← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 83

Sashe 14

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ya ce" Malan Innusa inaga dole zamu shiga gidan nan, kafin a tado wata macen kar aje wani ne a gidan nasu, duba da kwanakin baya hakan ta faru?"

Na'am suka yi da shawararsa, gaba dayansu suka shiga, sai daya da ya koma tado matarsa datijuwa da nufin ko menene mace sai ta fi su karfin taimakawa dan kare hakin musulunci

A yannayin da suka same su da ƴaƴanta a dole suka fara bata talafin tsayar da jikin da goshinta ke yi, sai kuma Aban Saudat ya fice da sauri dan ya dauko adaidaitarsa a tafi asibiti

Innar Audu itace da yarta suka talafi Maman biyu, sai Aban saudat din da kuma biyu suka nufi asibiti, su kuwa sauran suka je masalacin dan gabatar da sallah

Bayan an gama sallah ne yaron Liman ya shaidawa Liman abinda ya faru, da yake baban masalaci ne dake cen tsalake , har sallar juma'a a nan ake yi ya saka Liman anfani da lasifikar masalaci ya dakatar da datawan da samarin baki daya ya shiga nasiha da jan hankali, da neman alfarmar kowa ya binciki ya'yan gidansa ko idan ya kula yaron anguwarsa nada irin halin nan ya fada a sanarwa hukuma su yi gagawar shiga lamarin, yaren sun ce wani ne ya shigo ya taba mamansu ta suma, an sako yarinya a gaba dan an ga miji bai fito ba kuma ba uwa ba uba ba dangin da suka yi jin kai? To b zasu zuba ido sunna ji sunna gani a salwantar da rayuwar yarinya ba, yau koda ace itace ke janyo mazan da rashin kamun kai datawan anguwa ba zasu bari hakan ya ringa faruwa ba bale yarinyar an yi mata shedar kamun kai da kare mutuncin kai!

Sosai abin ya taba zukata, ciki kuwa Harda Mai Shanu dake yin doguwar tafiya a kafarsa shi da daidaikun ma'aikatan gidansa su zo har masalacin nan dan yin sallah, idan suka fita sukan zagaya ne a kafa su yi sport sosai dan jin saukin yannayin jiki

Hankalinsa tashe ya karasa wajen Liman bayan an sake yin addu'a a raragu sosai yana tambayar wada ake magana a kanta?

Liman ya san sarai mahaifinta ya masa gadi, hasalima gidan da take cikin Baba Mai Shanu ne ya malakawa mahaifinta suka fita daga haya suke ciki, dan haka ya sanar masa ko wacece da fadin anma kaita asibitin tafasa, shina yanzu cen din zai nufa

Sosai hankalin Mai Shanu ya karra tashi,
Tatare suka dungunzuma a cikin motar gidansa da ya sa Baba direba ya je ya dauko sula nufi asibitin Tasafar kowa hankalinsa tashe, zuciyarsa kuwa cike da tsoro da zulumin Allah ya sa wannan shedani bai samu galaba a kanta ba

Baba Mai Shanu kam abubuwan dake cikin zuciyarsa yawansu da girmansu Allah kadai ya sani
Ya shirya yin gaba da gaba da dangin iyayen yarinyar nan, idan zasu mayar da ita wajensu su mayar, idan ba zasu mayar ba to fa shi zai dauketa koda kuwa bata so! Ya isa haka, zaman tarenma da aka yi ai sai Allah ya tambaye su su da kansu bama dangin na iyayenta ba, sam an yi sake, an yi wasa da lamarin yarinyar nan, shi tunda ya kwatanta ta koma ta nuna ta fi son zama a nan tana gannin dakin mahaifinta da mahaifiyarta sai ya bar maganar, bai san ba baban tashin hankalinta zama tare da Matarsa bane, bai san ba Amina tana tsoron abinda zai taba mutuncinta komai kankantarsa, shi yasa ta iya garinta take tuka tuwonta

Sun tarar an gama wanke mata goshin nata ta farfado ama tana kunshe cikin hijabi sai kuka take yi, Aban saudat ya koma gida ya dawo domin bai fito da isashen kudin da aka ce zai biya ba

Baba mai shanu ne ya fito da fari kal din carbinsa ya je direct office din baban likitan wanda ya kwana a asibitin kuma bai sauka ba ya nemi izinin ganninsa

Likitan na fitowa ya gaisar da Baba cikin mutunci, domin likitan akoy daraja dan Adam, kuma kana gannin Baba ka san akoy hutu a tare da tsohon

A tausashe, da damuwa Baba ya ce" Jikata ce aka shiga gidansu jiya, nake so a duba min ita da fatan babu abinda ya sameta"

Cike da jimami likitan ya yi gaba ya kirayi likita mace ya sa aka kirawo Amina sula shige ciki dan a dubatan

