← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 83

Sashe 66

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa yayi ya fice daga dakin ta bishi da kallo ita ma a hassale sosai ta jinjina kai irin za ka sani ɗin nan! Ita kula Risala shine ta tafi ɗin dan ya ce ta tafi ba ko wani gardama da jan aji, to ta ya ma Abdul ɗin nan zai darajtata ne da wannan rawar kan?

________________

Tunda ta fito kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kanshi ya miƙe ya fice a falon ta bi bayanshi tana mai turo baki da jin ta ya zai mata haka? Ko fa waya ba sa yi tunda ta zo gidan nan bare kuma maganar zuwa dubata.

Abu ɗaya da ta ji daɗinshi shine karɓan jakar hannunta da yayi ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan a shige shi ma tare da aje jakar a tsakiyarsu.

Bai sake kallonta ba bare ya ce mata ƙala, ganin bai da niyyar yi mata magana yasa ta ɗan matsawa kusanshi kaɗan tare da ɗauke jakar ta ɗofata a kan cinyoyinta, a hankali ta zura hannunta na hagu ta sakalo a na shi hannun ta dora kanta a kafaɗarshi a sanyaye ta furta "Babbbb."

Tunda ta rike hannunshi yayi jim tare da tsayar da idanunshi yana kallon ƙeyar Muhamat dake masha Allah dagaa zaune ma za ka gane ba ƙarami bane.

Shigar da leɓenshi na ƙasa yayi cikin bakinshi ya ɗan ciza kadan sai kuma ya sake maida dubanshi kan wayarshi da yake dannawa bai kulata ba, tunkuɗo baki tayi gaba ta sake lafewa a kafadarshi ita ma bata sake cewa komai ba dan ta lura bai da niyyar yi mata magana, sai dai ita ai bata ga abinda ta mishi ba, kuma tunda har ya zo gidan da kanshi ya nemi ta koma, to tabbas yana buƙatarta ne a gidan, dan ta san wannan uwar biyun ta bakinshi ba abinda za ta iya tsinana masa dan ita ce sabuwa fil a leda.

Sai dai bata san Abdul ya amsa kiran mahaifinta ne ba wanda ya na girmamashi fiye da yadda a yanzu yake ganin mutumcin Mamanta, ba dan ya kirashi ba da ya so ya barta ta yi ta zama a gidan, idan an tamayeta dalili ta ce dan ya je mata ne ta zo jinya gida, aikin banza kawai! Shi bai ma taɓa ganin irin wannan rashin hankalin ba a rayuwarshi.

Sunna karasawa gida yanzu bai ciro jakarta ba, hasalima bangarensa ya nufa yana amsa waya da ta shafi kasuwancinsa

Itama fitowa ta yi tana yatsina, ita ga matar oga matar so,
Da isa ta dubi Muhammat ta ce" Kai ka daukon jakata ka kaita bangarena"

Da mamaki Muhammat ya kalleta, sai kuma ya dauke idannuwansa da sauri domin hijabin ta kwashe ta bi bayan Abdul

Tana shigowa yana gama wayar a zaune saman kujera ta shiga fadin" Bab, yanzu fisabililahi kana yi min adalci a rayuwa kuwa?, Ka duba ka gani a yadda aka daukeni aka tafi da ni, ashema kanada bukatata a gefenka ka wani shareni ba kira ba amsa kirana?, Bab soyaya fa ba karya bace, ni masoyiyarka nake ba makiyiyarka ba"

Da mamaki yake kallonta, zai bata amsa aka sake kiransa

A dole ya duba ya daga ya shiga amsawa
A kalaman da yake yi karara ta fahimci gini ne aka yi a cikin gidan nan da ya dauki sunnan Mom twins gyaran amare, wanda ta ji da kunnayenta yana maganar cewa yanada bukatar wajen ya yi fili, kuma dukkan abubuwan bukatar da aka kawo na ginawa a saka a tabatar sun shiga wajensu a tsare kamar yadda ya bada a hoto

Sun dauki dan lokaci sunna wayar dan mutumen famar da yake yi ya leko wajen, ama yace aa shi ba yanzu ba yana dai so a gama komai idan an gama zasu zo tare ta gani shima sai ya gani, abinda bai yi mata ba sai a cenza mata

Risala har idannuwanta ke neman rufewa da duhu da tashin hankali

Kallonsa kawai take yi har ya katse kiran ya juyo sashenta ya ce" Sorry, mema kika ce?"

Maimakun ta dawo kan maganarsu, sai ta sake dubansa tana fadin" Abdul, gini menene ake yi ne?"

Idannuwansa ya lumshe , sannan ya sake budewa ya ce" Wajen gyaran are ko mene, Na maman twins ne"

Sake dubansa ta yi ta ce" Kuma a cikin gidan nan?"

Shima dubanta yake dan son gane me take nufi

Risala ta dafe gaban goshinta ta ce" Bama wannan ba, wai ba kace ka hanna mace sana'a ba?, Ba kace ba zan yi aikin saloon dina ba?, Ba kai da kanka ka shiga tsakanina da nawa neman ba?, A kan me ita zata yi?"

