← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 83

Sashe 26

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwarai Mansur yanada gaskiya, sai dai shi dinma ai ba muharamar tasa bace, subahanalah, shi yasa kwata kwata baya son irin abinda take son nunawa, ta tashi ya zo gidansa su cewa junna me? So take yi mutuncinta da yake gani ya daina ne? Me yasa ta cika naci a kan abinda bashida wani anfani? Menene ya sumar da ita ne?
Sai dai a yanzun ya zama wajibi su bata kula, abin takaicin a kasan hijab dinta wando ne dogo wanda a yanzu da ta fadin gayanan a fili a jikin kafarta ya bayana, shin me yasa yarinyar nan ke wasa da abinda yake dorata a kai? Shi yasa ya dakatar da maganar kai kudi gidansu, yana so sai ya gamsu da ita da tarbiyarta, ama a kulun sake baudewa umarninsa take yi

A nutse ya ce" Ya zama wajibi ka bata irin kular da ta dace ai Mansur, kai din likita ne, idan muka ce sai mun nemi muharaminta ya riketanma karshe kai din zaka dubata, ka dubata kawai Allah ya bata lafiya!"

Mansur ya yi gagawar fadin" To ai ka kamata mana, ina zaka je kuma?"

ABDUL RA'UF ya ce" Zan koma na sha magani ne nima, kaina ke ciwo, nd zafi nake ji har cikin idannuwana"

Da kula Mansur ya ce" To wa zai kama min ita?"

ABDUL RA'UF ya ce " Ka san ba zan iya tabata ba ko? Kai kana da damar tabata dan talafawa rayuwarta likita ne kai, ni fa?"

MANSUR dake ta kallonsa sai da ya ajiye wata ajiyar zuciya mai zafi, dan walahi yarinyar nan ta tsorata shi, kuma bai tabbata ba dan ya san waye abokinsa a kan matsalar kishi, shi fa yakan ce macen dake yafa mayafi wani kato ya kalla ya raya a ransa shi kam ya haramtawa kansa ita, yanzu haka a cikin rudun da yake da Baba Mai shanu ya sheda masa cewa ai maman biyu ce za'a aura masa, har suka je daurin auren a tare suka dawo yana cikin tunanin ra'ayi irin na ABDUL RA'UF, macen da ta auri wani har ta haihu aka aura masa ba da ra'ayinsa ba? Ya san abokinsa na son kakaninsa kamar ransa, ama kuma baya hada ra'ayinsa da na kowa ( kun san shima bai san cewa ba itace uwar biyu ba )

"Duda haka, ka tsaya kana tsaye mana, ka sani ko me ya summar da yarinyar nan yanada nasaba da kai, ka yi kokarin mutuntata kamar yadda ka saba, ka fi kowa sannin irin son da take yi maka, ba karya bane, ba kuma dan abin hannunka bane, so kuma ba karya bane "

A hankali ya karra juyawa ya kalleta
Idanuwansa ya lumshe, shi kadai ya san damuwar dake daskare a zuciyarsa

Dawowa ya yi ya zauna saman kafet din a hankali ya tankwashe kafafuwansa ya mayar da kansa baya saman kujerar ya lumshe idannuwansa

Mamaki ke neman halaka shi
*SO?*
Shima ai yana sonta! Sonta da yake ne ya sa yake hakuri da halayanta, lalle tana kular da shi da bashi haushi, ama ai shi dinma yana sonta
To ama..................to ama fisabililahi...................
To shi din nan a kan SO ko ciwon yar yatsarsa zai yi ne bale Summa? Wai har a kai ga mutuwa!, So ko wani dalili daban? RISALAH dama mai tsananin tsananta abu ce, ko abinta a gidansu babu mai taba mata, nata fa nata ne, domin ba zai manta wani lokaci da cousin sister dinta ta yi masa wasan cewa mijinsu, RISALA dan rashin wayo a ranar fata fata suka yi da yarinyar, kuma har yau basa magana, a gonakinsa hakan ta faru, ya je kauye ne ya kwana bakwai dan ya bi harkar nomansa da alkhairan gonarsa tace itama zata je kauyen wajen dangin mahaifinta, suka je da y'ar uwar tata, shi tunda ya fahimci karya ta yi ba wani dangin mahaifinta biyo shi ta yi ya cenza mata, kuma sai aka samu matsalar nan Yar uwar tata ke masa irin tsokanar nan, karshema sai shine ya bada mota aka maida y'ar uwar tata, bale yanzu ta ji an aura masa wata? Uhum

Yana hakan MANSUR ya ringa zirga zirgar hanyar kicin da wajen da RISALA ke kwonce har na tsayin mintuna kusan ashirin

Cen ya ji jan numfashinta, sai kuma ya ji kacaniyar da ya tabata ta kokowa ce

A hankali ya sake lumshe idannuwansa dan baya so ya bude ya ga a wani yannayi ta farka da kokowar?

