← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 83

Sashe 40

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia ta sake matsawa kusa da shi ta dauki kafafuwansa masu hasken gaske ta dora a saman cinyarta ta shiga dan mamatsawa ta ce" Alkali?"

Baba ya ce" Na'am Honorable?"

Murmushi ta yi tana sada kai ta ce" Dan Allah ka barmu mu yi bikin nan yadda ya dace mana ka ji?"

Murmushin ya yi shima ya ce" Ai ba zan hanna ba Hajia, damuwata daya ce zuwa biyu, ba za'a dauki sadaki dan duniya ta fada a maka ba, ba kuma za'a dauki kayan amaryar da ya wuce na uwar gidansa a maka mata ba, yadda aka yiwa Uman biyu za'a yiwa yarinyar itama, in sha Allah zan shiga dakin Uman biyun gobe da yama na ga kayan nata da kika ce an yi mata, idan ya so itama haka nake so a kawo mu zamu kai dan bana so mata su kai bi izinillah, albarkar abin nake nema da kuma kamanta adalci, domin bana so dan uman biyu ba zabinsa bace a nuna mata bambamci, koda ba zata yi magana ba ai mahalincinmu na gani, kuma har mu zia tsayar a kan wannan laifi, bayan haka na biyun shine ina so a ba Uman biyu dama itama ta yi gayarta ta yi bikinta ta yi wadakarta, ko ba komai ai ba Alkali bane zai karra aurw, mijinta ne zai karra ko?"

Hajia ta kume tans kallon Alkali
Gannin ya sake kafeta da ido yana tambayarta ta fahimta? Bayan wannan bashi da wata damuwa, gida kuwa zai sa a yiwa uman biyu jere a nata bangaren itama in sha Allah domin dama shi yake da alhakin yi mata kayan daki, ba yau ba ya daukarwa kansa wannan alkawarin

Hajia tana ji tana gani Alkali ya gama ya fice a gidan, watau suka nufi gidan gona da yaren

A haukace ta sauko ta fice a gidan tana waya da ABDUL
Ah toh ina ta ga ta zama wani aikin na shirin balo mata? Dama maza ne zasu kai lefen, abinda dai ta tsara abokinsa da abokansu zasu kai a yi jeren motoci da kayan setinnan akwatunna na gigita kwakwaluwar karamin mai kudi mai baban buri a kai gidan, dan so take tun daga kan kayan lefen nan ta fara nunawa uwar yar ita ba sa'arta bace, da mijinta zata ja , shima ba wai dan ya isa ba, aa dan dai mutun ne shi mai baki da kazagi a wajen manya, sai gashi Alkali na son kasheta da ranta

ABDUL dake cikin aiki gaba da baya , domin a lokacinma sunna cikin meeting ne ya yi excusing din kansa a sawake ya ce" Hajia, menene abin tayar da hankali a nan? Ki hada mata irin na wancen yarinyar mana menene a ciki?"

"Abdul? Kayan da banma san me da meye a ciki ba? Saitin akwati daya dal ne fa aka hada mata, shine za'a hadawa RISalAH? Ka san da ba zai taba yiwuwa ba ko?, Ka ga ka yiwa kakanka magana kana ji fa jerema shi zai saka a yiwa yarinyar nan, ni tsorona daya kar ya dauki bangaren da ya fi kyau din a jerawa yar kauyen nan da tarkacen ƴaƴanta!"

Abdul ya dafe kansa, tafia ce ke gabansa ta kusan sati guda cir kasar spain, harkar man fetur zata fitar da shi dan nan yake son fadawa kuma, ga kuma rigimar mutanen nan a gefe? Shi da ya gama magana da Risalah auren sai ya kusa zai sauka dan yanada abubuwan yi sosai, ama kakaninsa na son rikita masa lisafi?

A tausashe ya ce" Hajia kina ji? Ki kwontar da hankalinki Please, du ni ban ga menene na daga hankali a nan ba, maganar lefen ki zauna dukkan abinda kike da bukata in a nan kike so a hado maki a hado a kawo, idan kuwa kin fi son fita ki hado sai a duba passport dinki ki je inda kike so, plz bana sin fadan nan ke da Baba"

Hajia ta sake dafe kanta ta ce" Idan nace na fita zai ga kayan da na ba yarinyar nan, kawai gamunan zuwa NI da Uma kampani mu hada komai sai a loda a kai gidan, daga yanzu har gobe zan jure na yi zaben har mu gama"..

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kashe sannan ya koma suka gama meeting dinsu ya kuma fitowa ya nufi office din manager ya sheda masa a bude bangaren VIP na kayan lefe ga su Hajia nan zuwa, ko duka zasu kwashe a basu dama

Nan da nan aka bude bangaren VIP din, baban bangare ne da idan yayab manya zasu hada lefe suke zuwa, domin ko akwatunnan ba kowa ke iya siya ba ko a manyan bale mu (🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️)

Hajia da Hajia Uma sun rikice wajen daukan kayan amaren, sai dai a zaben nasu sun saka son zuciya a ciki, domin a duk wajen da ya dace su zuba abu iri daya wani abin sai su bambance su dauki wanda ya fi class su saka a kalar akwatunnan da suka daukarwa Risalah masu kyau da kalar yan gayu, sai su zuba sauran a sauran akwatunnan da suka daukarwa Amina color din zabin a cakule domin har kala biyar sula kwatsa mata

