← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 83

Sashe 25

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ikon Allah, Baba ta ayana a cen kasan zuciyarta, koda yake tunda Amina ta wayo gari da kula da kanwarta, da aurar da kanwarta, da rainon biyu ta dauki girman duniyar nan ta dora daman kanta, Amina kamar ita ta yankewa kasa cibiya, a kulun maganarta itace ka samu dan datijonka ka aura ka je ka yi zamanka, sai ga wayewar gari an tashi da Amina da auran yaro kanninta? Shekara fa bata fi daya da ta bashi ba in ta cike dayanma, kuma Aminar in ba karfin zuciya irin tata ba aa hadiye sai Abdul Ra'uf ya hadiyeta da yawun bakinsa ko asuwaki ba zai yi ba bale maganar kora ruwa kar a shake, ita mamakinma fa ta yi da take masa kallon yaro bayan a cike yake kuma ya ajiye saje irin na samari masu ji da kansu da tsafta suka kuma tada kai da yayan banki suka yi asuwaki da kafar dawisu!, Ta yiwu dan shirunsa, da bada amsarsa da murmushi irin na kililin kasau majicin kumba ne ya sa take saurin haye masa? Da ta san sari ka noke yake yana iya zuba mata gubar da zata kaita ga halaka da ta bi komai a hankali ta yadda zata kai ga ci ba tare da ta jigata ba

A sanyaye Baba Lauratu ta ce" Allah ya rabamu da abinda kike fada Amina, Allah ya nisantamu da kunya da abin kunya, meye abin kunyar a ciki?"

Amina ta ringa kallonta, kallo irin na son fahimtar ko ta san abinda aka yi mata ne?
A hankali ta ce" Baba, Hala kin san yaron cen aka aura min?"

Sai da baba ta kama habarta, sai kuma ta ce" Ki maida hankali, kin ji? Nace ki maida hankali sosai ki ringa yiwa lamarin nan muguwar fasara ta yadda bakinki zai tabo maki rigima danya, ke yanzu in ba abu irin naki ba mijin naki zaki ringa cewa irin haka? To ki hanzarta hawa ki tarda Mai Shanu mana ki ce masa kul kar ka konani ka kona kanka bana so ka kashe auren nan dan fitsarariya ce ni komai zai iya faruwa , nace ki je ki same shi a cen sama bashida lafiya ki tashe shi ya yi abinda kika yanke kar ya barki da abin kunya!"

Sosai Baba abin ya kular da ita, gani take yi wannan din ai rashin hankali ne da rashin sannin ciwon kai
A kaikaice take yaba mata magana da fada da sharar fage, domin tana yi mata fadan ta ce da ita" Tashi dan Allah ki shige ki wanke abin nan da sabulu da soso dan kin bata min gyara ga na kwan na hada maza ki fito mu shafa, kin san dai na kwai ba'a masa wasa ko? Da yama zan koma gida kulun da safe na dawo dan dazu mai Shanu ya bada kudin siyayar nan na gyaran jiki dole zan je kasuwa na sisiyo , a kadan ma kusan wata muna yi fa, tashi tashi tashi bana son bata lokaci!"

Walahi sai Babar take neman cenza mata a idannuwanta da tunaninta, gyara na kwai? Yaushe ta samu kudin kashe kwaya kwayan yin gyara irin na kwai? Kwan da a kadan a kashe goma cikin madara da kurkum a murje jiki gaba daya da shi shine tace ta hada hadin? Ita kuwa kudin zata lalata hala a wannan abin?

Har ta shige bayi tana waiwayen Baba da ta hade gabas da yama, kudu da arewa take jira ta sake daga mata hankali, wankan ta shiga tana tunanin ran Baba ya baci ne dan ta tafi yawo da kurkum a jiki, ta tabata idan suka zauna ta yi mata dala daka zata rakata wajen babban da kanta, dan haka sai ta shiga yi din

______________________________________

Hannunsa yake dan karra sinsinawa dan ji yake yi du irin wankan da ya yi warin man jan nan akoyshi a jikinsa, shi dama baya cin man ja , jin warinsa yake yi sosai har cikin kansa
Du irin uban turaran da ya yiwa kansa wanka da shi shi kam yana jin warinsa a hancinsa

A nutse yake tafia dan zuwa wajen dining ya dauki coffee ya sha, domin ba zai iya yin barcin a yanzu ba, kansa ya fi komai caza shi a irin wannan lokacin , baya son dogon tunani sam

Idannuwansa ne suka sauka a kan MANSUR da RISALA dake zaune a falon
Shi MANSUR din shi yake kallo da wani expression a fuskarsa, ita kuma tunda ya sauko ta sada kanta kasa, domin ba zata taba manta lokacin da ta zuwa gidan nan ta tardoshi da kananun kaya sosai irin yadda suka lwashe ba, batama taba gannin namiji mai shegen jin kunyar suturarsa irin ABDUL ba

Dan sakw dubanta ya yi , hijab ne a jikinta , sai kafar wandon dake kasa da yake hange daga inda yake tsayen, sai tissu din da take ta faman murzawa wajen hancinta zuwa idannuwanta tana fyace hancin da buga hancin dan kukan da ta sha hancin ya done mata sosai