Da farko ya so hawa ta hanyar da ta hau, watau kalubalantarta ita da kanta kafin ya tsigeta daidai da laifinta
Sai kawai ya ga ciwon kai ne zai dorawa kansa mai zafin gaske
Dan haka yana dubanta ya ce" Ba sana'a na hanna mace yi ba, bana son sana'ar da mace zata yi a waje ne, idan kema kina so sai a maki naki a nan cikin gida sai ku ringa yin abinku a cikin gida, ai nema hallal ne, ama ni na fi gane na cikin gida wa iyalina"

"ABDUL, kennan kana nufin zama zaka yi na aure na dindindin da wannan matar da har kake kirrarin iyalinka? ABDUL hakan na nufin matar aure take a gidanka mai darajar da har ta samu wajen sana'a a cikin gidanka wanda yake nufin bakada niyar rabuwa da ita?" Risala ta fada a sanyaye

ABDUL ya dago daga ringeshen da yake yana kallonta

Risala ba zata daina bashi mamaki ba a rayuwa

A nutse ya ce" Kina ji, da san samu ne mu ringa kauce irin wannan magangannun, kin ga kamar yadda kike da daraja a wajena haka takeda ita, maganar na zauna da ita ko aa wannan kuma ni ta shafa, haka kuma maganar abinda zan iya yi dan kyautatawa dayarku, Risala bana mayar da abu dole idan ba adininane ya koyar da ni ba......Amina matata ce, bayantama ban maku alkawarin auren zobe ba bale ki damu kanki, tsakaninku baki daya kuwa kowa ya yi ta kansa kawai, wanda ya iya allonsa ya wanke .....ai fili ne a gabanku!"

Yana dasa aya ya mike ya haura sama dan futa zai kuma yi, ga wayar da Baba ya masa a kan auren jikar Baba Rabi'u na yana son ganninsa dan gudunmuwar da zasu kai, ga kuma zuwa da zai yi kauye su ga wasu dabobi da aka ce magada nada bukatar kudinsu, garke ne har shida na mahaifansu, zasu raba gado

Shi kam abubuwan dake gabansa da yawa , ba zai zauna Risala ta ringa bata masa rai ba! , Tunda batada wayau ai sai ta yi ta yi.

_____________________________________

Tunda Risala ta dawo aka ci gaba da gabatar da zaman kwana daidaya a tsakanin iyalinsa, rigimarsu suke yi a cen tsakaninsu a dalilin ginin gyara, kasancewar kowa da part dinsa ba lale ka san me dan uwanka ke ciki ba idan ba zumunci kuke yi ba, ko kuma kunna yaegumtar junna
A wannan rigimar Harta baba sai da ya shiga, yace kuwa yana bayan jikansa, idan zata yi aiki a cikin gidanta ba laifi ta yi, in ba haka ba ta hakura, shima da ya yarda macen ta fita gashinan abinda ya haifar masa!
Karshe dai mahaifiyarta ta tsaya kan ya zuba mata kudin da ya kashewa Amina tunda hakinta ne ai itama a asusunta, a zuciyarta kuwa ta kudurta a dai zauna zama mai sunnan zama, da kansa zai yarda ta koma bakin aikinta ne

Kwanaki daidaya da yake masu sam Amina bata gane hakan sosai ba, domin yakan daga mata kafa ne idan ya gaza yake tarda ita da dabara da wayo ya cin mata, sai komai ya lafa ta gaza dago ido ta kalleshi dan kunyarsa da kunyar kanta, shi kuwa babu abinda yake sakashi daria irin lokacin, da ganganma yake mikewa yada ya fado duniya a gabanta ya yi tsaye, watarana har ihu take ta fice bayi da gudu tana fadin sam bashida kunya wannanba hali bane!, Ya yi ta dariarsa shi kuwa.........

Baban abinda ke saka Amina a farin ciki a yanzu idan ta daga ido ta ga irin walwalar da kanwarta ke tsinta a hankali a hankali
Bama idan ABDUL ya masu shigowar yama,
A da takan gudu ta barsu da yaren da su Firdausin
A yanzu kuwa sai kawai ta zauna nesa ta ringa mamakin tadinsu, da walwalarsu, da wasa da dariya
Bama abinda ke sake sakata dariya sai Fido ta ce masa wai wani Dady, shi kuma ba kunya ya amsa abinsa

Takan ji wani irin farin ciki idan ta ga sunna kus kus da Fido,
Sam bata taba sannin me suke fadi ba, ama a yadda suke dinkewar su yi kuskus harma da Baba idan tana gidan sai ta ji wani irin kwonciyar hankali na samunta a cen kasan zuciyarta

Da wannan ta je ta zanna jarabawarta, jarabawar da ta ringa shan wahala a kan ajiyewa kadai bama har ta samu damar zannawar ba

Jarabawar da babu abianda bata ganni ba a kanta

Har an so a wulakanta mutuncinta a kanta
Har an so a wulakanta mutuncinta a kan jarabawar nan

An nuna mata idan tana so ana iya bata hanya ama idan itama zata bayar da wani abin da take da shi kuma takeda iko da shi

Kiri kiri saboda dan cikon da bai taka karra ya karya ba aka rike mata hannunta harma aka so a nuna mata itace ta ki ci gabanta a duniya
Chapter 66 · 0% Book details