Muryar kukanta, da ratsatsin abin da ya tabata na madubin gilas din dake dauke da ruwan lipton da lemon tsami da akan matsa masa mai yawa a ajiye masa dan bukatarsa ta kansa wace shi kadai ta shafa

Sai kuma muryar MANSUR dake magana da ita yana ta ambatar sunnanta da fadin ta nutsu kar ta jima kanta ciwo, ta nutsu kar ta yi abinda zai ilatata, ko me ya daga mata hankali idan ta bi a hankali ai zata ji saukinsa

Kuka ta kuma fashewa da shi a hankali ta kai zaune tana duka hannunta a saman cinyarta

Idannuwanta da suka fara kumbura suntum , sunna dauke da gashin ido gazar gazar masu tsadan nan ta dauka ta sauke a barin da ABDUL RA'UF yake

Hannunta ta kai daidai zuciyarta tana murzawa a hankali , hankalinta a karshen tashe ta dake kallonsa muryarta a raunane ta ce" Dama zan ga wannan ranar? Dama zan ji haka da kunnena ? Dama zan wayi gari My man, my heartbeat, my happiness my love ace min ya auri wata? , U'r are mine....ka tabatar min da haka da ka barni na kamu da soyayarka!"

A hankali ya dago kansa, jajayen idannuwansa ya sauke a kan fuskarta, muryarsa mai karfin ta balagagun maza ba masu lankwasar harshe irin na launin muryar mata ya bude a hankali ya ce" Kina da matsala!"

"What? U say inada matsala? Inada matsala?"

" Ki min magana a tausashe, nd ki daina min ihu a kan shirmamiyar maganar nan RISALAH, sai da na ce maki ki koma gida, zan zo shine kika....................."
Ya dan nuna wajen da ta summe din irin a rashin damuwa ya sake dubanta ya ce" Ke din ba yarinya bace, ke din ba karamar yarinyar da zata ringa yin shirme bane, ina tunanin kin kai wajen da sai dai ki yiwa wani nasiha da irin abubuwan nan"

Ciwo take ji a zuciyarta, da rarafe ta rarafa da saurin gaske da niyar kamo hannunsa dan ta sake nuna masa irin halin da take ciki na tashin hankali
Sai dai da sauri ya janye hannunsa yana kallonta wannan karron a hankali ya ce" RISALAH?"

Lebensa da ya yi maganar take kallo, jan lebensa mai kama da na jariri take kallo, sajensa dake kwonce da dan madaidaicin gemunsa take kallo, ta san dalilin kiranta da ya yi a haka da kuma janye hannunsa

"U knw, i lv u, i really really love u ABDUL, ka san ba zan taba iya rayuwa da kai da wata ba ko? Kai ka san ba zan iya hakurin hakan ba ko? Wacece ita? Soyaya ka yi da ita bayana? Me yasa baka zo ka aureni ba sai ita ka je ka aura? Yar siyasar su Mama ce tace a gidanku ma ta kwana, tace ka zo, ni banma san ka zo ba, tace aurenka ka zo.........ka daina sona ne ban sani ba? Ka daina ra'ayin aurena ne bani da labari? ABDUL ka daina sona ne?" Ta karashe da muryar kuka sosai, muryar kuka mai taba zuciya sosai, muryar dake taba cen kasan zuciya sosai

Mansur ya kuma yin yinkurin fita a karro na uku

A hankali ABDUL RA'UF ya ce" I said ka zauna tare da mu, domin bana so shedan ya yi tasiri a kaina ta kowace fuska!"

"Ya salam" ya fada kasa kasa, shi da kansa shekara daidaidai hudu ya ba ABDUL RA'UF a duniya, taraiyarsu ba ta ya bishi bane dan yana da kudi, taraiya ce ta mutunci, sun hadu a aji daya tun secondary, shi ABDUL RA'UF an sakashi makaranta ne da wuri sosai, sabanin shi Mansur sai da ya kai shekaru kusan tara ya fara zuwa makarantar sakamakon cenje cenjen waje da tsatsauran ra'ayi irin na mahaifinsa, a sanninsa da ya yi, har zuwa yau da suke dinke matsayin abokai ya sanshi da yin taka tsantsan da harkar mata, ABDUL RA'UF nada kyankyami mai masifar yawa, haka kuma yanada kishi mai kargin gaske,
Ba zaka taba sannin ABDUL RA'UF shima namiji bane sai ka yi zama da shi mai sunnan zama, kamewarsa ta sa baya shiga irin magangannun samari a kan lamarin mata, ko ya nuna zakewarsa ko ya nunaa yes shima yanada wani abu mai sunna feeling a kan mace

Da yawa na masa kallon anya zai iya sakewa da mace kuwa? Da yawa na tunanin da wahala idan yana daya daga cikin maza masu anfani da damar da Allah ya basu dan su mori rayuwarsu ta hanyar badala da ƴaƴan mutane MATA da suka wulakantar da kansu, sai dai basu gane bane, shi din ya fi su more rayuwarsa domin ya guji harkar kazanta yana tanadar zamansa da *WACE ZATA YI MASA LAFABI!*
Ko zamansa shi kadai a gidan nan sai da aka kai gauro aka kai mari kafin kakansa ya amince, kai kakansa ko a yanzu yakan yi masa ziyarar bazata, sannan ya ringa bin daki daki dan bincikensa, yakan yi murmushi idan ABDUL RA'UF din ya tsatsareshi da ido yace" Ka daina kallona a haka, ka san yaren zamani ba'a shedarsu, bale kanada masu bugawa bawa gangar shedan?, Shi yasa nake dan dubawa dan na ringa dan tunatarwa cewa idan aka daki layin an tafkawa kai kuskure mai zafin gaske"
Chapter 26 · 0% Book details