A bangaren shadoji dinkaku bugagu yan waje masu zubin manyan dinkunnama sai da suka yi san rai, dan harta yawan shadojin Risalah sun fi na Amina yawa
Haka a bangaren lafaya da abaya sun daukarwa risalah na lwaliyar amarya yar gata ne, su jefawa Amina na uwar gida sha gida zaunaniyar cikin gida

Takalma ne da jakunkunna na alfarma a nan kuwa babu na koma baya, kowane ka dauka na gani na fada ne
Atampopi da lesh , kananun kaya da kayan barci, sarka da yan kunnaye
Masu tsaron bangaren sai da zuciyoyinsu suka karye gannin yadda ake kwasar kayan ana jidawa , sai da magariba ta gansu a kampani sannan suka koma gida bayan an shiga sakawa kayan irin abin nan mai kyalkyali na amare ana yin yadda Hajiar ta fada, ga sunnayen da ta bada cewa a kowane a saka sunna, Amina da RISALAH

A daren hankali kwonce ta sha barcinta dan ta san an gama wannan rikicin kuma, yanzun ta shiga shirye shiryen biki ne na garari, duda haka tana cike da jin haushin wai Amina ce za'a ba wannan jerin kayan? Ta kaisu inama wai? Ta saka su ta yaya?

Washe gari ya rage kwana goma daurin auren da kusan karfe goma sha biyu a falon Baba mai SHANU Matarsa ce da Baba Lauratu, da shi Baban ana ta shigo da kayayakin da kallonsu kadai sun isa su haukata mutun a cikin akwatunnan bama a waje ba

Baba yana murmushi yana gyada kai har aka gama shigowa da komai ya dubi Baba lauratu ya ce" Allah mai iko, Laure wannan kaya ai sun isa a bude shago, Allah na tuba zamani mai tafe da rikici kin ga kayan yan mata biyu ne wannan, ai gwara da mun zo wannan zamani mun rufe daukowa bale mu gigice, kuma fa a haka sai ki ga ana saurin rabuwa da macen ta kwashe komai kana kallo kai ga shashasha ta tafi? Ai idan nine na zuba rabin wannan ba zan yi wasa ba gaskiya, kin san da lokacin Hauwa akwatin ta kwano ce mula kai kwaya biyar? Kar ki so ki ga yadda ake rububin kallo ana ka baki"

Hajia ta karra hade rai cike da takaicin yadda baba ya bararahe yake ba wannan mata labarin aurenta, hum, shi kam ya iya zubar da mutunci walahi da girma, ina shi ina wannan dadadaur matar da ko a yar aiki ita ba zata dauketa ba?

Baba ya sake yin murmushi ya ce" Masha Allah, to Hauwau kin ga wanda na zabarwa Uman biyu, ai uwar gida ce da daukan farko ko? Tunda na ga an raba abin biyu na tabata an gama gyara komai kai masha Allah "

Cikin Hajia sai da ya yamutse waje daya kafin ya bada wani kuka kuuuuuuuuu a lokacin da ta ga Baba ya nuna kayan da suka zuba da sunnan RISALA yace wai su ya zabarwa Amina!

Murmushi ta kakaro tana mikewa ta ce" Lah alkali, ka ga ai kowace da sunnanta a jikin nata, ka ga na uman biyun nan, wannan kuwa ai na Risalar ne ko? Duka kaf komai iri daya ne aka zuba ai"

Baba ya yi murmushi a ransa yana ayana' Na san a rina'

A fili kuwa ya ce" Kai masha Allah, ai kin ga nima kawai kalar ce wannan din ta fi birgeni, shi yasa na daukarwa uman biyun ita, ai tunda komai iri daya ne menene a ciki?, Kin ga Lauratu ga fa kayan uman biyu sun sauka ni kamar a saukar mata da ni mu sha kallo wannan kaya ai sai mu bude shago da su"

Baba Lauratu wani irin farin ciki ya sakata fashewa da kuka a lokacin da Hajia ta tabatar da gaske Alkali yake kayan da ta zabo classs, masu dan uban tsada da tsarin kalar na yan gayu ne ya daukarwa bagidajiyar yarinyar nan ta juya da sauri domin ko gabanta bata ganni da kyau ta shiga sauka tana hade matatakalar da bibiyu tana rike kukan dake ciyota ta saka hannunta ta murda kofar amina ta bude da karfi ta shiga ranta bace, hankalinta tashe ta kai dubanta kan Amina ta ce"

Rikicin cikin gida.....da mai rai ake yi 😍😍😍😍😍😍

Cmmnt dinku ya saka ni sakowa da sasafe jama'ata 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
*NZL PAGE2️⃣5️⃣*

Kokowa ce ke neman kaurewa a tsakaninsu, ko nace neman amsar kai, saurara mata ya yi ya bata dama ta ringa yakushi da son kwatar kanta har sai da girgizar da take ta gama kai masa sakon da yake ta daukan caji lamari ya amsa iya amsa duniya ta dauki dumi komai ya yi taurin da zai iya yaki sannan ya saka hannunsa ya janye hannayenta da ta rugfe mamanta da su ya zuba masu ido yana kallo
Kalarsu gaba daya ya ji tana ruda kwonyarsa, dan duhunsu da bakin bakinsu ke ta harararsa
Chapter 40 · 0% Book details