← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 83

Sashe 47

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ABDUL dai da ya yi shiru baisake ce masa komai ba, dan ya kula Mansur sai wani nemansa da masifa yake yi, wai wani ya dauki magani dan kawai ana cewa ko namiji idan dai yinsa na farko ne yakan fadi rashin lafiya, ya manta ba kowa da kowa ba? Hm!

Sai da Mansur ya tafi sannan Abdul ya sake mikewa daga zaunen da yake ya karasa kusa da wayarsa ya dauka ya sake gwada number kakarsa
Sai dai still bata daga ba
Murmushi ya yi ya yi kiran mijinta suka sake gaisawa a mutunce sannan ya ce" Tsoho, ina fata ka leka asibitin wajen Hajia?"

Baba Mai shanu ya kadakai yace" Ka ganni nan a gidan gona bangaren shanu mun kada shanu ni da Rabi'u muna rakasu kiwo , ka san me Abdallah? Wannan rufe shannu da kuke yi ku yan birni bashi da wani anfani, shi yasa shanayenku basa sakin karinsu su dauki girman jiki sosai............., Abincima kulun kunna kayade masu wanda zasu ci ta yaya kuke so su yi kiwo?"

"Baba, kalli wancen farar ta ki yin gaba ta ki yin baya sai wani irin abu take yi" Muryar Husaini ta shigo cikin wayar, sai kuma muryar Baba Rabi'u yana fadin" Aliyu wancen fa haihuwa zata yi, ka ga fa ta hau gwuiwa"

Baba da dan sauri ya karasa yana sauraron ABDUL dake fadin" TWINS na tare da kai ne?"

Baba yace " Eh ai daga makarantar tasu nake na dauko su sai muka wuce nan "

Dan shirun ya sake yi, sai kuma ya samu kansa da fadin" Ina iyayensu suke?"

Baba ya dakata da tafiyar da yake yi dan tambayr ta zo masa a ba zata, kwarai ya dan zai tambayeshi hakan , dama da gangan ya boye masa dan yana so ya fara gane idan har yaron ya fara damuwa da wani abu nata , duda ya san zai yi wahala ama kuma yana tunanin idan har ta samu gurbin zuciyarsa sai ta yi fata fata da duk wani tanadinsa

Yana kallon yadda ma'aikatan ke taimakawa sanuwar dake dan fitar da kuka irin na sanuwa mai karfin nan tana ta faman haihuwar ya ce" Umansu ba tana gidanka ba? Ko dai basu je ba da na turo su ne? Likitan ya ganta kuwa?"

ABDUL ya dafe gaban goshinsa a hankali ya ce" tell me father, ka fada min abinda ka san ina son ji mana?"

Baba ya yi murmushi ya ce"
*NZL PAGE3️⃣0️⃣*

A raunane tana kallonsa ta ce" Ka ga, ko a anguwarmu ni bana wasan maza, bana shiga harkar maza, dan haka dan Allah ka fita a harkata kafin ka bani takardata, ka daina yi min maganama kwata kwata"

Sake matse mata waje ya yi hakan ya saka AMINA, da girmanta da komai ta kwala ihu tana rintse idannuwanta, domin ita abinda ta yi tunani daban, sai ta ga ya tsaya yana kallonta

Tana bude idannuwanta suka sake yin ido hudu sai ta ga ya sakar mata murmushin da ko a gaban sarki aka gurfanar da ita zata iya rantsewa murmushin rainin wayo ne

Juyawa ya yi bai ce nata komai ba ya kama hanyar ficewa

Har ya kama kofar ya dakata ya juyo kasa kasa yace " Ki tabatar kin saka masu kayan barci sannan ku masu addu'a ki rufe masu dakinsu"

Baki bude take kallonsa zuciyarta na raya mata abubuwa irin na rashin kunya da ya dace ace ta yayaba masa ko zai shiga hayacinsa ya gane yarenta

Bai bar dakin ba sai da ya sake fadin" Kar ki saki ki hada daki da su AMINA"

Ido ta kwalalo tana kallon kofar da ya rufe ya fice ta karaso tana fadin" Idan na hada din sai me? Ina ruwanka da hada dakina da y'ayana? Malan sai shishigi ni zaka nunawa raini? Ka bari na warke walahi sai na koya maka biyaya wa manyan gabanka, kuma zalina da kake ci kai da Allah.....shima Hasan....Hasan? Hasan?"

Ta nufi dakin da aka ce nasu ne wanda ko shiga bata yi ba tanai masa kiran da yana ji ya yi turus dama fitowarsa kennan daga wanka Husaini kuwa yana ciki

Tana shigowa ta ja da mamaki tana kallonsa
Rigar wanka ce a jikin Hasan jama'a ya wani yi fresh kamar dan yan gayu na kasa da kasa shi kadai sai shinning yake ga abin ruwa dake nuna fitowarsa kennan a wanka

Farin cikin ganninsa a haka ya so mantar da ita abinda ta shigo yi, har sai da ta zauna gefe ta tuna sannan ta sake hade fuska ta ce" Kai zo nan, zo nan"

Fuskarta yake kallo kafin ya shiga matsowa ya tsuguna a gabanta
Tsayinta ta rage tana sake hade fuska ta ce" Waye yace maka ka ringa fadawa wancen dady?"

Dagowa ya yi da mamaki yana kallonta, sai kuma ya ce" Ba dady bane Mama?"

