Sashe 60
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina ta yi masa kallon ka ji kaina, ta yi masa kallon tarin tarwatsewar da zuciyarta ke neman yi, wanda ya sakashi faduwar gaba da tsurata mata ido tamkar zai hadiyeta danya, muryarta na rawa ta ce" Ka dubi Allah, ka dubi girman Allah ka bani dama na fita da ita asibiti, duba ka ga halin da take ciki? Ka tausaya mana ka barmin ita na sadata da asibiti ka ji? Walahi na rantse maka ba zan bari namiji ya duba maka ita ba, kuma ko kwabo ba zan nema na maganinta ko abinda zata haifa ba, dan Allah yaya Mudi ka min rai ka barni na kai kanwata asibiti........" Ta idasa tana hade hannayenta da ta shafo ruwan da Firdausi ke zubarwa jikinta sai rawa yake tana malolowa tamkar tana fitar rai,
Da mamaki ya rike habarsa ya ce" Yau nine yayan? Yau zan yi maki rana ko Amina? Nine zaki kalla ki kiraya da yaya? Ai ki ci gaba da raininki da salon wulakancinki, kema sai na haramta maki shigowa gidana in ga ta tsiya da karyar zumuncin munafurci, kin ga ba inda za'a kaimin matata, a barta a nan idan lokacinta ne ya yi ai haka Allah ya nufa ko akoy dan iskan likitan da zai hannata mutuwa ne?"
Amina ta ringa kallonsa hawaye wani na korar wani
Wani irin nishi da Firdausi ta yi ta kakafe gaba dayanta ya saka Amina fashewa da matsanancin kuka ta mike tana ajiye Firdausi gefe ta yi waje da gudu tana ihun a taimaketa
Idannuwansu ne suka sarke, dama gaba daya hankalinsa ba wani a jikinsa yake ba yana kai kawo
Kafa daya ya daga zai nufeta sai gata ta rigayeshi zuwa
Tana zuwa ta fada jikinsa ta rukunkume shi tana sakin wani kukan muryarta a hade, a cakule tana fadin" Wai ba za'a kaita asibiti ba, nakuda take yi ABDUL, wayo Allahna ABDUL ka taimakeni, ita kadai ta rage min, ita kadai nakeda ita ABDUL "
Biyu har rige rigen fitowa daga cikin motar suke domin tun fitowarta da ihun kukanta suka saki wayar direba Muhamat da suke buga game da ita sunna kallon mamansu hankali tashe
Da kyar ya iya bambareta a jikinsa yana kallonta ya ce" Amina, ki nutsu mana Amina, me yasa ba za'a kaita asibiti ba? A ina take?"
Zuwa lokacin mazan dake tsalake su sun tsalako, haka mata na anguwa dake kusa du sun garzayo da yara, duda Amina na rukunkume ne a jikin ABDUL a yau ba wannan suke ganni ba, rashin mutuncin Mudi da son kashe baiwat Allahn yarinyar dake tare da shi ya fi komai bakanta masu, yaren ne dai ke zarro ido gannin baba da baba sun kama junna namiji da mace kuma, abin mamaki (🧐)
Amina ta yarfar da hannunta tana fadin" ABDUL, wai ba za'a kaita asibiti ba ABDUL, wai ya haramta mata zuwa asibiti da aurensa a kanta ABDUL, shin ya halata irin wannan abin kuwa ABDUL? ABDUL cewa ta yi wai mutuwa zata yi, Abdul da hannuna na rufe idannuwan Mamanmu, ba zan iya rufe na Firdausi ba tare da zuciyata ta buga ba Astghfrullah Abdul, dan Allah ka taimakeni ABDUL"
"Shuiiiiiiit, ya isa haka, ya isa....." Ya fada a hankali yana kallon kofar da hangen kamar mutun ne a tsaye yana hangensu
Biyu ya kama ya umarcesu kan su koma mota, sannan ya kama hannunta suka nufi gidan kansa tsaye , ba ko dar bale dari dari ko wani dan tsaye tsaye, jama'a kuwa suka nemi mara masa baya
Shi ya fara saka kansa zauren da salama a bakinsa ciki ciki yana janye da hannunta
Summa ne kadai Mudi bai yi ba a lokacin da ya ga mutumen dake rike da hannun Amina
Wannan shine mai kampanin da ya je neman aikin share share da gyaran filin wasan yara aka ce masa ya je ya yi jira idan an tashi kara ma'aikata a duba a ga cencentar wanda ya cencenta idan yanada rabo za'a neme shi
Wannan shine ABDUL RA'UF fa? Ko menene? Meye hadinsa da Amina?
Hannu ABDUL RA'UF ya mika masa ya sake yi masa salama
Kukan da Amina ke yi ya saka ABDUL RA'UF katse masa tasa salamar da ya kwasa wata doguwat salama yana fadin" Idan ba damuwa zamu je asibiti da ita"
Mudi ya wani gyara tsayuwa, halin wulakanci na bibiyarsa ya ce" Ai damuwar Elhaji mu a gidanmu har rantsuwa muke yiwa babanmu cewa matanmu ba su ba asibitin nan ta yahudawa, idan kuwa suka taka suka je a bakin aurensu"
ABDUL Ya sake fuskantarsa ya ce" Kana dai nufin idan har muka fita da ita zuwa asibiti ka saketa kennan?"