A ransa ya ayana ' Ya Salam, ranar nan gaba dayanta ta hade min da abubuwa sosai, RISALA ta ji ga dukkan alamu, mtssssssss ni kam ba zan iya yin maganar yanxu ba'

Da hannunsa ya yiwa Mansur alamar yana zuwa sannan ya nuna masa gajeran wandon dake jikinsa ya juya ya shiga haurawa

Idannuwanta ta sake dagowa ta raka bayansa da kallo har ya bacewa ganninta

Wani kukan ta barke da shi tana saukowa daga saman kujerar, lokaci daya Mansur na kokarin tausarta da bata hakuri , zai fara magana wayarta ta fara kuka

Hannunta ta saka ta dauko dan ta zaci mahaifiyarta ce dake fada kamar zata ari baki tana cen gida tana bambamin sai me? Aure? ABDUL RA'UF din ne ya yi aure tun ba'a je ko'ina ba? Ta dage kan yarta ta rabu da shi ko shine autan maza, tana ta cin alwashin ai su irin kyau ne walahi karyane su yi tsawa, idan ABDUL RA'UF baya yi wani zai yi ta yiwu wanda ya ninka shi sau dubu!, In dai ita ta haifi yarta ta kare da shi, ba zai yiwu ta yiwa kato kuka ba!, Darajarsu ta wuce nan, bata san a irin wannan lokacin tuni yar ta silale ta sadado gidan dan ta fuskanceshi ba, bata san a yanzu daf take da rasa ranta ba, ta yaya mamanta zata yi tunanin zata iya rabuwa da zazafan gayen nan? Komai nasa baba ne, shi din baba dan baba ne, soyayarsa kuwa mai zafi ce, ajinsa kuwa zazafa ne, ita yaya zata iya soyaya da wani bayan ta dandana da shi? Ta sani ne ko wacece, ko y'ar gidan uban waye zata daka ta bara mata shi ne, idan me ta zo da shi gidan ta tarar, RISALA yar gayu sunnanta ya koma ko a kasar amerika bale a kasar hausa, in menene ta taka ta iya ta kware!, Ba zata taba sharing din Abdul ba sai dai ta rikeshi ita kadai, ko wacece ta shirya mata tsaf zata kuma gwabza da ita daga nan har duniya ta tashi in dai sunnada rai su dukansu!

Gannin hoton zuciya da jinni kamar yadda ta yi seving din numbersa ya sakata jikinta na bari ta daga ta kara a kunnenta hadi da saurarawa

A tausashe ya ce" RISLANAH, plz go, zan shigo gidanku yau, kin san na hannaki zuwa gidana? Nd yanzu bana iya doguwar maganar plz"
Daga haka ya katse kiran

Tamkar ya katse da numfashinta ne, domin mikewa ta yi tsaye da sauri ta juya wajen da MANSUR ke tsaye ta budi bakinta zata yi magana, sai dai ta gagara yi ta shiga jan maganar da bakinta da hancinta, karshema gaba dayanta ta rike gaban kirjinta ta kifa a wajen da take tsaye hannunta rike da kirjinta, idannuwanta sunna neman kakafewa.........

Ya Salam, anya baku dauki lamarin nan da zafi ba kuwa?

Happy wkdn mutanena🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰😊
*NZL PAGE1️⃣5️⃣*

Gaba daya Mansur ya mike tsaye daga zaunen da yake

A hanzarce ya karaso inda ta kife din, da irin abinda ta yi kafin ta ja numfashi ta dauke ya sake rikita shi

Hannayensa duka ya kai da niyar daukanta
Lokaci daya ya tsaya cak da abinda ya so yi din ya yi baya sannan ya juya da gudu gudu yana haurawa

Yana karasawa ya ringa doka kofar dakin ABDUL RA'UF yana ambataon sunnansa

ABDUL RA'UF dake idasa bala boturan rigarsa daga sama ya juyo da dan sauri yana sake saurarawa
Jin sunnansa a bakin Mansur ya saka shi takowa a dan hanzarce kadan domin irin yadda Mansur din ke ambaton sunnansa lalle zaka san ba lafiya ba

Yana budewa Mansur ya ce" Man, me ka fadawa yarinyar cen ne? Ta summa fa, ta summa?"

Har ga Allah sai da ya ji kamar kansa zai sarra, Innalilahi wa inna ilaihi rajune, shine abinda yake ambata a kasan zuciyarsa hankalinsa na neman tashi, gaba daya kansa ke sara masa, cofee dinma bai sha ba bale a kai ga hutawa kafin la'asar ta shige

'Summa kuma?' ya saske tambayar kansa

A dole ya fito ya bi bayan Mansur yana sauka a nutse suka nufi inda take yashe kafarta daya har a jirge dan bata fadi a daidai ba

Duban Mansur ya yi girarsa na karra hadewa sosai na ciwon kai ya ce" Summan ne kuwa wannan Mansur?"

Mansur ya dube shi, ya sake dubanta, a hankali ya ce" Na si na dubata da kyau duda ban fito da kayan aiki ba, to gani na yi iya din ba muharamata bace, sannan babu wani da ya bani damar hakan a makusancinta"
Chapter 25 · 0% Book details