← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 83

Sashe 34

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ikon mai yi mana ruwa kawai Hajia ta tsaya tana kallo, gaba daya sai ta so shiga wani tunani daban a kan yarinyar, kai harma sai ta so afkawa a tunanin kiyaya ce ta saka haka ko kuwa kwarewa a iya wasan ne?

Ta dan jima tana nazartarta a haka, karshe ta ba kanta amsa daya jal, koma meye ke dawainiya da yarinyar ita ba shine a gabanta ba, a yanzu abinda ya fi dadada mata rai da tace zata yi , ta zata idan ta ji maganar kishiya hakan zai daga mata hankali harma ta kasa boyewa, sai ta ga ba wannan bane a gaban yarinyar gaba daya

Kai ta dan girgiza ta sake duban kayan, to ita kayan nan ai ko kyautar da ake yiwa ma'aikatan gidan idan zasu kai lefen aure ya fi haka yawa bale wai matar ABDUL
Duda bata san abubuwan dake cikin akwatunnan na, ama ko meye a ciki ta tabata kadan ne a abinda matar ABDUL zata malaka harma ta anfana
Motar kanta ba wata baba bace dan ba zata wuce million bakwai ba da ta sa aka kawo sannan ta zuba kudi a ambulop du saboda koda ta karkare ta siyeta da kudadan da ta tabata kaf danginta basu taba rikewa ba, sai ta samu mamakin furucin yarinyar

Kafadunta ta dage ta ce" Kina nufin zaki yiwa Alkali maganar nan ba tare da kin nuna masa saka ki aka yi ba, kuma ki nuna masa da Abdul kuka tatauna maganar, irin kin aminta ne da son ranki?"

Amina ta gyada kanta ta ce" Hajia, duka kaf zan yi, zan yi gaba daya , in dai nima zan koma bakin shagulgulana na yau da gobe"

A gaskiya Hajia bata da cass da hakan, bata da matsala da hakan ko daya, dan fice da shigowarta kuwa bata tunanin zai damu wani, ta je inda zata je, ta dawo a lokacin da take so, bata da matsaya da hakan, in sha Allah ita kuma zata bata damar yin abinda take so har a yi auren nan, in yaso da laluma sai a saketa ta kama gabanta,....ashema abin ba wani wahala ko raini a ciki

Murmushi ta yi na samun nasara tana gyada kanta ta ce" Ya yi, ama ki sani kayan nan da kudin nan duka ai hakinki ne, haka kuma motarma taki ce, kina iya hawa ko ki saida duka malakinki ne, ina so daga gobe ki same shi, idan har ya amince da maganar ki shaida masa karshen watan nan ne za'a tura din, kuma saka auren sati biyu ne suke so"

Kai Amina ta gyada sannan ta karra yin shiru tana sauraron dukkan tsare tsaren da Hajia ke dorawa da abinda suke so a yi ita da jikanta

Sai da ta gama ta salameta
Tare da yan aiki suka sauko aka shiga shigewa da tulin kayan da aka batan ana jibgewa

Baba Lauratu da ta kasa tsaye ta kasa zaune tana gannin hakan ta mike tana duban Aminar da yannayin son karrin bayani

Sai da suka gama suka tafi sannan Amina ta samu waje ta zauna ya sada kanta zuciyarta na afkawa a kogin tunani

Aure? Dan bata da daraja, an bata danar fita a lokacin da take so ta dawo a lokacin da take so? Lalle gaske hankalinta ya dugunzuma ya tashi a kan maganar auren dan gata, koda babu maganar shekaru rayuwar nan ba tata bace sam

Baba Lauratu ta kalla dake yi mata tambayar wadinnan fa?

A hankali ta ce" Baba, da kika je gidan Fido kin kuwa fada mata komai? Ama ban ganta ba?"

Baba ta zauna fuskarta na cenzawa ta ce" Kin sani sarai fa yar nan, ga ciki ya tsufa ga rayuwar firdausi sai yadda Allah ya yi kawai, ana fatan samun cenji na alkhairi in sha Allah "

Amina a wani sanyayen ta ce" Zan je gidan nata gobe in sha Allah, Baba ai cikin nata yanzu zai kai wata takwas ko?"

A kufule Baba Lauratu ta ce"Ke Amina, yaya ina maki wata maganar ke kina yi min wata ne?, Ina maki magana a kan kayan nan ke kina min wani shirme daban? Wace irin fita? Auren naki dudu kwana hudu yau ki fara fita gobe ko bazawara kike ai kya gama amarci bale ko tarewa baki yi ba?"

Amin ta yi murmushi tana sada kanta , sai kuma ta dago a sanyaye ta shiga labartawa baba duka kaf abinda ya faru, komai da komai bata boye mata ba, ta dora da fadi " Baba, ki yarda, sannan ki saka dangana da maganar nan, ba aure kike so na yi ba? Zan yi, daidai da ni, zan yi auren , ama ki bari lamarin nan yaa warware cikin ruwan sanyi, akoy cin zarafi a cikin lamarin, wanda ya hada din kuwa ba wanda zan ringa tararwa da kukana bane a kan wace take iyalinsa, sai abin ya fado a kan gabar nima bana ra'ayin hakan, Baba idan da halima ni din nanma ya fitar da ni ya dauko hudu tashi daya, shine isar namiji ba wai daya tal ba, kayan nan ko tsinke ba zan taba ba, kuma kin manta gobe juma'a ranar tuyar wainar Baba ce? A goben kuma nake son zama da Baban in sha Allah"