Sosai aka sha daga da ita, domin sake rikicewa ta yi da nuna ba za'a dubata ba, ba zata kunce zanninta ba, sai da Likitar ta rarasheta ta nuna mata za'a duba ne idan bai yi mata komai ba sannan ta amince ta dubata

Tare suka fito Likitar ta shedawa Baba cewa Allah bai bashi dama a kanta ba

Gaba dayansu sai da alamun nutsuwa ta bayana a tatare da su

Fuska a hade Baba ya ce" Amina Wuce ki shiga mota mu tafi gida"

Amina da har yanzu bata wani dawo normal ba ta kalli Baba hankalinta na sake tashi ta ce"

ASALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️

*NA*

*SAJIDA NIGER*

Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida

Wannan Novel na kudi ne ba free bane

Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER

Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai

Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka

*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*

*Page 1️⃣0️⃣*

Baba Mai Shanu ya ce" Kwarai kuwa, zan fi so Amina ta dawo gidan nan ta zauna kusa da mutane, cikin mata da jama'a yan uwanta, zata fi sakewa ta ci gaba da karatunta har Allah ya kawo miji a yi aure"

Irin abin nan na wasu tsofin idan abu ya basu mamaki ko takaici ya yi yana dafe haba ya ce" Aure? Yanzu tsakaninku da huwa rahamanu baku gane yarinyar nan ta gama wulakantar da kanta bane ya sa ta kasa samun miji? To ai mai sunnan iya ko dan gidan na kawota na kawowa kaina fitina da balaki ne, domin a cenma da bata giga ba dan kawai yayansu ya daki kanwarta furduduwa take ko wa? Ta dauki ice tace ko shi ko ita, a haka wani sakarai ne zai dauka ya kai gidan watarana gardama ta hada su ta masa tsinanen duka? Ta zo ta kalli tsabar idona da nace a siyar a raba masu gado a saukewa bayin Allah nauyi a kansu tace aa su ba za'a raba masu gado ba, yarinyar nan a nan na hanneta maganar karatu da tace an ce iyayensu su zo nace me ake da boko? Boko ai lalacewa kennan! Tace da ni ba lalacewa a maganar boko , ilimi ne halal ne a neme shi!, Na kuma yi tataki na mata magana a kan rikon yara har biyu maza, da me zata ciyar da su? Waye zai aureta da yaren nan maza ? Zamanin nan waye zai iya rikon ɗan wani? Ama idona idon mai sunnan iya tace Baba zan iya ka bar min su kawai zan iya! Yarinyar nan gardama a kanta ta sauka kamar a kwakwaluwarta aka rawaito, ni kuwa yaya zan yi na iya rikonta? Ai kawai gidan nata zata koma ta je ta rayu da ya'yan ta ci gaba da gantalinta har ta tsufa, shi kam Uban mai sunnan iya ya yi asarar haihuwa walahi!"

"Subahanalah, subahanalah malan, subahanalah, fal yakul khairan au li yasmut malan, yaya da girmanka da hankalinka malan da kanka zaka yi furuci irin haka? Yau kofa yar zumunka *LALATACIYA* ce ai zaka siranta,, harshenka ya bita da addu'a bale mu zahirinta da muka sani yarinyar tana da kamun kai, ba zamu yi shedar badininta ba, ama abinda idannuwanmu ke gani tana dauke da sheda ta alkhairi sosai, to ni a ganina ai rikon ƴaƴan y'ar uwarta da take yi dan tana da zuciya mai kyau ce, ga jajircewa a wajen baiwar Allahn nan, mai zuciyar alkhairi kan yi mata dan talafi a gareta, ka tausasa kalamanka malan a kan yarka" Liman ya fada cike da jin ba dadi a furucin Uba a wajen Amina

Sai dai su suka san dadin abinda suke hange, basu san shi ya riga ya yi nisa baya jin kira ba sai da ya kara gyara zamansa yana dan kada kafarsa ya ce" Tototo, Aya, Allahu akhbar, kennan Man liman fadin gaskiyarma matsala ne? To Allah shi kyauta, ama ni kam Mai sunnan Iya ta fi karfina walahi, ba zan iya zama da ita ba"

Baba Mai Shanu ya fi kowa jin takaicin bawan Allahn nan, wani irin mamaki ke lulube zuciyarsa da mamakin zumuncin zamani, y'ar zumunka? A gobe kiyama ita zaka gani fa! Itace kake wulakantawa haka? Maganar Liman ce yau ko bariki aka tare a kan yarinyar nan ai zai siranta ya bita da adu'a balle babu wanda zai ce ya taba gani ko ya ga wanda ya gani, shin menene a cikin rikon baki uku kawai? Yarinyarma bata da zubuwa, ko kyauta ka yi mata sai ka zare ido zata amsa, shine har zai kireta da sunnan idan ta gama dadiron? Ta tsufa? A cikin haka? Wannan dan uwa ne ko makiyi ne?
Chapter 14 · 0% Book details