Mudi ya wani gyada kai shi ga azalumin karshen zamani, mace na kwonce a halin summa ciki na mata wani iri har ya daina motsi ama ya kafe kan akidar da bashida ilimi a cikinta dan tsabar duhun kai, da kafiya irin ta jahilci yana sake maimaita eh a kan bakansa yake
Ran ABDUL ya baci, bacewa irin mai tsananin nan, bai taba gannin marar tausayi da imani irin mutumen nan ba
Fita ya yi da wani irin sauri
Jim kadan ya dawo da litafi da takarda fara a samansa da byro ya mika masa yana fadin" Tabatar min da sheda,, dan samun ingantacen zawarci in sha Allah"
Ido Mudi ya wara a kansa, yana kallon takardar a hannun ABDUL, uwa uba yadda ABDUL din ya kere tsayinsa da cika fiye da shi, kana gannin Abdul ka ha rikaken dan dambe! sai ga direbansa da ya biyo baya, jikeken kato maji karfi wanda a da ya yi zaman yin fashi da makami , sanadiyar ABDUL din ya shiryu ya dawo yi masa aiki, shine direbansa ko tafiyar mota ta barin gari ne shi ke jansa, sunna tafe sunna shan hira kamar ba mai gida da yaron gidansa ba, ko salama bai yi ba ya dubi Mai gidansa yana fadin" Sir yaya dai, ta cije ne na kwonceta?".....da irin muryar nan ta dabamci, domin sai da ya matsar da jama'ar bakin kofar gidan ya ja masu kashen ba kyau leke sannan ya shigo
ABDUL ya girgiza kai yana duban Mudi da ya shiga zazaro ido ya shiga fadin" Aa, yaya haka a shigo min gida da karti fisabililahi bayan matata a yashe jiki a waje ? To wai da kake cewa na saketama a matsayinka na wa zaka iya amsar sakinta ne? Ina cewa ko daurin aurenta liman din anguwa ya bani tsabar batada da dangi bale kuma wai wani kato ya sakani sakinta?"
Ido Muhamat direban ABDUL ya zarro ya ce" Kai rasa kunya ne kai hala?, Dadi kasheni zan daki yaro yau, kai wannan din ai babanta ne, mijin hajia ne fa, miji kuwa Allah na tuba ai uba ne kau?"
ABDUL ya taka ya karasa gabansa, a kausashe ya ce" Ka san Allah, idan ka yi mana rashin da'a a nan sai mun gwada maka danyen kai sannan mu barka a kwonce, da kake fadin wanene dinta, nine jigon yayarta, hakan ya bani damar zama uba a gareta;"
ABDUL ya sake duban yadda Amina ke kife a kan Firdausi ya dafe goshinsa ya ci gaba da fadin" Baka sani bane a sakefa take tunda na sani ne abinda zai hannani sadata da asibiti daga nan raina ya bar gangar jikina, KE UMAN BIYU KI RUFEN BAKI KE KUWA!"
Ya daka tsawa yana kallon wajenta dan walahi sai wani katse masa fada take yi yana kora jawabi ,
Ya dora da fadin" Irinku sam baku cencenci auren mace ko wace iri bace, domin baku da da'a da kunya da adini, kuma rakakun da ake yi ana kyaleku ne ke baku kwarin gwuiwa, kunna fakewa da ku masu adini ne kunna cutar yayan mutane dake karkashinku, .....bara ka ga karshen gardi ya shigo maka gida"
Yana gama fada ya karasa inda Amina take ya kamata ya mikar da ita ya nuna mata hanyar fita a hankali ya ce" Yi shiru mana kema haba uman biyu, jeki mota ganinan"
Ta so jan maganar, sai dai gannin ABDUL din du ya rikide kamar ba shi ba sai huci yake yi ya sakata juyawa ta fita da sauri tana karra rufe bakinta da hanna kanta sake fashewa da kukan tana ambaton sunnan kanwarta da fadin Allah ya bata lafiya
Dukawa ABDUL ya yi ya cicibi Firdausi dake da mugun nauyi ga na ciki ga na sakewar jiki , ko hijabinta ba'a saka mata ba ya juya ya nufi fita da ita a hannunsa fuskar nan a hade
Da garaje Mudi ya nufo shi yana ihun fadin a ajiye masa matarsa, walahi idan aka fita nan kofa da ita ya saketa saki uku!
Dau Muhamat ya daukeshi da wani bahagumen mari a kan kunnensa wanda ya bada wani sauti *GAB* dan karkacewar amonsa da zazafan sautinsa sannan ya saka kafarsa daya ya shure shi yana nanade hannayen rigarsa ya ce" Kai baba, baka yardaba kennan da Sir yace zamu iya kasara maka jiki, kai in ba rashin kunya ba maza suka ce maka ubanta ke magana ai sai ka saurara, haba elhaji kai har namiji ne kana wulakanta gidan hutunka kana wani hobara kamar jaki? A waje ake dawa, a cikin gida kai nama ne yaro, domin idan ba su ba mu, ko kana iya take mai jela irinka dan uwanka ne bamu sani? Shege arne mai bakin ido ka wani furta saki shashasha to Allah ya tashi kafadunta ta sha madara ta murje ka zo kama kukan jini !" Ya karashe da babar muryarsa yana hararan Mudi dake kasa yana ihun an cire masa kunne, a fasa masa keya
Muhamat ya ce" Kai daina yin ihu mana kar na kwashe maka hakora oga na kusa baya son hayaniya walahi, shege sauran daba kai nan har mafarauci ne? Ai ko daba bama son sakarai irinka wawa dillah! Kai dana irin tawa matar ka samu wa bilahilazi kana daga hannu ta fara sharara maka marin kuma ba inda zaka kaita sai hakuri"