Tabas abu ya daki Baba Lauratu, magangannun gaba daya sun shigeta ta yadda ba'a zato ba'a tsamani, haka kuma irin abinda Aminar kanta ta yanke ya bata mamaki
Koda yake haka ne, idan kana cikin hali na wuya wuya din zuci babu abinda ba zaka fadi ba

Murmushi ta yi tana kada kanta, a ranta ta ayana' Lalle akoy ranar kin dilaci, akoy ranar da zamu zauna da ke da kuma kakarsa da shi kansa mu nemo mafita a abubuwan kunyar da ake tafkawa, watau ita ta take dikar mijinta ta kuma kyamaci talaka, ke kuwa kin biye mata kin yi naki rashin kunyar kin nuna mata bakya son danta, shima uban tafiyar baima nuna ya yarda cewa mace aka bashi ba ko?, Ba damuwa lokaci ke raba gardama, rai dai da lafiya, ama da mamaki idan aka wayi gari kowa ya manta wanene MAI SHANU banda matarsa, yau ace Hajia da kanta ce ta manta waye mijinta? Lalle abin da matukar mamaki, wai har Mai SHANU ya dora doka a take? Uhum, ta manta ita din wacece, koda yake dadi kan sakawa a manga wuya.........'

A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Aa, ba zaki ki yin anfani da kayan cen ba, haka kuma ko kai kayan amaryarsa da ke za'a yi in sha Allah, dan ai ba zaki so mai Shanu ya irgaki cikin amsu bijire masa ba ko?"

Amina da bata yi tunanin amsar nan daga Baba ba ta tsareta da ido tana son karantarta

Baba ta dora da fadin" Wani nacinma bashi da anfani, ama ba zamu daina komai ba, haka kuma zaki ci gaba da yan shige da ficenki da ci gaba da kare mutuncin kanki, janyo kayan mu gani mu ware na dinkawa idan ba a dinke ba, mu yi sauri mu gama na je na hado maki kayan wainar ta Mai SHANU ko?"

Wata ajiyar zuciya ta farin ciki ta saki ta mike ta shiga yin abinda babar ta ce hankali kwonce , cike da farin ciki

Babar kuwa ta yi murmushi irin na manya a ranta ta ayana' Aya, ta yaro kyai take yi, bata karko, Amina...zaki saka kanki a ramin nan da kanki ne, haka shima zai zurma a lokacin da bai aune ba, ita kuma zamu ga irin nata hukuncin............sannan sai mu sake aunawa mu gani a cikin taron nan *WA ZAI YI LADABIN?!* ( TOH FA)

haka suka sake wuni, koda yama ta yi dukkan abinda ya dace kafin dare ya shigo yrenta suka dawo suka dinke a ciki, abinci baya gafce masu haka kuma a yau bayan muryar baban harda ta hajia ta ringa tsinkayowa a falon, ta yi murmushi abinta watau ta samu solution hankalinta ya kwonta ko? Rayuwa kennan

Kamar yadda Baba ya saba zaman sasafe idan ranar juma'a ce, hakan ne yauma

Sai dai zaman nasa na yau tare da uman biyu, da biyu ne ga wainarsa a gefe sai turiri take yi kanshinta ya gama cika masa hanci so yake yi su gama magana da Uman biyu wace ya gama fahimtar da magana a bakinta ya kama wainar nan ya ci iya cinsa

Tsai ya yi yana kallonta, maganarta gaba daya dai ya ji bai gamsu da ita ba, yannayinta kansa ya tsargu da shi, furucin bakinta kuwa ya fi komai bashi mamaki

Amina ta sake sadda kanta tana sake kamo ayoyin samun galaba tana ta yi da addu'ar da ta shiga bakinta, dan idannuwan Mai SHANU kaifin tsiya ne da su yana iya saka ka fadin gaskiyar da ka boye a cikin karyarka

Murmushi Mai SHANU ya yi yana girgiza kansa a tausashe ya ce" Waye ya tsatsaraki ya tsara maki magana irin haka Uman biyu? Waima yaushe kika lakanci karya haka ne?"

Da sauri ta dago tana kallonsa hadi da kai hannunta mai dauke da yelow din kurkum da bata wanke ba abinta ta ce" Lah🫢"

Mai shanu ya yi yar dariya yana fadin" Fadi da kyau, Lah, to wai wa kike tsoro da za'a fara sako ki a gaba da tsararen zance ni kuma ki tardoni dan bakya jin tsorona?"

Fuskarta ta takwakwabe ta sadda kanta tana ta rubububi da kalamai dan samun galaba a kansa

Dagowa ta yi tana kallonsa a raunane ta ce" Ama Baba, ai ba haramun bane yin hakan ko?, Bayan wannan shi ABDUL din ai ya yi biyaya da ya yarda da zabinka ko Baba? Dan Allah a tura mana......"

Baba Mai Shanu ya kada kai murmushinsa ya ki ya kau, hikimar yarinyar na kayatar da shi, sai dai du yadda ta so da boye masa gaskiya a bayane yake karantar gaskiyar lamarin, abinda dai yake son fahimta ABDUL son da yake yiwa yarinyar cen har ya kai ya yi maganar da uman biyu? Lalle da kuwa ya sarawa lamarin, dan kuwa ga dukkan alamu ba karami bane
Chapter 34 · 0% Book details