Amina ta yi tsuru ta rasa amsar da ya dace ta bashi

Hasan ya sake soke kansa ya ce" Dama dazu ne da yama ya je cen gidan gona, shine Baba yace ga dadynmu nan, muka ce masa akace dadynmu ya rasu? Sai yace eh wancen ya rasu, yanzu kuma ga dadynmu nan, mu je masa dady, ni dai sai nace masa dady sai yace da gaske ina so ya zama dadyna?"

Amina dake kallonsa tsigar jikinta na kwonkwoncews tana sagewa a hankali ta ce" Sai kace me?"

Sake dagowa ya yi yana kallonta, sai ya sakar mata murmushi ya ce" Mama, kin manta dama munna ce maki mune bamuda dady a school? Yanzu muma fa mun samu kennan?"

Zuciyarta ne ta ji ta yi mata nauyi, amsar da yaron ya bata kuwa ta tabatar mata lalle baban burinsa ne ya cika, domin karara take karantar farin ciki a tare da shi idan yana maganar wancen mutumen

Fitowar Husaini da saurin cin birkinshi y saka Amina da Hasan waigawa sunna kallonsa

Kiri kiri ya yi ya ce" Mama ai na cewa Dady ba zan kuma cin abin kowa ba , walahu ba zan kuma ba Mamana"

Ajiyar zuciya ta sauke ta sakar masa murmushi ta mika masa hannu, haka kuma ta mikar da Hasan din ta nufi wajen da take tunanin a nan suturunsu suke, suturun da ita dai bata san lokacin da suka samesu haka ba, batama san yaushe aka zuba su ba, kai karshe bata san wa ya zuba ba

Sai da ta tsorata da ta bude wajen kayan
Kayan gasunnan birjik kala daban daban, kuma kowani launin tufa an yi gefensa daban

Ajiyar zuciya ta dauke ta nemo wajen kayan barcin ta ciro masu wando da riga kowa da color din da ya fi so ta basu , suka shiga sakawa ta dauko masu turare ta zo gabansu ta shiga dan fesa masu
Sai kawai ta lumshe idannuwanta tana jin wani irin sanyi da nutsuwa a cen kasan zuciyarta
Sai kuma ta ji wani gefe na zuciyarta na katse mata farin cikinta ta hanyar fadin' Amina, duka wannan jin dadi na dan lokaci ne, ke kin sani, duda mafarkin da kike yiwa yaranki samu kennan, watau irin wannan rayuwar, ama hakan ba yana nufin ki ringa mantawa da komai dake gabanki ba'

A hankaki ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gama shafa masun suka haye saman gado daya su biyun kowane na yi mata murmushi

Itama murmushi ta yi masu a hankali ta shiga yi masu addu'a tana kallon askin dake kansu mai kyau sak dai irin na yan gayu,

Murmushi ta yi , ta samu kanta da yiwa koma waye ya kular mata da ƴaƴanta haka adu'ar fatan alkhairi a zuciyarta

Bata tashi ba sai da ta ga sun yi barci sannan ta tashi da kyar ta nufi nata dakin tana ayana' Bara dai na yi wankan nima na dawo mu yi kwoncin mu , ba wani yaron da zai hannani kwonciya daki faya da y'ayana ba, idan fa suka motsa tsakiyar dare bana kusa suka yi kuka? Nima ba zan iya barci ni daya a dakin cen ba ai'

Tunda ya bude bangarenta ya ga sai hasken fitilu da TV dake yi ama bata falon ya yi tunanin tana dakinta

A nutse ya nufi dakin nata ya murda ya shiga da salama a bakinsa yana wara dubansa dan son gannin inda take

A jikin kofar ya jinginu yana kallonta, zaune take a saman gadonta da shiga irin ta sasaukan wando dogo da riga , kitsonta a daure a tsakiyar kanta, fuskarta a hargitse kamar ta sha kuka

Itama kallin take yi tana sauke ajiyar zuciyar bacin ran dake nukurkusarta, yanzu fa ta gama yanke cewar zata je ta same shi, sai kawarta tace da ita aa ta bari ya zo, kar ta manta amarya take, kuma gashi gida da kishiya kar a fara saka mata ido, ita dai ta saurareta ne ba wai da nufin zata yi aiki da abinda ta fada ba, sai gashi ya shigo

Murmushi ya saki gannin da gaske a shake take, dan haka sai ya dago ya karasa bakin gadon y zauna yana sake fadin" Amincin Allah ya tabata a gareki Risalah, ina nema maki amincin Allah kin yi shiru?"

Risala ta lumshe idaannuwanta tana rike hawayenta, domin idan akoy abinda mahaifiyarta ta yi ta jadada mata shine ta kiyaye yawan kukan nan, bashida wani anfani, idan ya kasance komai zata sakashi a gaba tana yi masa kuka to fa zai rainata ne

A hankali ta ce" Huby, yanzu fisabililahi ace yau kwana biyu da daura aurenmu sai yanzu na ganka? Kamar baka dokina? Wani irin kira ne ban yi maka ba bayan ka san kai ya dace ka neme ni? Irin kiran da ake yiwa mace ana murnar an daura din nanma baka yi min ba, nd mun ware babar ranar yin diner kace kar na fita? Why? Me yasa kake min irin haka ne?"

A hankali ya sake fuskantarta ya ce" Risala, tsarin gidanku ne sai an yi diner a kawo ki gidana shi yasa na baku dama, na hannaki zuwa diner ne dan baki saka suturar da zaki je gaban kowani kato ki wuce ya biki da kallo ba, ita diner din nan ai ba'a ce ba za'a yi ba, ama me zai hanna a yi shiga ta musulmai?"
Chapter 47 · 0% Book details