadin makanta"

Mai Shanu ya girgiza kansa yana fadin" Ka bani a bude yadda zan fahimta"

A tausashe, ba da yannayi na raini ba, ko isa, ko haikewa a kan maganar kakan nasa ya ce" Ita din misali ce a kan kalar rayuwar da ba zan so ta gabata a kaina da iyalina ba, ita din aya ce mai karfi da nake kokowa da ita dan burina ta farga ta zubar da dabi'un da ba adininta ba!"

Mai shanu ya sake fuskantarsa ya ce" Wadine daga cikin dabi'un tawa matar ne baka so su zamto abin koyi a wajen naka iyalin?"

Dan murmushi ya yi, domin ya fuskanci kakan nasa na son jan maganar ne kawai, ya gane komai ama sai takewa yake yi, yau hira yake ji sosai shine yake so ya yi ta jansa a kasa dan fin karfi, sai dai shi din kansa yana so yau Mai Shanu ya fahimci siyasa ba ra'ayinsa bace, ya yiwa matarsa magana ta barshi haka, idan maganar kudin ce zai zuba mata ta je ta gwada sa'arta, ama zai yi ta adu'ar kar Allah ya dafa mata a burin zamowarta gwamnar garin nan!
A tausashe ya ce" Ni fa ba nufina matarka nada matsala ba Elhaji"

"Aboki, ka yi maganarka sak, idanma iyalin nawa kake nufi da wata sirfar sai na baka amsa daidai da bayaninka, ai ka san baka kam ba tsami " mai Shanu ya fada shima yana murmushi
Chapter 8 · 0% Book details