Sashe 13
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ya kalli Husaini dake sake jan hijab din uwar sai sake lika mata shi yake yi a jikinta dama gashinta a fili tuni, da furucinsa na bakin yara sai ihun wayo Allah za'a zane su yake yi
A zuciyarsa ya ayana' Um, Allah ya sa kar ku yi halin rashin kunyar uwarku, gwara ku gaji mahaifinku!'
Bai ce komai ba ya juya ya koma motar ya bude gaba ya shiga ya ba direban damar su tafi, dan ya ga Mansur bai gama magana da su ba
Docter Mansur kuwa Husaini ya janyo yana fadin" Haba jarumina, kai da kace min kana so ka zama likita kuma shine abu kadan sai ya rikitaka ka ringa rusa kuka kamar yar budurwa?"
Husaini da ya raka motar da kallo yana ta hakin kukan ya ce" Ba uncle din cen bane zai zane mu? Dan Allah kar ya zane mu mamanmu bata iya jifa ba ko a gida ni fa Hasan muke korar mata kyankyaso daga daki tsoronsa take yi kamar me"
A hankali ya dago da dubansa yana kallon maman nasu ya ga sai kiciniyar mayar da hijab dinta take yi kasa kasa sosai ya ce" To abanku fa? Shi ba zai korar mata ba?"
Ido ya zarro hadi da kama baki yace" Kai, mu ai bamu da Aba ya rasu akace"
A sanyaye yake kallon yaron, sai kuma ya mike ya rike hannunsa suka karasa wajen da bokicinta yake tana ta kakabar jiki ta dauki bokicin da jakarta da ta watsar du ta hade tana jan numfashi domin warin abin hawan mata kai yake yi sosai
A sanyaye ya ce" Maman twins, ki yafe mana dan Allah"
Sosai ta so jan maganar, sai dai mutumen nan tana matukar gannin girmansa, a haduwarsu sau biyu kadai alkhairi ya shiga tsakaninsu , ya kare mata mutunci sau biyu kuma ya rarashi Farid sau biyu, duda shi dinma bata tunanin idan ya girma sosai , ta yiwuma ta girme masa, ama tana gannin darajarsa, dan haka a sanyayen itama ta ce" Ba komai, zamu wuce gida"
Ya so su bari ya kaisu, ama ta kiya, a dole ya hakura ya tafi ko kyautar da ya so ba Biyu ta tubure ta kiya, da wannan ya tafi da addu'ar Allah ya sake hada su, shi kam yana son taimakawa matar nan da ƴaƴanta, kamun kanta na matukar birge shi a rayuwa
___________________________________
A gajiye suka dawo gidan tare da Baba lauratu, domin kasa zuwa wajen markadan ta yi sai gidan baba lauratu ta je a nan ta fashe mata da kuka tana fadin an ci mata mutunci, karshe dai Baba laurantun sai ta rufeta fa fada tana fadin ta lura a kan lamarin Biyu sai ta tube a daku da ita, ta ringa sanyaya lamarinta, ina ita ina jifan motar masu kudi, masu kudin nan da daidaiku suka san yafiya da kyaliya ? Idan aka makata a cel yayazata yi kennan? Ta san basu da inda zasu je su kama a cirota , Allah ne kadai ya isa ya yiwa abin tsawa, ta kiyaye Allah ya taimaketa ta fada hannun na kirki
Ita kam shanye abinta ta yi a ranta, ama ta san babu maganar na kirki, mutumen banza ne kawai Allah dai ya hada shi da aboki na kirki
Da kaza kazar Baba Lauratu ta hasa wutar suyar kosan ta dora kasko ta shiga soya mata da siyarwa ita kuma ta shige ciki ta ja ruwan wanka ta dumama shi ta darje Hasan da Husaini da kanta , har kawunnansu sai da ta wanke da sabulu da soso sannan ta ji dama dama
Itama ta yi wankan tamkar zata cenza fata ta fito ta gyara katifarta ta kwonta gashinta a barbaje dan ta samu ta huta, du wata kasala da bacin rai ke taso mata, ta so a bari ya mareta, da sai ta daka tsale ta shatawa jar fuskarsa mari sannan ta ciro sajensa a hannunta walahi! Karyar rashin kunya, ta rasa me yake yawo a kwakwaluwar samarin zamani
A ranar dai bata wani sake yadda ya kamata ba, ƴaƴanta kansu basu haye mata ba sun kula ranta a bace sai suke shigowa idan ta kama su shigo din, sunna cen wajen Baba Lauratu sunna tayata ciniki, masha Allah sai zuwa siya ake yi taa ko'ina, dama samari sun fi gane irin haka, sai ragwagin matan da basa girki a gidajensu, sai yara da kwadayin abin ke saka su amso ashirin din iyayensu su siya su laka a hakoransu
La'asar sakaliya Baba Lauratu ta gama gyara komai ta shiga ta hau dardumar da Amina ta yi sallah bata ninke ba ta shiga gabatar da sallar itama
Tana salamewa ta yi addu'a ta shafa ta waiga barin da Amina ke zaune sai cika take yi tana batsewa
Murmushi ta yi ta ce" ko dai na raka ki ki je wajen Baba Mai Shanu ki zane jikansa ne Amina?"
Amina ta kalleta jin abinda ta fada da dan mamaki, sai kuma ta sada kanta tana turo bakinta hadi da jan numfashi kasa kasa sosai ta ce" wai bani da kunya"
Baba Lauratu ta yatsina baki tana ciro kudaden itama ta ce" To ai ba'a yi abin kunya ba, ki ware uman Mijin shine kawai alkhairi, fushin bashi da dadi ai ko? Tunda dai ba ramawa zaki yi ba ai batawa kai lokaci ne, matso ki ga kuɗaɗen cinikin, masha Allah kasuwa na sonki Amina shi yasa nake ce maki ba dole sai da aikin gwamnati zaki ci abinci ba, baki taba kasawa kika kwashe ba'a siya ba, ama ke kin dage da maganar boko"
Amina ta mike kamar an tuna mata tana fadin" Yauwa Baba kin ga tunda na fara kosan ga dubu gomar nan hadeta da ajiyar wajenki, kin ga har kudaden sun zarta wanda ake da muradi na jarabawar nan, sai dai lokaci ya kure, ama ba komai zan ta ajiyewa ana adanawa kafin badi idan ina cikin masu rai sai na kuma ajiyewa na zanna , Baba ina son boko, ko dan kaina ya karra wayewa, bale boko din fa tana biya baba"
Baki Baba ta kebe, ita kam bata ga abin matsawa kai da maganar boko boko ba, a yi bokon a gama aikinma ya gagara? Ai kasarmu in dai baka da dogon hannu ko ka san mai dogon hannu ka shiga uku kennan, da zafin a kawo a kawo kawai ya isa ya koreka daga hanyar bokon, ta ce" Allah dai ya fito da miji da kudin na je na sa Lukman lafinta ya dandasa mana gado dandasheshe"
Shirun da ya biyo baya ya saka Baba Lauratu karra kallonta, dama ta san a rina, da zarar an mata maganar aure sai komai nata ya tsaya, kamar wace bakin aljani ya aura, ta dauko damuwa ta ɗorawa kanta , a cikin manemanta mutun biyun nan tana gannin idan Allah ya yi aka yi da su ko yayane zasu kular mata da yarenta, domin a cikinsu babu na banza, daga baban Sauda har Muktar sunna da mutunci kuma an sheda sunna da riko da iyalansu da gaskiya, ba yinwa ba matsalar sutura, daidai karfinsu sunna kamantawa, bama kamar matar Muktar mai kanti, babu dashin da bata shiga na anguwa, kwanakin nan harda dashin gidan Baraka na dari uku a wata ta shiga dan tana samu, ama ita sai ture su take yi ta kasa sakin jikinta, idanma a nan take so su zauna da mijin ai ba damuwa sai su yi zamansu, duda da wahala mazan yanzu masu takaici su aminta da haka, ama ai hakan dinma ba laifi bane
Ita dai Baba sai da suka ci abincin dare ta yi masu salama ta tafi
Amina ta dawo ciki ta dage labulen dakin ta bude kofar dakin sosai, domin yau wani irin zafi take ji, biyuma da duka fara yin barci ta ga du sun rage suturar jikinsu babu mai riga a cikinsu , kowane kuma ya kama gabansa ya kwonta a gefensa dan yau basa so su likuma junna dan zafin da garin yake da shi
Sake watso ruwa ta yi ta koma dakin ta dawo baki baki ta kwonta da daurin kirjinta sai hijab dinya da ta jiko ta rufa shi a jikinta ta shiga yin adu'ar tsaro ta tofawa yaren , itama ta yi ta tofa a jikinta sannan ta kwonta tana neman barci
Barcin ne ya yi awon gaba da ita a nutse, sai dai a cikin barcin mafarki ne marar dadi ke dawainiya da ita
Mafarki take yi wai ita da namiji, mafarkin da ta jima rabonta da yin irinsa
A hankali ta ringa ji kan nononta na zafi sosai kamar ana tsikara mata allura,
Juyawa ta yi domin gaba daya abinda take mafarkin tamkar a zahiri ne
Dakatawar da aka yi na dan lokaci ya sakata sake neman barcin hadi da sauke ajiyar zuciya
Sai dai bata jima ba ta ji ana shafar kasanta an kara shafawa
Tun tana daukan abin da wasa sai ji ta yi ana mulmular abinda ke gabanta da yatsa ko da mene? Ita dai tana ji abin na sake shigarta dan haka ta kai hannunta cikin magagin barci dan kadewa, ko turewa,
Hannunta ne ya yi raf da hannun dake kasanta ,lokaci daya barcin dake idnanuwanta ya dauke sakamakon fizge hannunsa da ya yi ya mike tsaye
Wani irin razananen ihu ta saka hadi da wawurar hijabinta da zaninta tana sake ihun kwarto hadi da neman fitowa ko Allj zai bata sa'ar guduwa ta labe
Jikinta rawa yake yi, kuka take yi, bata gannin gabanta hakan ya sa ta maku da jikin garun dakin nata ta yi baya ta zice a kas ta tafi a sume
Ihun da yarenta ke yi sunna kiran sunnanta ya ankarar da daidaikun mazan dake fitowa dan zuwa masalaci
Hankali ne ya fara tashi, domin daya na girgizata ne daya na ihun kiran sunnanta, uwa uba kofat gidanta a bude ham
A hankali mazan suka fara dan taruwa a kofar gidan har suka kai mutun hudu, ciki harda yaron liman, shima magidanci ne kuma bai fi gida uku tsakaninsu ba